Monday, 10 June 2019

LABARIN TSOHUWA MAI YARA UKU

*UWAR MIJI DA FITSARIN KWANCE A GIDAN SURKUWARTA!!!!!!*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
✍ *Haruna I Muhammad*
*080 6958 2878*
Hdindima@gmail.com
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

*Asl. Yan'uwana wan nan labari ne mai dauke da darasi,*

*Akwai wata mata wacce ta manyanta, kuma Allah ya azurtata da yara har uku Maza, duk kansu kuwa Sun yi aure.*

*Wata-Rana wan nar mata taga girma ya kamata kuma ga tarin Arziki da ta boye ba wanda ya sani, sai tace zata gwada matan yarantan nan baki daya, duk wacce taga ta fisu kirki sai ta mallaka mata wani abu mai tsoka daga wan nan dukiya.*

*Matar nan sai ta dau aniyar zata kai musu ziyara baki daya,*

*Ran nan sai gata a gidan daya daga cikinsu, aka karbeta hanu bib-biyu, aka bata masauki.*

*Da ta kwana sai ta dibi ruwa ta zuba akan gadon, ta kira matar dantan, tace mata, 'ya ta an samu matsala fa! yau na yi fitsari akan gadon da na kwana!!!!.*

*Matar dan kuwa ta fara surutu, da cin mutunci, a karshe ma har ta ce sai dai ki wanke da kanki!*

*Haka tsohuwar nan ta wanke gadon, kuma da dantan ya dawo aka bashi labari bai ce komai wa matarsa ba.*

*Ta sallamesu ta tafi gidan daya yaron nata,*

*Tana isa gidan kuwa, sai labari ya maimaita kansa, shima aka ci mata mutunci har ta wanke kayan fitsarin.*

*Ta sallami gida na biyun ta kama hanya zuwa gidan na ukun.*

*Tana zuwa aka mata karba mai kyau. Ta sake zuba ruwa akan gadon.*

*Da gari ya waye sai matar dan ta fito, tsohuwa ta fada mata ga abun da ya faru ta mata fitsari akan gado.*

*Matar tace "Haba Mama! Ai Wallahi ba komai kar ki damu, ai wan nan girma kenan, muma ai da muke yara kun wahala damu fiye da haka, ba komai zan wanke kar ki damu."*

*Ta nemi wani kaya ta ba tsohuwar nan ta kuma wanke gadon da kanta, ta rarrashi Mahaifiyar tasu.*

*Tsohuwar nan ta sallamesu ta koma gida, daga nan sai ta tura musu cewa duk kansu su zo su sameta a gida.*

*Yaran nan kuwa kowa ya dauko matarsa suka iso, bayan sun gaisa sai Mahaifiyar ta kwashe Labarin abun da ta yi a gidajensu, ta kuma fada musu tayi haka ne da gangan dan ta gwadasu.*

*Anan dai ta musu fada sosai, ta kuma dauki dukiya mai yawa taba wacce ta ci wan nan Jarabawa. Ta ce mata in Allah yasa tsufa ya kamani sosai, ina ba da wasiyan a kaini gidan wan nan yarinyar dan ita ce zata iya kula dani da kyau.*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲

*Anan darusan dake ciki a fili suke, maza ku kara sa ido akan yadda mata ke Mu'amula da iyayensu, suma matan su kara ba da muhimmanci ga iyayen mazansu kamar yadda suke bawa iyayensu.*
☘☘☘☘☘☘
www.hdindima.blogspot.com

MADACI BISHIYA MAI AMFANI AMMA SAI DACI

*MADACI WANI BISHIYA NE MAI DACIN GASKE, AMMA KUMA YANA MAGANI, AMMA GA WANI WAI SUNANSA MADACI!!!*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
✍ Haruna I Muh'd
*080 6958 2878*
Hdindima@yahoo.com
🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Yan'uwana ku biyoni a hankali kuji hirata da Madaci.

Turkashi!! Jiya an kwalla rana matuka kuma sai gashi kafin yamma an samu ruwa, ikon Allah, nazo wucewa kenan sai na tarar da Madaci yana zaune a majalisa shi kadai, kuma abun mamaki yana cikin rana!!

*NI*: Madaci mai ke faruwa ne haka yau na ganka kamar an koroka daga gida ko baka da kudin cefane ne?!!

*MADACI*: Ka fara kenan ko, kai ko ma kaji me ke damuna baka yi ba, kawai ka hau kaina da zancen gida, gida kam ai sai wanda Allah ya bashi mata ta gari, amma in ba haka ba zaka ga yana yawo yana lissafi akan titi.

*NI*: kai madaci so kake dai sai na zauna, ni kuma yau so nake in je in karbo bashina dan naji anyi salary, sabo da masu karban salary wani lokaci ma ko isansu baya yi, kasata kenan!.

