Wednesday, 30 October 2024

RAFKANWA A SALLAH BAKI DAYA KAMAR YADDA YAZO A AL-AKHDARY

BABIN RAFKANWA (WATO MANTUWA A CIKIN SALLAH) KAMAR YADDA YAZO A LITTAFIN AL-AKHDARY*


๐Ÿ”˜ Hukuncin Sujudan Rafkanwa a Sallah, Sunnah ce.

 

๐Ÿ”˜ *Qabli*:-- Idan mutum yayi ragi a Sallah, zai yi sujada guda biyu kafin yayi Sallama bayan ya kammala Tahiya, sai yayi sujadan, sannan ya sake maimaita tahiya, kafin sai yayi Sallama.


๐Ÿ”˜ *Ba'adi*:--- Idan mutum kuma yayi karin wani abu a cikin Sallah, shi yake saka yayi Sajada biyu, amma bayan yayi Sallama, san nan ya sake yin tahiya sai ya sake wata Sallamar.


*HUKUNCE-HUKUNCE QABLI DA BA'ADI*


1. Idan mutum yayi ragi kuma yayi kari lokaci daya, sai yayi Qabli (wato sujada kafin Sallama)


2. Wanda Kabli ya kamashi sai ya manta baiyi ba har yayi Sallama, in yana kusa sai yayi Ba'adi , in abun ya jima ko kuma ya yi nisa da wajen Sallahr sai ya duba, in abun da ya ragen yafi sunnoni uku ko sama da haka, Sallah ta ษ“aci, in kuma basu kai ba, sai yayi ba'a.


3. Wanda ya manta Ba'adi, duk lokacin da ya tuna zai yi koda takai shekara ne.


4. Wanda ya rage Farillah a Sallah, Sallahrsa ta baci, babu sujudan da zai gyarata, sai in ya biyata.


5. Duk wanda ya rage Mustahabbi, ba komai a kansa, Sallahrsa tayi.


6. Mutum ba zaiyi Qabli ba sai lokacin da ya rage Sunnoni har biyu ko sama da haka, amma banda Sunna ta bayyana karatu ko boye karatu, su kam suna saka yin sujada koda dayansu ne.


7. Wanda ya boye karatunsa a wajen da ake bayyanawa, zai yi Sujadan Qabli.


8. Wanda ya Bayyana karatunsa a wajen da ake boyewa zai yi Sujadan Ba'adi.


9. Wanda ya manta yayi magana a Sallah , zai yi Sujadan Ba'adi 


10. Wanda ya manta yayi Sallama a raka'a ta biyu, a salla mai raka'a uku ko hudu, bayan ya ciko zai yi Sujadan Ba'adi 


11. Wanda ya manta ya kara Raka'a daya ko biyu a Sallah, zai yi Sujadan Ba'adi 


12. Wanda ya manta ya kara raka'o'i a Sallahrsa daidai da Raka'o'in Sallahr da yake yi, Sallah ta bace (Kamar a Sallahr Asuba ya kara Raka'a biyu, ko a Magrib ya kara Raka'a uku......)


13. Duk wanda yake kokonton Sallahr ta cika ko bata cika ba, ya kaddara kawai bata cika ba ne, sai ya tashi ya cikato, Sannan sai yayi sujadan Ba'adi 


14. Duk wanda yayi Kokonto yayi Sallama ko bai yi ba, In yana kusa da wajen Sallahr, sai ya sake Sallama, kuma ba zaiyi komai na sujada ba.  in kuma ya yi nisa ko abun ya jima, Sallahrsa ta baci sai ya saketa.


15. Duk wanda kuma dabi'arsa ce yana da yawan kokonto ko yaushe (wasi-wasi), ya dage ko yaushe yana kore kokonton, amma duk lokacin da hakan ya sameshi, zai dinga yin Sujadan Ba'adi ne, ko yayi ragi ko yayi kari, duk dai Ba'adi zai dinga yi.


16. Duk wanda ya manta ya bayyana Qunutu a Sallah, ba komai a kansa, amma ba'a son yana yin hakan musamman in da gangan ne.


17. Duk wanda ya manta a Raka'o'in da ake karanta zallahn fatiha sai ya karanta Surah, ba komai a kansa (babu Qabli babu Ba'adi)


18. Duk wanda ake Sallah sai yaji wani ya ambaci sunan Manzon Allah (SAW) sai shima ya karasa, ba komai a kansa, ko da kuwa da gangan yayi hakan, ko da mantuwa ko a zaune ko a tsaye a Sallah.


19. Duk wanda a Raka'a daya ya karanta surah daya ko biyu ko sama da haka, ko kuma yana cikin karanta wan nan surar ya fita yaje wata Surah, ko kuma yana cikin karanta wan nan surah bai gama ba sai yayi Ruku'u, duk babu komai a kansa (wato babu Kabli babu Ba'adi).


