Thursday, 7 March 2019

FIQHUN MATA (1)

*ZAKI IYA WANKAN IBADA DA SAURAN RUWAN DA MIJINKI YAYI WANKAN IBADA DA ITA, HAKA SHIMA ZAI IYA YI*
*____________*

✍ *Haruna Isah Muhammad*
08069582878
www.hdindima.blogspot.com

*Assalamu Alaikum yan'uwana maza da mata kamar yadda muka yi bayani a baya kan yadda musulunci ya gwada mana yadda ake tabbatar da Soyayya a tsakanimmu har ya bamu damar muyi wanka tare, na janaba ko na jin dadi tare da mazajenmu.*

*Har ila yau musulunci ya bamu damar muyi wanka da sauran ruwan da mijimmu yayi wankan Ibada da ita ko shi yayi da namu,*

*Hakan ya tabbata cewa Manzon Allah (saw) yayi wanka da sauran ruwan da matansa suka yi, duk da hadisan sun zo har da wanda aka hana yin haka,*

*A karshe dai abun da yafi dacewa shi ne ba kokonto kan suyi wanka tare, kuma ba kokonto mace tayi da sauran na mijinta, haka shima sai dai in kamar tayi wanka ne da ya shafi kawar da wata jini, to ana son shi kar yayi.*

*Manufa dai ana son kowa ya tsarkaka ne.*

*Allah ya bamu ikon amfana da abun da muke gabatarwa ya kuma bamu ladan yadawa.*

Domin mana gyara ko ba da gudumawa
*_____________*

Hdindima@gmail.com

Pls Join Us @
*ZAUREN FIQHUN MATA ZALLA*

https://chat.whatsapp.com/FomGxvgI5UT9fN737GdDbV

Tuesday, 5 March 2019

FIQHUN MATA (4)

*FIQHUN MATA ZALLAH*
*_________*

*MATSAYIN ALOLAR MACE IN TA TABA GABANTA*

✍ *Haruna I Muhd*
*08069582878*
*hdindima@gmail.com*
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

*Assalamu Alaikum Yan'uwana mata, kamar yadda muka gabatar a sama, lallai ya tabbata a Musulunci cewa idan har Mace ko namiji bayan tayi alola sai kuma ta saka hanu a al'auranta to alola ya karye.*

*Lallai Majority na malamai suna kan wan nan fahimtar,*

*Hakan kuma yana da alaqa da wadan nan Hadiths na Manzon Allah (saw):*

*Manzon Allah ya ce: "duk wanda ya taba al-auransa to ya sake alola, haka duk macen da ta shafi farjinta to ta sake alola*

Imam Ahmad (2/223)

*Ummu Habiba ta ce taji Manzon Allah (saw) yana cewa: "Duk wanda ya shafi Farjinsa to yayi alola"*

Ibn Maja (48)

*Bisa kuma yadda malamai suke bayani cewa, sai dai in ya zama ta taba gabantan ba tare da wani abu akai ba(zallah/tsirara) amma in har da akwai wani dan kyalle ko tsumma a kai ba matsala.*

*Allah yasa mu dace baki daya, kuma kar ki wuce wan nan sako ba tare da kin yadashi a grp naki ba. Fatana Allah yasa mu dace baki daya.*

Ga masu neman shiga grp  zasu iya tuntubarmu ta

08069582878
Ko kuma
Hdindima@gmail.com

ko kuma su dinga ziyartar shafimmu

www.hdindima.blogspot.com
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

FIQHUN MATA (3)

*SHAFAN KAI AKAN HIMAR KO DAN KWALI A LOKACIN ALOLA*
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

✍ Haruna I Muhammad
08069582878
Hdindima@gmail.com
🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Lallai ya tabbata a musulunci idan namiji yazo Alola yayi shafan kai akan Rawaninsa,

Haka kuma ita ma mace tana da wan nan babbar damar.

Idan kin zo yin shafan kai sai ki dan fidda kadan daga cikin gashin farko na gaban goshinki, sai ki fara shafawa ki kuma hada da Himar naki ko dan kwali.

Duk da cewa Hadithan akwai maganganun akansu

Amma mafi inganci shi ne ya halatta tayi shafar.

Allah yasa mu dace.