*MADACI*: Hahahahaha ai ni na riga na karbo nawa, kai ne ka makara, amma fatana kar kaje a hanya kaga kaga _Direrriya_ kaima ka nemi cikin rana ka zauna irina.

*NI*: Kai Madaci nifa ban gane ina ka dosa ba, so dai kake sai na zauna, kuma a rana, amma dan ka bani labari bari in zauna na minti uku. Amma ban gane direrriya ba!!, kana nufin zanga wata mata ta diro a KEKE NAPEP ne?

*MADACI*: Hahahahaha, abokina kenan, ni ko labari ma ba zan baka ba.

*---------------*
Sai muka zauna shiru kowa na zuwa ma kowa ido
*---------------*
*NI*: Kai ka ganka ko daman na fada maka bata min lokaci kawai zaka yi, amma sai naga kamar Zikiri Madaci yake yi, yana Astagfirul-Lah, kai sai na lura da kyau naga kamar yana son ya kawo wata aya ce a cikin al-Qur'an. Sai na ce kai Madaci me kake tattaunawa kai kadai?!.

*MADACI*: Na kasa kawo wata aya ce ta al-Qur'an, amma zan iya tuna kan gaban da zan fada maka, in kaga dama ka dauka in kuma baka so ka kama hanyarka, Allah ya kiyaye dan ban san ina zaka isa ba.

*NI*: ko zaka iya tuna sakon ayar in tuna maka?

*MADACI*: EE tana maga ne akan _Jalabib_

*NI*: Hahahahaha na ganoka ga ayar

Surah Al-Ahzab, Verse 59:

*"يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَابِيبِهِنَّ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا"*

"O Prophet! say to your wives and your daughters and the women of the believers that they let down upon them their over-garments; this will be more proper, that they may be known, and thus they will not be given trouble; and Allah is Forgiving, Merciful."

*MADACI*: yauwa na tuna wan nan ayar ce, Amma sakona ita ce, sai kuma wan nan Sallah naga mafi Yawancin yan matanmu ba adon da suke yi kamar adon GYALE, ni kuma a ganina yawancin gyalen bai rufe dukkan jikinsu, kuma abun tausayimma har da yaran malamai, kai kusan ko ina fitinar ta shiga.

*NI*: har kasa jikina yayi saniyi duk da yadda Allah yake hana mata bude jiki amma yanzu ya fara zama kamar ma ba komai ba ne.!! Allah sarki al-Ummahta!!!!.

*MADACI*: tashi ka tafi nasan ka gane me nake nufi da direrriya, ai duk macen da tasa kaya amma duk zanen halittanta ya bayyana ina ji mana tsoron kar mu fada cikin wadan da ba zasu shiga al-Jannah ba, ko kamshinta ma ba zasu ji ba. (Kasiyatun Ariyat). Inji Manzon Allah (saw).

*NI*: Lallai Madaci abun da ka fada Gsky ce Allah ya bamu ikon gyrawa.

*MADACI*: Abokina kenan bamu makara ba, mu tura wan nan sako ma kowa, amma daci gareta kamar yadda Ni madaci nake da daci.

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
www.hdindima.blogspot.com

Monday, 20 May 2019

DARUSAN RAMADAN (009)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (014)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
ADDU'AR DA AKE YI BAYAN WUTIRI
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

✍ Haruna I Muh'd
Hdindima@yahoo.com
  080 69582878
————————
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai akwai addu'ar da ya tabbata Manzon Allah yana yi bayan Sallar Wutiri, wanda da dama an shagala akai.

Ga addu'ar kamar haka: ana son mutum ya karanta sau uku, amma na ukun sai ya dan daga muryarsa kadan sama da na baya.

"SUBHANAL MALIKIL KUDDUS"
(Sahihu Abi Dawud 1284)

سبحان الملك القدوس

Kuma ya halalla mutum ya kara da

"Rabbil Mala'ikatu War-Ruuh" wato mutum ya ce
"Subhanal Malikil Kuddus, Rabbil Mala'ikaku war-Ruuh"

سبحان الملك القدوس، رب الملائكة والروح

Allah ya bamu ikon kiyaye wan nan Sunnah ta Manzon Allah (saw).
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
www.hdindima.blogspot.com
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

DARUSAN RAMADAN (008)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (015)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
RAMADAN WATAN TUBA CE
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍ Haruna I Muh'd
    08069582878
Hdindima@gmail.com
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

Assalamu Alaikum yan'uwana maza da mata, lallai Ramadan ko bayan Ramadan ana son kowa ya tuba zuwa ga Allah akan duk zunubansa, ana son mu kara neman tuba musamman a wan nan wata mai al-Barka

Lallai tuba tana da sharuda har guda shiga (6) kuma in mutum bai cikasu ba, tubarsa ba ta zama mai amfani ba.