20. Duk wanda yake Sallah sai wani yazo yana neman wani abu, dan ya nuna masa da hanunsa ko da kansa ko da wani abu, ba komai a kansa (Babu Qabli babu Ba'adi)

[10/30, 4:19 PM] Admin Haruna: 21. Wanda ya manta ya maimaita karanta Suratul Fatiha, zai yi Sujadan Ba'adi, in kuma da gangan yayi, Sallahrsa ta baci.


22. Duk wanda ya manta bai karanta Surah ba, har kuma ya rusuna (tsuguna) ruku'u, kar ya ce zai dawo ya tsaya dan karantata, kuma babu Komai a kansa don sunnah ce guda daya 


23. Duk wanda yake tsaye a Sallah bai tafi Ruku'u ba, ya manta wajen  karatun Surah , inda ake bayyanawa sai ya boye ko wajen boyewa ya bayyana, amma bai tafi Ruku'u ba, sai ya maimaita daidai din, kuma babu Sujuda a kansa. In kuma hakan ya shafi karatun Fatiha, ita Fatiha zai maimaitata kuma tunda har da fatiha zai yi Ba'adi. in kuma baya tsaye kuma har ya tafi ruku'u , zai lura in ya bar bayyanawa ne sai yayi QABLI, in kuma ya bar Boyewa ne, sai Yayi Ba'adi. Maganar yin Qabli da Ba'adin nan ya shafi na surahr ce ita kadai ko ita fatihan ko dukansu, tunda ya riga ya tafi ruku'u.


24. Duk wanda yayi Dariya a Sallah koda Mantuwa ko da Gangan Sallahrsa ta baci. Dan babu mai dariya a Sallah sai wanda bai san ciwon kansa ba, rafkananne, shi da ake so ya tuna yana gaban Allah ne!!.


25. Wanda yayi Murmushi a Sallah babu komai a kansa.


26. Wanda yayi kuka a Sallah don Tsoron Allah ba komai a kansa, Ana fatan Allah ya gafarta masa ne.


27. Duk wanda yake Sallah sai yaji wani ko wasu suna surutu, sai ya dan saurara masu kaษ—an, ba komai a kansa.


28. Duk wanda ya manta zaiyi tahiyar farko sai ya yunkura zai tashi zuwa raka'a ta gaba, in har hannayensa da guiwowinsa basu rabu da kasa ba, ya dawo ya zauna , sai yayi tahiyarsa, kuma babu komai a kansa. Amma in har hannayen da guiwowin sun rabu da kasa, sai ya zarce da zallahrsa kafin yayi Sallama sai yayi Qabli.  In Kuma bayan hannayensan da guiwowinsa sun rabu da kasa , sai duk da hakan ya dawo ya zauna, ko yayi da mantuwa ko yayi da gangan Sallahrsa tayi, amma anan zai yi Sujada ne bayan Sallama (BA'ADI).


29. Wanda ya manta sai ya hure abu yana cikin Sallah, zai yi sujadan Ba'adi, in kuma da Gangan ne, Sallahr ta baci sai ya saketa.


30. Duk wanda yayi Hattishawa a Sallah ba'a son ya ce Alhamdulillah, kuma ba zai amsa ma wanda ya jishi ya mayar masa ba, shi kuma in har ya ji wani ya yi Hattishawa ya ce Alhamdulillah, shi ba zai ce masa "yarhamakallah ba"  da mai Sallah zai manta bayan yayi Hattishawar sai yace Alhamdulillah duk da hakan babu komai a kansa.

[10/30, 4:33 PM] Admin Haruna: 31. Duk wanda yayi Hamma a Sallah ba komai a kansa, sai dai ana son ya rufe bakina, kuma koda wani abu zai fito ta baki ko hanci kar ya tofar a kasa, sai dai ya zuba a aljuhunsa ko wani abu na tsumma ko abun share baki, wajen zubawar ma ya kiyaye fitan harafi daga bakinsa.


32. Duk wanda yana cikin Sallah sai ya dan tsaya tunanin ko jikinsa akwai najasa ko hadashi kamar kashi, ko fitsari ko wani abu,  amma a karshe ya gane baiyi ko daya ba kuma komai nashi da tsarki. Babu komai a kansa don yayi wan nan 'yar tunani.


33. Duk wan ya waiwaya a Sallah bisa mantuwa babu komai a kansa, amma in ya yi da gangan ne hakan ya zama makaruhu (wato abun da ba'a so ya aikata) in kuma har waiwayen yakaishi ga kauce wa Gabas (Qibla) misalin har ya juya ma Gabas baya, Sallahrsa ta baci.