Sako daga:
_*Zauren Fiqhun Mata Zallah*_

Ka tura wan nan sako zuwa grp biyu a kalla, dan muyi tarayya dakai a wajen lada.

🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Wednesday, 5 December 2018

YADDA AKE HADA LEMON KWAKWA DA ABARBA

🥥🥥🥥🥥 🥥🥥
🍍🍍🍍🍍🍍

KAYAN HADIN LEMON NAMU:

*wpKwakwa
*Abarba
*Madara
*Sukari

YADDA AKE HADAWA:

👉Ki fere abarbanki ki cire farin samanta.

👉 Sannan ki markada ta a blanda, ki fere bayan kwakwan naki san nan ma sai ki yanka gutsi-gutsi.

👉 bayan nan sai ki nika a blanda ko ki goga ta, san nan sa, ki zuba a cikin ruwan abarbar
👉Sai ki zuba madarar ruwa ko ki dama ta gari ki zuba, kisa sugar kadan, kisa kankara ko ki sa a frij.

Shi kenan ya zama Lemon Kwakwa da Abarba.

Wannan lemo (juice) yana da dadi da daukar hankalin mai sha. Gwadawa maigida kiga santi

✍ Haruna I Muhd
       08069582878
Hdindima.blogspot.com

NI BAA KASHE MIN KOWA BA A YAKIN BOKO HARAM

BA WANI NAWA DA AKA KASHE NA JINI
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

✍ *Haruna I Muh'd*
        *08069582878*
Hdindima.blogspot.com
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Assalamu Alaikum Yan'uwana maza da mata yau na tuna da irin mummunar halin da Al'ummah ta shiga ne a shekarun baya!!!!

A shekarun baya Ko ta ina ba zaman lafiya, daga kaji maganar an ta da bomb sai kaji an sace wasu ana garkuwa dasu, sai kaji wai Boko Haram.........

Abun da ya faru a baya yasa kowa ya shiga taitayinsa dole tasa muka koma ga Allah muna yawan addu'o'in zaman lafiya, Allah kuwa ya jikammu ya kawo mana sauki.

Kamar yadda muka ta addu'o'in nan yanzu haka ma ya kamata Yan'uwana kowa da kowa ya sake dukufa musamman yadda muke fuskantar zabe mai zuwa.

Fitintinu sabbi suna kara tunkarar mu, ga wata kungiya wai sabuwa ita ma ba boko Haram din ba ce, ga kuma wasu sun shiga sun kashe soji wai suna cewa su ba Boko Haram ba ne wata ce ta balle daga Boko Haram.

Manzon Allah (saw) ya fada mana addu'a ita ce takwabin mu'amini, da ita zamu iya yakan ko wace irin bala'i da ta fuskancemu.

Kuskure ne kaji wasu suna cewa _ai ni tun da aka fara baa kashe kowa nawa ba_!!!

Ya Allah ka bamu zama lafiya, wan nan sako ya kamata mu yada wa Yan'uwa a ko ina mu rike addu'o'i, a gidajemmu, kasuwannimmu, da ma Masallatanmu kamar yadda muka yi a baya.

A kashe ina addu'ar Allah ya hadamu dakai/ke a cikin ladan yada wan nan sako dan Al'ummah mu fadaka Ameeeeeen.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_________________

Wednesday, 5 September 2018

AMFANIN ZOGALE

Ana Bukatar Jama’a su yada wannan Post zuwaga Sauran Al’umma domin Qaruwa da Juna.
1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).
2- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.
3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.
4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.
5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin sauri warkewa.
6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana
maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.
7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon shawara.
8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.
9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.
10- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.
11- Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.
12- Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.
13- Ana daka ganyen zogale da ‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.
14- Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya ‘ya’yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.
15- A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.
16- A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).
17- Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon AIDS zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.
18- Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.