Sharudan tubah(6):
———————
1. *Tuba domin Allah, kar mutum ya tuba dan wata abun da ta shafi duniya, (wato a saka tsoron Allah a ciki).

2. Tuba a cikin Lokacinta da Allah yake karba, in mutum yazo mutuwa ko yaga mutuwa da idonsa ko ya tuba anan ya makara, mutum ya tuba tun kafin wan nan lokaci ya sameshi.

3. Mutum yayi Baran-Baran da zunubin da ya aikata a baya, mutum ba zai tuba kuma amma yana cikin ko yana kan aikata zunubin ba.

4. Mutum yayi nadama akan abun da ya aikata, sabo da Manzon Allah (saw) ma ya ce :"Nadama ma tubah ce".

5. Mutum ya kulla Aniyar cewa ba zai sake dawowa kan wan nan laifi ba har abada.

6. Idan kuwa abun da ya tuba akai tana da alaqa da hakkin wani ne, dole ne ka mayar masa da kayansa, na kudi ne ko na mutunci ko wani abu daban.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Alhamdulil-Lah Allah ya bamu ikon tuba zuwa ga zunubammu baki daya, ya kuma karba mana ibadunmmu. Ameeeeeen

🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Share this pls
www.hdindima.blogspot.com
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Saturday, 18 May 2019

DARUSAN RAMADAN (007)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (013)
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

BA LAIFI BA NE DAN KA AIKATA A RAMADAN
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

✍ Haruna I Muh'd
     08069582878
Hdindima@gmail.com
—————————

Assalamu Alaikum yan'uwana akwai wasu abubuwa da mutane na ganin kamar laifi ne a Ramadan amma ba komai:

➡ Ba laifi ba ne dan al-Fijr ya tarar da mutum yana da Janaba a jikinsa.

Nana Aishat (RA) ta ce, Manzon Allah (Saw) ya kasance al-Fijr na samunsa yana da Janaba a Ramadan, ba kuma (Janaba) na mafarki ba, sai yayi wanka ya ci gaba da Azuminsa ".
(Ibn abi Shaibah 9171)

Kuma haka ma akwai Hadith na Ummu Salma wanda Ibn Abdul-Barr ya fitar shima mai kama da wanda ya gabata.

A karkashin wan nan haka duk macen da ke al'adah ko jinin Haihuwa, in har ya tsaya musu kafin al-Fijr zasu iya daukan Azumi koda ba su yi wanka ba har gari ya waye.

➡ Zuba ruwa a kai dan zafin Rana ko Wahalar Azumi.

Lallai ba laifi ba ne dan mutum ya na yawan zuba ruwa a kansa ko yana wanka akai-akai dan zafi ko wahala.

Hadith na Abubakar Ibn Abdur-Rahman ya ce" daga sashin Sahabban Manzon Allah (saw) ya ce naga Manzon Allah (saw) a Lokacin zafi yana zuba ruwa a kansa kuma yana Azumi, sabo da Ishi ko Zafi (Zafin Rana)".
(Abu Dawud: 2365)
👆👆👆👆👆👆👆

Da wan nan yar nasiha nake rokon Allah ya karba mana ibadummu baki daya.

🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Ka tura wan nan sako ma yan'uwa baki daya dan muyi tarayya a lada baki daya
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
www.hdindima.blogspot.com
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

DARUSAN RAMADAN (006)

DARUSAN RAMADAN 1440/2019 (012)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

HADITHAN DA BASU INGANTA BA GAME DA AZUMI
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

✍ Haruna I Muh'd
    080 69582878
hdindima@gmail.com
————————

Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai, lallai akwai Hadithai da dama da basu inganta ba inji malaman Hadith, wadan da suke da alaqa kuma da Azumi, ga sunan kamar haka:

➡ Hadith _"Barcin mai Azumi Ibada ne" Hadisi ne mai Rauni, bai inganta ba.

➡ Hadith _"duk wanda ya sha (ya karya) Azuminsa da Gangan ko da yayi Azumin Shekara bai wadatar ba"  Wan nan Hadith ma Bai inganta ba.

➡ Hadith _"Ku yi Azumi zaku ji Wasai (zaku samu lafiya garau)"_ Wan nan ma Hadith ne mai rauni sosai. Bai inganta ba.

➡ Hadith da wai ake cewa Annabi (saw) yana ce wa Sahabbai in Ramadan ta zo _" Ramadan ya zo muku....(har in da wai yake cewa) Ramadan ya zo muku wata mai Girma mai Al-Barka, Allah ya sanya Azumi a cikinsa Farillah, Sallan dare a cikinsa kuma Sunnah, kuma duk wan da yazo da wata dabia mai kyau kamar wanda yayi Farilla ne a wasu watanni, haka wan da yayi farilla a ciki kamar wan da yayi Farillai Saba'in ne a wasu watanni, kuma wata ne wanda Farkonsa Rahma, tsakiyarsa Gafara, Karshensa kuma yantawa daga wuta,".
wan nan Hadith din ma Ba ingantacce ba ne. Da'ifi ne, wasu ma sun ce Munkar ne.