34. Duk wanda yayi Sallah da kayan da akwai Hariri ko Zinare ko yayi dan Satan kallo a Sallahrsa ko garin wani abu ya kalli haramun a Sallah, ya saษ“a wa Allah, Amma Sallahrsa ta inganta.


35. Duk wanda yana cikin Karatun Sallah sai ya gwamutsa da wata kalmar da bana QUR'AN ba, amma duk da hakan bata canza ma'anar ayar ba, ko kuma bata jirkiษ—a ma'anar ayar ba, babu komai a kansa, Amma in har ta bata ma'anar ko ta bata lafazin, zai yi Sujadan Ba'adi sabo da yayi karin wani abu a Sallah.


36. Duk wanda yana Sallah sai ฦŠan gyangyadi ya kamashi, babu komai a kansa, Amma in har barcin tayi nauyi, nan kam Sallahrsa ta baci har ma da Alolansa duk sun baci.


37. Idan mutum bai da Lafiya kuma a Sallah yana da nishin jinya, ba komai a kansa, ana fatan ma Allah ya gafarta masa.


38. Duk wanda ke Sallah sai tari ya dameshi ba komai a kansa, amma wanda ke tari don isar da sako ma wani ko wasu, ba'a son haka (Makruhu ne) duk da cewa hakan baya bata Sallah.


39. Duk wanda ke Sallah sai wani ya kwala masa Kira, sai ya manta yace Subhanallah! Shima babu komai a kansa.


40. Wanda ke Sallah sai ya tike a karatu kuma ya rasa wanda zai tayar dashi, sai ya bar ayar ya tafi aya ta gaba. in ita din ma ya kasa kawota, ya ci gaba da Sallahrsa babu komai a kansa, kar yace sai ya dauki QUR'AN. Amma in batan akan Fatiha ce nan dole in ta kama ya dauki QUR'AN ko wani abun da zai taimaka masa, babu komai a kansa. In har ya tsallake aya daya a cikin Fatiha zai yi Sujadan Qabli, in har yafi aya daya Sallahrsa ta baci.


41. Wanda yake Sallah sai wani a gefe ya bata a karatu sai kuma ya masa gyara, in har ba limaminsa bane Sallahrsa ta baci.


42. Mai bin liman Sallah ba zaiyi gyara ma Liman ba in ya bata a cikin Karatu, sai in Limamin yana neman a taimaka masa, ko ya ษ“ata Ma'anar Ayar.


43. Wanda yake Sallah sai tuninsa ya dan karkata zuwa tunanin Duniya, Ya rage ladansa amma Sallahrsa tayi kuma babu komai a kansa.


44. Duk wanda yake Sallah wani yazo wucewa ta gabansa shi kuma ya tunkudeshi, ko kuma da yazo yin sujada sai ya sanya gefen Goshinsa, ko kuma ya janyo wutsiyar Rawaninsa yayi Sujada akai , duk wadan nan in yayi babu komai a kansa.


45. Duk wanda yake Sallah sai amai yazo masa ba shiri ko Magos ba komai a kansa.


46. Indan Mamu (Mai bin Liman Sallah) yayi Rafkanwa duk Limaminsa ya dauke masa, sai dai in ya samu matsalar akan Farillan Sallah ne.


47. Idan Mamu (Mai bin Liman Sallah) yayi Rafkanwa ko ya fara gyangyadi ko aka Matseshi  har aka tsere masa a ruku'u, in har ba'a Raka'ar farko ba ne, in yana so zai iya yin ruku'unsa har yaje ya samu liman kafin ya taso daga Sujuda ta biyu, Idan kuma baya so, sai ya jingine Raka'ar yabi limaminsa, in liman Yayi Sallama sai ya cikato Raka'ar da ya bartan. (Babu sujada akansa)


48. Idan kuma mutum yayi Rafkanwa akan Sujuda ko ya fara gyangyadi ko kuma aka matseshi har limaminsa ya tashi ya fara wata Raka'a , in yana so sai yayi nashi sujudan yayi sauri ya samu liman kafin yayi Ruku'u, in kuma baya so, sai ya bari ya bi limaminsa, bayan anyi Sallama sai ya biya raka'ar da ya barta. Kuma lokacin biyan nan babu komai a kansa na Qabli ko Ba'adi, sai dai in a cikin biyan kuma an sake samun wata Rafkanwar daga bangarensa


49. Duk wanda yake Sallah sai Kunama tazo masa ko Maciji, sai ya kasheta, babu komai a kansa in har bai jima ba wajen kashewar ko kuma bai Juya baya ma gabas ba, in har ya jima ko ya juya bayan, sai ya yanke Sallahr.