BEAUTIFUL MESSAGE

*BEAUTIFUL MESSAGE*
*——————*
✍ *Haruna I Muh'd*
*08069582878*
*——————*

🔴  *_Stay   Away   From   Anger... It   Hurts ....Only   You !_*

*Kar ka dinga yin fushi dan kai ne wanda zai cutu*

*كن بعيدا عن الغضب لانه لايوذي احدا سواك.*
*———————*
🔴  *If    You    Are  Right  Then     There is No Need    to Get  Angry ...*

*Idan kana kan Gsky, ba bukatar kayi fushi.*

*اذا كنت علي حق ليس لديك حاجه  للغضب*
*——————*

🔴  *_And    If    You    Are    Wrong    Then    You     Don t     Have    Any    Right    to    Get    Angry*

*Idan kayi kuskure, kar ka zama mai fushi*

*اذا كنت علي خطا ليس لديك حق في الغضب* 
*——————*

🔴  *_Patience    With    Family    is   Love ....._*

*Yin hakuri ma Iyalanka ma Soyayya ce*

*الصبر علي الاسره هو الحب*
*——————*

🔴  *_Patience    With    Others    is   Respect._*

*Yin hakuri ma sauran al-Ummah, hakan karumci ne*

*_الصبر علي الاخرين يعني الاحترام_*
*——————*

🔴  *_Patience     With     Self     is   Confidence   And   Patience   With   GOD   is   Faith._*

*Kayi hakuri akan karan kanka, wan nan shi ne karin samun amintuwa da karfin gwuiwa, hakuri kuma wajen bin Allah Imani ne*

*الصبرمن اجل النفس هو الثقة    والصبر من اجل  الله هو الايمان*
*——————*

🔴 *_Never    Think    Hard    About    The    PAST ,    It    Brings    Tears..._*

*Kar ka yawaita tunanin abun da ya kubce maka ya wuce, balle har yasa ka zubar da hawaye*

*لاتفكر كثيرا في البعدين عنك حتي لاتجلب الدموع*
*——————*

🔴  *_Don t    Think    More    About   The   FUTURE ,   It   Brings   Fear..._*

*Kar ka tsawarta tunanin abun da zai zo gobe, dan kar hakan yasa ka firgita*

*لاتفكر كثيرا في الغد حتي لا تجلب الخوف*
*——————*

🔴 *_Live   This   Moment   With   A   Smile ,  It    Brings   Cheer._*

*Ka zamto a rayuwa kana mai Murmusawa, hakan zai sai ka samu dacewa da Kyakkyawar zamantakewa da kuma rabauta*

*الحياه بابتسامه تجلب لنا السعادة*
*——————*

🔴 *_Every     Test     in    Our    Life   Makes   Us   Bitter   Or   Better .....*

*Ko wace Jarabawar rayuwa takan mayar damu , imma muji ba dadi, ko kuma mu zama muna morewa*

*اي امتحان فهي حياتنا يجعلنا افضل او اردى _*

*——————*

🔴  *_Every   Problem   Comes   To   Make   Us   Or   Break   Us  !_*

*Ko wace matsala in tazo, imma ta kara mana karfin gwuiwa, ko kuma ta sace mana gwuiwa*

*الصعاب تاتينا لتجعلنا اقوياء او تكسر قوتنا*

🔴  *_The      Choice     is       Ours   Whether   We   Become   Victims   Or   Victorious._*

*Zabi a rayuwa, shi ne yanayimmu mai dadi, imma sanadiyyar sa, mu zamto muna darawa cikin  nasa, ko kuma mu zama muna cikin tasku*

*اختياراتنا هي التي تحدد بين ان نكون ضحايا او منتصرين*

🔴 *_Beautiful   Things    Are    Not   Always   Good   But   Good  Things   Are   Always   Beautiful ......_*

*Kyakkyawar abu a fuska wani lokaci ba shi ne mai kyau ba, amma Kyakkyawar abu kullun mai kyau ne*

*الاشياء الجميله ليست دائما جيده ولكن الاشياء الجيده قطعا دائما جميله*
*——————*

🔴 *_" Happiness "   Keeps   You ....  Sweet   But   Being   Sweet   Brings   Happiness!!!*

*"Farin-ciki "* *a ko wani lokaci ka sanya  mai Kaunarka cikin Farin-ciki, dan hakan na kawo Kyakkyawar zamantakewa, ka zama mai fara'a sai ka samu Kyakkyawar zamantakewa*

*السعاده تجعلك حلو المزاج ولكن كن حلوا انت حتي تجلب السعاده*

*——————*
*hdindima.blogspot.com*
*——————*