*KO DABBOBI BASU HAKA! MASU YI SUNFI DABBOBI BABBANCI*
Haruna I Muhd
30th Dec, 2016.
_______________
Asl. Yan'uwana wani abun takaici ne da ban haushi ya tayar mun da hankali, a ganina masu wannan dabi'un sunfi Dabbobi dabbanci! Don na rasa da wani suna zan kirasu dashi. Wato shi ne
*Luwadi ko Madigo*
Wai ace namiji ya kwanta da namiji ko mace ta kwanta da yar'uwarta mace!!
Ko mace ce ta aure da namijin halal na aure sanda Allah ya sanya mana doka da sharadin kar a sadu da ita ta dubura, duk wanda ya aikata haka kuma yana cikin tsinuwar manzon Allah (Saw).
A 'yan kwanakin nan a ~Facebook~ na ci karo da irin wadannan lalatattun mutane, yadda suka ta kokarin in zama member a cikinsu.
Subhanal-Lah!!
Yanzu ya zama dole a kaina da ku Yan'uwana mu tashi muna tallata addinin musulunci, bawai kristoti su dinga mana tallan addininsu ba, balle lalatattu irin yan Luwadi da madigo.
Na ta gwada musu ni tsohon hanu ne don na cim ma burina ko zasu fahimci illar hakan.
Allah da kansa ya halakar da mutanen *Annabi Luud* ya kuma gwada wannan mummunar alfasha ce wacce ba wanda ya fara a duniya in ba su ba. da yake bayanin yadda ya halakar dasu, ya gwada mana ruwan duwatsu Allah ya musu ba babba ba yaro duk aka halakar dasu.
*Manzon Allah (Saw)* ma a hadisin Ibn Abbas (r.a) a lokacin da yake jero wadan da Allah ya tsine musu, har yazo kan *'yan Luwadi'* ya tsine ma duk masu aiki (luwadi) irin aikin da mutanen Annabi Lud suka yi.
A karshe dai sai (yan'Luwadin nan) suka fara fahimtar ni ba a layinsu nake ba sai suka yi blocked nawa a fcbk. Mutum guda ne kawai yanzu ya rage muke dan tattauna matsalar a addinance da hankalce da kuma illarsa.
Ina fatan duk masu irin wannan hali Allah ya shiryar mana dasu, mu kuma Allah ya karemu daga irin wannan mafi munim dabbanci. Ameeeeeeeeeeeen.
Via:
hdindima.blogspot.com
No comments:
Post a Comment