50. Duk wanda yake kokonton yana kan Yin Wutiri ne ko kuma raka'a ta biyun Shafa'i! Sai ya kaddara ta biyun Shafa'i ce san nan in ya gama sai yayi Ba'adi, sannan kuma sai ya tashi ya kawo Wutririnsa.

[10/30, 4:54 PM] Admin Haruna: 51. Duk wanda ya manta yayi magana a tsakanin Shafa'i da Wutiri babu komai a kansa, in kuma da gangan ne, Makaruhi ne (wato ba'a son hakan) amma babu komai a kansa.


52. Wanda aka wuceshi a Sallah kuma bai samu ko raka'a daya ba, in har liman zaiyi Sajudan Qabli ko Ba'adi shi ba ruwansa, in kuma har yabi limamin to Sallahrsa ta baci sanadiyyar bin liman wajen Qabli ko Ba'adi, in kuma ya samu raka'a daya ko sama da haka, in limaminsa zai yi Qabli zai bishi, amma in Ba'adi ne sai ya gama cikato Sallahrsa kafin yayi Ba'adin. In kuma har yabi liman da mantuwa akayi Ba'adi alhali bai cikato ba, zai yi Ba'adi daga baya in kuma yayi hakan da gangan ne Sallahrsa ta baci 


53. Idan mutum yabi liman Sallah amma bai samu duka ba, da ya tashi cikatowa sai aka samu rafkanwa, to anan kam in Qabli ne ko Ba'adi ta kamashi haka zai yi, duk abun da ya faru dashi kamar yana Sallah shi kadai ne, sai yayi kokarin gyarawa.


54. Idan mutum da yabi liman Sallah bai samu Sallah duka ba, sai abu biyu suka hadu masa, misalin limaminsa Ba'adi ya kamashi,  shi kuma da ya tashi cikatowa shima sai Qabli ta kamashi, idan yayi Qablin ya wadatar ba sai yayi dayan ba.


55. Wanda ya manta baiyi Ruku'u ba sanda yana cikin Sujada kafin ya tuna, sai ya mike, kuma ana son ya dan maimaita karatu ko kadan ne, sannan yayi Ruku'un yayi sujadan, bayan ya kammala sai yayi sujadan Ba'adi.


56. Duk wanda ya manta sujada daya baiyi ba, sanda har ya mike sai ya dawo ya zauna ya yi ta, amma in har bayan sujadar da ya manta yayi tahiya, ba zai maimaita tahiyar ba. (Ya zama yayi kari a Sallah kenan)


57. Duk wanda ya manta sujada har biyu baiyi ba, nan danan ya fadi yayi sujadan, amma ba zai sake maimaita zaman da yayi ba, kuma zaiyi Sujadan Ba'adi.

58. 51. Duk wanda ya manta yayi magana a tsakanin Shafa'i da Wutiri babu komai a kansa, in kuma da gangan ne, Makaruhi ne (wato ba'a son hakan) amma babu komai a kansa.

52. Wanda aka wuceshi a Sallah kuma bai samu ko raka'a daya ba, in har liman zaiyi Sajudan Qabli ko Ba'adi shi ba ruwansa, in kuma har yabi limamin to Sallahrsa ta baci sanadiyyar bin liman wajen Qabli ko Ba'adi, in kuma ya samu raka'a daya ko sama da haka, in limaminsa zai yi Qabli zai bishi, amma in Ba'adi ne sai ya gama cikato Sallahrsa kafin yayi Ba'adi. In kuma har yabi liman da mantuwa akayi Ba'adi alhali bai cikato ba, zai yi Ba'adi daga baya in kuma yayi hakan da gangan ne Sallahrsa ta baci 

53. Idan mutum yabi liman Sallah amma bai samu duka ba, da ya tashi cikatowa sai aka samu rafkanwa, to anan kam in Qabli ko Ba'adi ta kamashi haka zai yi, duk abun da ya faru dashi kamar yana Sallah shi kadai ne, sai yayi kokarin gyarawa.

54. Idan mutum da yabi liman Sallah bai samu Sallah duka ba, sai abu biyu suka hadu masa, limamin  Ba'adi ya kamashi,  shi kuma da ya tashi cikatowa shima sai Qabli ta kamashi, idan yayi Qablin ya wadatar ba sai yayi dayan ba.

55. Wanda ya manta baiyi Ruku'u ba sanda yana cikin Sujada ya tuna, sai ya mike, kuma ana son ya dan maimaita karatu ko kadan ne, sannan yayi Ruku'un yayi sujadan, bayan ya kammala sai yayi sujadan Ba'adi.