Allah ya bamu ikon aiki da Hadiths na manzon Allah Ingantattau, ya kuma sa muyi muwa faka, kuma kowa ya kara shiga taitayinsa kar daga ganin an ce maka Hadith kawai ka fara yada wa mutane. Allah yasa mu dace.
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

www.hdindima.blogspot.com
———————

Saturday, 11 May 2019

DARUSAN RAMADAN (001)

*֮֮֮R֮֮֮A֮֮֮M֮֮֮A֮֮֮D֮֮֮A֮֮֮N֮֮֮ K֮֮֮A֮֮֮R֮֮֮E֮֮֮E֮֮֮M֮֮֮ 2֮֮֮0֮֮֮1֮֮֮9֮֮֮*֮֮֮
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*֮֮֮M֮֮֮u֮֮֮h֮֮֮i֮֮֮m֮֮֮m֮֮֮a֮֮֮n֮֮֮c֮֮֮i֮֮֮n֮֮֮ A֮֮֮z֮֮֮u֮֮֮m֮֮֮i֮֮֮*֮֮֮
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

֮✍֮ *֮H֮a֮r֮u֮n֮a֮ I֮ M֮u֮h֮'֮d֮*֮
֮*֮0֮8֮0֮ 6֮9֮5֮8֮2֮8֮7֮8֮*֮
Hdindima@gmail.com
☂☂☂☂☂☂

Bismillahir-Rahmanir-Raheeem

🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Yan'uwana musulmai lallai watan Ramadana yana da falala sosai tare da muhimmanci a rayuwarmu tanan Duniya da kuma Lahira.

Ga kadan daga cikin Falala da muhimmancin Azumin:

1. Allah (swt) ya farlanta wan nan Azumi a kammu da kuma al-Ummah da ta rigayemu.
(Qur'an:2:183)

2. Sanadiyar Azumi Allah yana gafarta wa mutane duk zunubansu, kamar yadda Manzon Allah ya ce " Wanda yayi Azumin watan Ramadan yana mai Imani da kuma sa ran samun Lada, za a gafarta masa duk abun da ya aikata a baya"

3. A Azumi ne Allah ya gwada mana cewa ladansa ba adadi,  kawai Ladan kamfata za a yi a bashi.

Manzon Allah ya ce: " Allah ya ce duk ayyukan bayi sakamakonsa nasu ne, amma banda Azumi ita kam tawa ce, kuma Ni zan ba da ladansa,....."

A karkashin wan nan Hadith Allah ya ambato abubuwa masu muhimmanci kan wan nan Wata mai al-Barka:

a) Allah ya ware Azumi ya zama nashi ne dan yana cewa "bawana yabar ci da sha da kuma sha'awarsa duk danni" ni zan bashi ladan hakan.

b) Allah fa da kansa ya ce zai saka ma wadan ya yayi Azumi, dan ya gwada karrama mai Azumi.

c) Allah ya ce Azumi garkuwa ce, zata hana mutum aikata munanan ayyuka, kuma manzon Allah ya ce
:" Azumi garkuwa ce wada ake samu tsanin mutum da shiga wuta".

d) Kuma a Hadith din Allah ya ce warin da yake fita daga bakin mai Azumi darajarsa yafi kamshin Turaren Al-Misk, hakan na gwada yadda Allah yaba Azumi daraja.

e) Allah ya ce mai  Azumi zai yi farin-ciki a wurare biyu,

i. Lokacin da yayi bude baki da kuma
ii. Lokacin da zai hadu da Ubangiji, dan zai samu lada mai yawa.

4. Azumi zai ceci mai yinsa a ranar al-Qiyamah, Manzon Allah (saw) ya ce :" Azumi da al-Qur'an zasu ceci bawa ranar al-Qiyamah, Azumi zata ce ya Allah na hanashi cin komai da kuma sha'awarsa, ka bani cetonsa mana! Sai Al-Qur'an ma ya ce ya Allah na hanashi Barci da dare, ya Allah ka bani cetonsa mana! (Sai manzon Allah) ya ce  sai kuma a basu ceton".

Anan zamu takaita Allah ya bamu ikon fara Azumi lafiya ya sa mu gama lafiya ya kuma bamu duk ladan da ake samun a wan nan wata mai al-Barka.

Dan samun wan nan lada tun daga yanzu ka/ki tura wan nan sako  grp naku dan muyi tarayya a ladan baki daya.
🌼🌼🌼🌼🌼🌼