*WANKAN JANABA, AL-ADA(HAILA), BIKI(JININ HAIHUWA), KE DANI( WANKA BAYAN SADUWA), JUMA'AH, DA GAWA( WANKAN MAMACI)*
Haruna Isah Muhd
Asl. Yan'uwana ina farin ciki da fatan al-khairi ma kowa da kowa,
Kamar yadda kuke gani a taken wannan rubutu, zamu kawo dan bayani ne kan mas'alah ta wanka a musulunci.
Bayan haka shi wanka a Musulunci iri daya ne, sai dai ban banci wajen niyyar da kayi a zuciyarka.
*Yadda ake wanka*
Zamu ambato su ne daki-daki:
*1. Za a nemi ruwa mai kyau kuma ishesshe mai yalwa.*
*2. Ana shiga ban daki, Sai a tankwara abun ruwan a zuba a hanun dama sai a wanke haguna dashi, kamar mai fara wanke hanu a alola.*
*3. mutum sai ya wanke duk yadda najasa ya taba da kyau. Kuma da hanun haguna,( bayan haka sai a goge hanun a jikin bango ko a wanke da kayau)*
*4. Sai ka yi alola cikekke a bayan gidan( amma banda kafa sai a karshe)*
*5. Sai mutum ya dan saka hanu a cikin ruwan sai ya ciro ba tare da ya kamfato ba, ya dinga shafe kansan sai yaji ruwa ya taba kasan gashin kansa, sannan sai kuma ya dibo ruwa(a kamfata) sai ya wanke kai sau uku.*
*6. Sai mutum ya kamfato ruwan ya watsa ya jikinsa daga tsagin jiki na dama, daga sama har kasa a wanke.*
*7. Sai mutum ya wanke dayan gefen jikin shima daga sama har kasa. Sau uku uku.*
*8. Sai mutum ya wanke dukkan jikinsa ta ko ina a jikin, tare da cuccuda ko wani bangare da lungu na jiki*
*9. Sai a dan kauce kadan daga yadda ake tsaye a wanke kafafuwa (cikiton alolansa).*
*FARILLAI A WANKA*
Farilla na nufin abun da in basu wanka ya baci:
*1. Daura niyyah a zuciya (ba a baki ba).*
*2. Game jiki da ruwa( a tabbata ko ina a jiki ruwa ya taba).*
*3. Cuccuda duk jiki sosai yadda ya kamata.*
*4. Gaggautawa (yin wankan da hanzari a gama).*
*5. Tsattsefe gashin kai ( a tabbata ruwa ya shiga har kasan gashi).*
*NB* in mace tana da kitso ba sai ta waye ba, zata dinga tsoma hanunta ne a cikin ruwan tana dan buga kan a hankali har sai in taji ruwa ya taba kasar gashin.
*SUNNAN WANKA*
Sunnah shi ne abun da ake so mutum yayi su don koyi da fiyeyyen halitta manzon Allah (saw):
*1. Wanke hanu a farko zuwa wuyan hanu.*
*2. Kurkuran baki*
*3. Sheka ruwa a hanci (ba dandana ruwa a hanci ba).*
*4. Shafe ramin kunne.*
*MUSTAHABBAN WANKA*
Su ne abubuwan da ake so mutum yayisu don kara samun lada a wankansa:
*1. Farawa da wanke kazantar da ya taba jiki*
*2. Yin alola cikekke (wanke gabbai sau uku-uku).*
*3. Wanke jiki daga sama kafin kasa.*
*4. Wanke kai sau uku.*
*5. Komai a fara da dama kafin haguna.*
*6. Karanta ruwa( ba iyaka ga ruwan wanka, amma ana so da a takaitashe).*
*N.B*
Farillai da sunnonin nan sun riga sun gaba a cikin yadda ake ake wanka a sama, in mutum zai yi wanka kamar yadda aka ambata, to ya hada da farillai da sunnoni da mustahabbansa.
Da wannan nake fatan Yan'uwana zamu amfana, kuma zaku iya turawa sauran Yan'uwa don muyi tarayya a cikin lada. Mai gyara kofa a bude yake.
Kuma kullum mutum yake son samun sako irin wannan da wasu ma zaku iya binmu ta wannan *website*
Allah ya bamu saa ya kuma kara fahimtar damu addinin Musulunci. Ameeeeeeeeeeeen.
Via:
Hdindima.blogspot.com*