56. Duk wanda ya manta sujada daya baiyi ba, sanda har ya mike sai ya dawo ya zauna ya yi ta, amma in har bayanta sujadan da ya manta yayi tahiya, ba zai maimaita tahiyar ba. Sannan zai yi Sujadan Ba'adi.


57. Duk wanda ya manta sujada har biyu baiyi ba, nan danan ya fadi yayi sujadan, amma ba zai sake maimaita zaman da yayi ba, kuma zaiyi Sujadan Ba'adi.


58. Wanda ya tuna baiyi Sujada ba cikin Raka'o'in farko abun ya faru, kuma har ya dago kansa daga raka'a ta gaba, sai ya ci gaba da Sallahrsa ba zai dawo da baya  ba, tunda ya kulla wata raka'a, sai ya jefar da wancan Raka'ar da aka samu matsalar, sannan ya biya raka'ar. Sai kuma yayi Sujadan Qabli,  in kuma ba'a cikin raka'ar biyun farko ba ne,  kai koma a cikinsu ne amma muddin in bai kulla raka'a ta uku ba, bayan ya biya zai yi Ba'adi ne.


59. Duk wanda yayi Sallama a zatonsa Sallarsa ta cika ne, to Sallahrsa ta baci.


60. In mutum yazo biyan Sallahr da ta wuce masa, in har Qabli ko Ba'adi ya kamashi da sauran abubuwa duk babu banbanci da Sallahr da yanzu yake yi.


61. In mutum yayi Rafkanwa a Nafila daidai yake dana Farillah, sai dai sun sha banban akan abubuwa guda hudu:- i) *Akan Fatiha* in mutum ya manta fatiha a Nafila zai ci gaba da Sallahrsa ne sai ya gama yayi Qabli amma in a Farillah ne zai jefar da Raka'ar ce ya cikato Sallahrsa sannan ya aikata abun da aka fada a sama kan wanda ya bar Sujuda a Sallahrsa. ii), iii) & iv) *Akan karatun Surah* ko *Bayyana karatu* ko *Boye karatu* wanda ya mantasu a cikin Nafila bayan yayi Ruku'u, zai ci gaba da Sallahrsa ne kuma babu komai a kansa, Sabanin na Farillah. Idan mutum ya tashi ya fara raka'a ta uku baiyi Tahiya ba a cikin Nafila, in har baiyi Ruku'u ba saiya dawo yayi sannan kuma a karshe yayi sujadan Ba'adi. In kuma har ya kulla raka'a ta ukun sai ya ci gaba da Sallahrsa sannan ya kara Raka'a ta hudu, sai yayi Sujadan Qabli, Sabanin na Farillah zai dawo ne yayi sai kuma yayi Sujadan Ba'adi. 


62. Duk wanda ya manta wani Rukuni a Nafila (Kamar Ruku'u ko Sujada ko wani gaษ“ar Sallah) bai tuna ba har yayi Sallama kuma abun ya dau lokaci, ba zai sake Sallahr ba, Sabanin na Farillah dole sai sai ya sake muddin ya tuno komai jimawa.


63. Duk wanda ya yanke Nafila da gangan ko ya bar Raka'a da Gangan ko ya bar Sujuda da gangan, Zai maimaita wan nan Nafilar komai jimawa.


64. Duk wanda yayi gyaran murya a Sallah ba komai a kansa, sai dai in ya furta wani harafi, anan kam yayi kari a Sallahrsa. (In ya furta harafi)


65. Idan Liman Yayi Mantuwa ya kara wani abu ko ya rage, Mamu (Masu bin liman) zasu ce masa *Subhanallah* in mata ne sai suyi Tafi da hanunsu


66. Idan liman ya mike  daga Raka'a ta biyu baiyi zama ba, sai ku ce masa *Subhanallah* in har ya gama tsayuwa (Hannayensa da guiwowinsa sun rabu da kasa) kuma, sai ku bishi.


67. Idan Liman ya manta ya zauna zaiyi Tahiya a Raka'a ta farko ko a ta uku, kuma masu binsa ba zaku zauna tare dashi ba, sai ku mike. Idan a wata Sallah liman yayi Sujada daya ya bar ta biyu sai ku ce masa *Subhanallah* in bai dawo yayi ba kuma kuka ga zai shiga wata raka'a sai ku mike ku bishi, amma ba zaku yi tahiya tare dashi ba ta farko ko ta biyu, kuna tsaye , in yayi Sallama sai ku cikato Raka'ar da kuka watsar sannan kuyi Sujadan Qabli. In kuna da yawa a Masallacin wajen ciko Raka'ar sai ku tura wani liman ya wuce gaba ya ciko maku Sallahrku hakan aka fi so.


