*🔘AL-MAR-ATUSSALIHA ORPHANS AND VULNERABLE FOUNDATION🔘*
🔜 Shiriyar al-Quran ita ce shiriya
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*___________________*
● *{يا أيها الذين آمنوا اذكروا الله ذكرا كثيرا * وسبحوه بكرة وأصيلا * هو الذي يصلي عليكم وملائكته ليخرجكم من الظلمات إلى النور وكان بالمؤمنين رحيما}*
⌛Allah (Swt) ya ce:
*«Ya ku wadan da kuka yi Imani, ku na zikrin Allah (ambatonsa) zikiri mai yawa, kuma kuna masa tasbihi safe da yamma@ Shi ne wanda yake yabonku da kuma Mala'ikunsa suna maku Addu'a, @ don ya fitar daku daga duhu (na Shirka) zuwa ga haske (na Imani)»*
*_______________________*
♦️ *«مَن صلَّى اللهُ تعالى عليه وملائكته فقد أفلح كل الفلاح، وفاز كل الفوز، فهذه الصلاة منه تبارك وتعالى ومن ملائكته إنما هي سببٌ الإخراج لهم من الظلمات إلى النور، فأيُّ خيرٍ لم يحصل لهم، وأيُّ شرٍّ لم يندفع عنهم؟! فيا حسرة الغافلين عن ربهم؛ ماذا حُرِموا من خيره وفضله؟!»*
📜ابن القيم، الوابل الصيب (ص: 72)
♦️Ibn al-Kayyim ya ce game da wan nan Aya:
*«Tabbas duk wanda Allah ya yabeshi kuma Mala'ikunsa suka masa Addu'a wan nan ya rabauta, babban Rabo, kuma ya tsira, Yabon Allah da kuma Addu'ar Mala'ikunsa dalili ne na fitar da mutane daga Duhu zuwa ga Haske, akwai wani alkhairin da mutanen nan basu samu ba?!! kuma shin akwai wani Sarrin da ba'a tsaresu dashi ba?!, Tabbas rafkanannu ga Ubangijinsu sun tafka asara (wadan da basa zikiri), sun san irin Alkhairi da Falalansa da aka haramta masu kuwa?! (Wato an hanasu babban Alkhairi , muddin basa zikiri)»*
*________________________*
🪞 قال النبي ﷺ :
*«(علام يقتل أحدكم أخاه ، إذا رأى أحدكم من أخيه ما يعجبه فليدع له بالبركة)»*
📜رواه ابن ماجة 3509
🪞 Manzon Allah (saw) ya ce:
*«Alama ce da daya daga cikinku ke yakan Dan'uwansa dashi, idan dayanku yaga wani abu daga Dan'uwansa wanda ya burgeshi, ya masa Addu'a na albarka (Alkhairi)»*
Ibn Majah (3509)
❍ قال الشيخ ابن عثيمين رحمه الله :
● *«فإذا رأى الإنسان ما يعجبه وخاف من حسد العين فإنه يقول: ما شاء الله تبارك الله، حتى لا يصاب المشهود بالعين، وكذلك»*
❍ Sheikh Ibn Uthaimin (R) ya ce:
*« Idan dayanku yaga wani abun da ya burgeshi kuma yana tsoron Kambun baka, sai ya ce "Masha Allah, Tabarakallah" ta yadda ba abun da zai samu dayan daga Kambun baka»*
*«Haka kuma idan mutum yaga abun da ya burgeshi daga Kudi ko Dukiyarsa sai ya ce " Masha Allah laa Kuwwata Illa billah" dan kada ya kwallafu da dukiyar har ta wuce iyaka a zuciyarsa , da zarar ya fadi Addu'ar tabbas ya jingina Lamarin zuwa ga wanda ya cancanta (wato ya jingina zuwa ga Allah)»*
▪️ *إذا رأى الإنسان ما يعجبه في ماله فليقل: ما شاء الله لا قوة إلا بالله؛ لِئَلاَّ يعجب بنفسه وتزهو به نفسه في هذا المال الذي أعجبه، فإذا قال: ما شاء الله لا قوة إلا بالله، فقد وكل الأمر إلى أهله تبارك وتعالى»*
📜فتاوى نور على الدرب الشريط رقم 297
*📸Bayani📸*
Yan'uwana musulmai har yanzu bamu makara ba, mu kama azkar wato zikirorin da manzon Allah ya karantar, kuma muna yinsu yadda ya koyar ba yadda wasu ke bata tsarin ba, zikiri abu ne na nutsuwa ba na hauka ba,
Muna iya kokarimmu muna daukan wanda zamu dawwama muna yi, dan kadan daga cikin Rahamar da zamu samu ita ce, Allah da kansa zai yabemu kuma zai saka Mala'ikunsa su mana Addu'a. Wan nan kawai zai gwada mana girman Zikiri (wato ambaton Allah)
Zikiri ya hada da Karanta al-Quran da sauran Azkar na barci na safe da yamma, na tafiya , na shiga kasuwa, shiga Ban daki da fitarsa da sauransu................
Allah yasa mu dace baki daya. Ameeeeen
www.hdindima.blogspot.com