Thursday, 15 February 2018

ZANCE MAI KAWATARWA (10)

*ZANCE MAI KAWATARWA (10)*
💐💐💐💐💐💐
BA A KIN ILMI KO HIKIMA, KODA A WAJEN ARNE NE KO MAKIYI
🌿🌿🌿🌿🌿🌿

*_" Hikma kamar kayan da ya bata ne na mu'amini, ka amshi hikima(ilmi) koda a wajen munafukai ne"_*

*_"الْحِكْمَةُ ضَالَّةُ الْمُؤْمِنِ، فَخُذِ الْحِكْمَةَ وَلَوْ مِنْ أَهْلِ النِّفَاقِ"_*

☘☘☘☘☘☘

Yan'uwana wan nan zan ce na kara gwada mana shi Muamini baya wasa da ilmi (hikima), don ilmi da hikima a wajensa kamar Kudinsa ne Ko kadararsa ce wacce ta bata, in aka ce masa wani arne ko makiyinsa ya samu kudin/Kadara ya zo ya karba, shin zai ki karba ne?! Ai daman nasa ne ba zai bambance waye ya sama masa abunsa da ya bata ba. To haka ilmi da hikima take ba a duba waye yake da ita.

Allah ya azurtamu da ilmi tare da hikima.

🍀🍀🍀🍀🍀🍀
✍ *Haruna I Muh'd*
*080 69582878*

Via
Hdindima.blogspot.com
🌷🌷🌷🌷🌷🌷

Tuesday, 13 February 2018

ZANCE MAI KAWATARWA (09)

*ZANCE MAI KAWATARWA (09)*
🌿🌿🌿🌿🌿🌿

KAR KA ZAUNA CIKIN KUNCI, KA ZAMTO MAI WALWALA DA FARA'A
💐💐💐💐💐💐

*_"Ka dinga Murmushi (kana cikin Fara'a)... Sabo da akwai wanda... Ke sonka.....Yana lura dakai... Yana kulawa dakai... Yana taimakonka..... Yana sauraronka.... Yana kuma Ganinka.... Wan nan shi ne Allah mai Rahama"_*

*_"تبسم ..فإن هناك من ..يحبك .. يعتني بك .. يحميك .. ينصرك .. يسمعك .. يراك ..هو الرحمن .."_*

☘☘☘☘☘☘

Bawan Allah kullun ana son ka samu yakini akan Ubangiji Allah, dan shi ne mai kula da duk lamuranka.

✍ *Haruna I Muh'd*
*080 69582878*

Via
Hdindima.blogspot.com
🍀🍀🍀🍀🍀🍀

Monday, 12 February 2018

ZANCE MAI KAWATARWA (08)

*ZANCE MAI KAWATARWA (08)*

MAKIRCIN MAI MAKIRCI
🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*_" Kar ka daga hankalinka akan makircin dan Adam, mafi kololuwar abun da zai iya maka, shi ne kawai ya zantar da abun da Allah ya riga ya Kaddara maka"_*

*_"لا تقلق من تدابير البشر فأقصى ما يستطيعون فعلة معك هو تنفيذ ارادة الله"_*

💐💐💐💐💐💐

*Lallai yan'uwana mu kara sakawa a rai cewa, ba abun da wani ya isa yayi mana face abun da daman tun fil-Azal Allah ya kaddara zai samemu, shi dai kawai zartar da kaddar Allah ne kawai zai yi.*

*Allah ya sa mu dace ya kuma karemu daga sharrin Masharranta*

✍ *Haruna I Muh'd*
*080 69582878*

Via
*Hdindima.blogspot.com*

Tuesday, 6 February 2018

ZANCE MAI KAWATARWA (06)

ZANCE MAI KAWATARWA (4)
$$$$$$$$$$$

KIYAYE HARSHE

"Shi dan adam mai wayo da hankali shi ne wanda yake kulle bakinsa kafin mutune su rufe kunnuwarsu. Ya kamata kaima kayi tunani yaushe kake magana kuma yaushe kake tsayawa, (mutum ya dinga tauna abun da zai dinga fada"

Baki shi ke yanka wuya

"الانسان الذكي هو الذي يغلق فمه قبل أن يغلق الناس آذانهم. أرجوك فكر جيداً متى تتكلم و متى تسكت"

Allah yasa mu dace, mu kuma dinga fadan al-Khairi ko kuma muyi shiru

✍ ​Haruna I Muh'd
080 69582878
———————

ZANCE MAI KAWATARWA (05)

*ZANCE MAI KAWATARWA (07)*

ZABIN MASOYIYA TA HAKIKA

*_"Kada kayi bakin-ciki wai dan Budurwa ta ha'inceka, domin ita kamar Tsuntsu ne, duk Kwalbatin/hanyar da ya samu ruwa zai sha"_*

*_"لا تحزن أذا خانتك فتاة ...فهى كالطير يشرب من كل قناة"_*

✍ *Haruna I Muh'd*
*080 69582878*

Via
Hdindima.blogspot.com