68. Idan Liman ya kara Sujada , a maimakon yayi biyu sai yayi uku, kai mai binsa ba zaka yi sujadan tare dashi ba.


69. Idan ana Sallah sai liman Ya kara Raka'a (misali a Sallahr Azahar sai yayi raka'a biyar) to duk wanda Yake ganin kirgen daidai ne ko yake  kokonto zai bishi. Amma duk wanda yana da Tabbacin anyi kari ne ba zai bishi ba, sai ya zauna har su gama. Amma in mai kokonto bai bishi ba Sallahrsa ta baci, haka shima mai tabbacin ta cika in ya bishi Sallahrsa ta baci.


70. Idan Liman yayi Sallama kafin Sallah ta cika, na bayansa zasu ce masa *Subhanallah* in ya gaskata abun da suka faษ—a sai ya cika Sallahrsa sannan yayi Sujadan Ba'adi. Idan kuma yana kokonto akan wadanda suka ce Subhanallah, sai ya juyo ya tambayi adalai ko masu kima daga ciki don ya samu tabbacin hakan.  Anan ya Halatta suyi Magana a Sallahr. In kuma ya aminta da kansa cewa yayi daidai, ya ci gaba da Sallahrsa ba sai ya juyo ya tambayi kowa ba, sai dai in har wadanda ke masallaci da yawa sun ce Subhanallah, sai ya bar tashi fahimtar yabi nasu.



Allah ya bamu Nasara, ga mai bukatar Wanan Rubutu ko waninsa, ya bibiyemu a shafimmu kamar haka


Website:- 

www.hdindima.blogspot.com


 Or

https://hdindima.blogspot.com/2024/10/rafkanwa-sallah-part-01.html?m=1

Thursday, 29 February 2024

ADDU'A AKAN ‎NEMAN ‎HAIHUWA

*ADDU'A GA MAI NEMAN JUNA BIYU KO FATAN SAMUN SAUKA LAFIYA*
 
Wadan nan su ne addu'o'in da duk mai neman Haihuwa zata lizimci yi duk, a duk lokacin da tayi Salla, bayan addu'o'in bayan Sallah ko kuma bayan Nafila.

*ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ ูˆุนู„ู‰ ุงู„ ู…ุญู…ุฏ ูƒู…ุง ุตู„ูŠุช ุนู„ู‰ ุงุจุฑุงู‡ูŠู… ูˆุนู„ู‰ ุขู„ ุฅุจุฑุงู‡ูŠู… ุฅู†ูƒ ุญู…ูŠุฏ ู…ุฌูŠุฏ ، ูˆุจุงุฑูƒ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ ูˆุนู„ู‰ ุขู„ ู…ุญู…ุฏ ูƒู…ุง ุจุงุฑูƒุช ุนู„ู‰ ุงุจุฑุงู‡ูŠู… ูˆุนู„ู‰ ุขู„ ุฅุจุฑุงู‡ูŠู… ุฅู†ูƒ ุญู…ูŠุฏ ู…ุฌูŠุฏ"*


1. *"ุฑَุจِّ ู‡َุจْ ู„ِูŠ ู…ِู†ْ ู„َุฏُู†ْูƒَ ุฐُุฑِّูŠَّุฉً ุทَูŠِّุจَุฉً ุฅِู†َّูƒَ ุณَู…ِูŠุนُ ุงู„ุฏُّุนَุงุกِ "* [ุขู„ ุนู…ุฑุงู†:38]

2.  *"ุฑَุจِّ ู‡َุจْ ู„ِูŠ ู…ِู†َ ุงู„ุตَّุงู„ِุญِูŠู†َ"*  [ุงู„ุตุงูุงุช:100]، 

3. *"ุฑَุจَّู†َุง ู‡َุจْ ู„َู†َุง ู…ِู†ْ ุฃَุฒْูˆَุงุฌِู†َุง ูˆَุฐُุฑِّูŠَّุงุชِู†َุง ู‚ُุฑَّุฉَ ุฃَุนْูŠُู†ٍ ูˆَุงุฌْุนَู„ْู†َุง ู„ِู„ْู…ُุชَّู‚ِูŠู†َ ุฅِู…َุงู…ًุง"* {ุงู„ูุฑู‚ุงู†:74}.

4. *"ูŠُุฑِูŠุฏُ ุงู„ู„ู‡ ุจِูƒُู… ุงู„ูŠُุณْุฑَ ูˆَู„ุงَ ูŠُุฑูŠุฏُ ุจِูƒُู… ุงู„ุนُุณْุฑَ)"* .[ุณูˆุฑุฉ ุงู„ุจู‚ุฑุฉ، ุขูŠุฉ:185]

5. *"(ูˆَู…َุง ุชَุญْู…ِู„ُ ู…ِู†ْ ุฃُู†ْุซَู‰ ูˆَู„ุง ุชَุถَุนُ ุฅِู„َّุง ุจِุนِู„ْู…ِู‡)"* .[ุณูˆุฑุฉ ูุงุทุฑ، ุขูŠุฉ:11]

6. *"ุฅِุฐَุง ุฒُู„ْุฒِู„َุช ุงู„ุฃุฑْุถُ ุฒِู„ْุฒَุงู„َู‡ุง*ูˆَุฃَุฎْุฑَุฌุช ุงู„ุฃุฑْุถُ ุฃَุซْู‚َุงู„َู‡ุง)*.[ุณูˆุฑุฉ ุงู„ุฒู„ุฒู„ุฉ، ุขูŠุฉ:1-2]

7. *"(ูˆَู†ُู†ุฒِّู„ُ ู…ِู†َ ุงู„ู‚ُุฑْุขู†ِ ู…َุง ู‡ُูˆَ ุดِูَุงุกٌ ูˆَุฑَุญْู…َุฉٌ ู„ِู„ْู…ُุคْู…ِู†ูŠู†َ ูˆَู„ุงَ ูŠَุฒِูŠุฏُ ุงู„ุธَّุงู„ِู…ِูŠู†َ ุฅِู„ุงَّ ุฎَุณَุงุฑุงً)"* .[ุณูˆุฑุฉ ุงู„ุฅุณุฑุงุก، ุขูŠุฉ:82]

8. "*(ุฅِุฐَุง ุงู„ุณَّู…َุงุกُ ุงู†ْุดَู‚َّุชْ * ูˆَุฃَุฐِู†َุชْ ู„ِุฑَุจِّู‡َุง ูˆَุญُู‚َّุชْ * ูˆَุฅِุฐَุง ุงู„ْุฃَุฑْุถُ ู…ُุฏَّุชْ * ูˆَุฃَู„ْู‚َุชْ ู…َุง ูِูŠู‡َุง ูˆَุชَุฎَู„َّุชْ)"* [ุณูˆุฑุฉ ุงู„ุงู†ุดู‚ุงู‚، ุขูŠุฉ:1-4]

9. *"(ุฑَุจِّ ู„َุง ุชَุฐَุฑْู†ِูŠ ูَุฑْุฏًุง ูˆَุฃَู†ุชَ ุฎَูŠْุฑُ ุงู„ْูˆَุงุฑِุซِูŠู†َ)"* .[ุณูˆุฑุฉ ุงู„ุฃู†ุจูŠุงุก، ุขูŠุฉ:89]

10. *"ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ّูŠ ุฃุนูŠุฐู‡ ุจูƒ ูˆุฐุฑูŠّุชู‡ ู…ู† ุงู„ุดูŠุทุงู† ุงู„ุฑุฌูŠู…، ุงู„ู„ู‡ู… ุณู‡ّู„ ุญู…ู„ู‡، ูˆุณู‡ّู„ ูˆู„ุงุฏุชู‡، ูˆูŠุณّุฑ ุณุจูŠู„ู‡، ุฃู†ุช ุงู„ุฐูŠ ุฎู„ู‚ุชู‡، ูˆุฃู†ุช ุงู„ุฐูŠ ุฃู†ุดุฃุชู‡، ูˆุณูˆูŠّุชู‡، ุฃุจุฑุฃ ุฅู„ูŠูƒ ู…ู† ุญูˆู„ูŠ ูˆู…ู† ู‚ูˆุชูŠ، ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุฃู†ุช، ุงู„ู„ู‡ู… ุงุญูุธู‡ ู…ู† ุจูŠู† ูŠุฏูŠู‡، ูˆู…ู† ุฎู„ูู‡، ูˆุนู† ูŠู…ูŠู†ู‡، ูˆุนู† ุดู…ุงู„ู‡، ูˆุงู‚ุฐู ุงู„ุชูˆุญูŠุฏ ูู‰ ู‚ู„ุจู‡، ูˆุฃุนู†ّูŠ ุนู„ู‰ ุชุฑุจูŠุชู‡ ูŠุง ุฃุฑุญู… ุงู„ุฑّุงุญู…ูŠู†."*

11. *"ุงู„ู„ู‡ู… ุฃุนูŠุฐ ู…ุง ููŠ ุฑุญู…ูŠ ุจูƒู„ู…ุงุชูƒ ุงู„ุชّุงู…ุฉ، ูˆู…ู† ูƒู„ّ ุดูŠุทุงู† ูˆู‡ุงู…ّุฉ، ูˆู…ู† ูƒู„ّ ุนูŠู† ู„ุงู…ّุฉ، ุงู„ู„ู‡ู… ุฃุณุฃู„ูƒ ุฃู† ุชุญูุธู‡ ูˆุชุฌุนู„ู‡ ู…ุนุงูู‰ ูƒุงู…ู„ ุงู„ุฎู„ู‚ุฉ، ุงู„ู„ู‡ู… ุญุณّู† ุฎَู„ู‚ู‡ ูˆุฎُู„ู‚ู‡، ูˆุณู‡ّู„ ุญู…ู„ู‡ ูˆู…ุฎุฑุฌู‡، ูˆุงุฌุนู„ู‡ ู‚ุฑّุฉ ุนูŠู† ู„ูŠ ูˆู„ูˆุงู„ุฏู‡، ูˆุงุฌุนู„ู‡ ู…ู† ุนุจุงุฏูƒ ุงู„ุตّุงู„ุญูŠู†."*


*ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ ูˆุนู„ู‰ ุงู„ ู…ุญู…ุฏ ูƒู…ุง ุตู„ูŠุช ุนู„ู‰ ุงุจุฑุงู‡ูŠู… ูˆุนู„ู‰ ุขู„ ุฅุจุฑุงู‡ูŠู… ุฅู†ูƒ ุญู…ูŠุฏ ู…ุฌูŠุฏ ، ูˆุจุงุฑูƒ ุนู„ู‰ ู…ุญู…ุฏ ูˆุนู„ู‰ ุขู„ ู…ุญู…ุฏ ูƒู…ุง ุจุงุฑูƒุช ุนู„ู‰ ุงุจุฑุงู‡ูŠู… ูˆุนู„ู‰ ุขู„ ุฅุจุฑุงู‡ูŠู… ุฅู†ูƒ ุญู…ูŠุฏ ู…ุฌูŠุฏ"*

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*_________________________________*

Tuesday, 12 September 2023

HUKUNCIN KASUWANCI A INTERNET

*AL-MAR-ATUSSALIHA ORPHAN AND VULNERABLE FOUNDATION*
 
๐Ÿ”˜ *Hukuncin Kasuwancin Internet*

Yan'uwana musulmai mai tambaya akan masu tallan kaya ta waya ta habyar photon kayan sai su karbi kudin su kawo masu kaya.

Amsa

Tabbas Internet (yanar gizo) yana da alkhairinsa kuma yana da sharrinsa.

Kasuwanta ta Yanar gizo kamar Facebook, Twitter, Instagram, workplace, WhatsApp, Millate, da sauransu, ba haramun ba ne, hasali ma yana daga cikin alkhairin internet.

Amma yana da sharudan da malamai suka gindaya:

1. Dole ya zama mai kasuwan yana tura asalin Photon abun da zai sayo (banda yaudara, kar ya dauki photon abun da baya hanunsa)

2. Ya zama akwai alaka na Kasuwanci tsakaninsa da masu Kasuwan (In baya da shago, sai yaje ya samu mai shago, suyi ciniki, a bashi farashi, sai ya dauki zahirin photon abun ya tura wa mai saya) ya zama kamar mai talla ne.

3. In bai zama mai talla ba , dole ya zama ya mallaka da kansa kafin ya dinga tallan, (Kamar mai Dinkin kayan sawa da kanta, ko mai sayar da abu da kanta na abinci ko abun sha.)

Sannan kuma akwai dokoki kamar haka:

1. Kar mutum ya tura abun da bai da tabbaci a kansa.

2. Kar mutum ya tura abun da Musulunci ya haramta  sayarwa (kamar karin gashi, na ido ko na kai ko giya ko duk kayan shaye-shaye ......)

3. Kar mutum ya yi kasuwan da akwai ribah (interest) a cikinta

Yan'uwa wan nan shi ne bayani a takaice akan Kasuwanci na yanar gizo. Allah ya bamu nasara baki daya. 

Allah ya sa masu irin wan nan Kasuwancin zasu dinga mai da hankali sosai, dan hatsarinsa na da yawa, wanda zai iya kiyayewa Alhamdulil-Lah Katheeran ba laifi.
*______________________*

Friday, 12 May 2023

ุฃุญูƒุงู… ‏ุงู„ุนูŠุฏ

[20/04, 8:42 AM] +970 567 674 559: *⬛ ุฃุญูƒุงู… ู…ุฎุชุตุฑุฉ ููŠ ูŠูˆู… ุงู„ุนูŠุฏ ❶⬛*

*⭕ู…ุง ู‡ูŠ ุงู„ุฃุนูŠุงุฏ ุงู„ู…ุดุฑูˆุนุฉ ููŠ ุงู„ุฅุณู„ุงู…❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
▫️ุงู„ุฃุนูŠุงุฏ ุซู„ุงุซุฉ :
*1) ุงู„ูุทุฑ:* ูˆู…ู†ุงุณุจุชู‡ ุงุฎุชุชุงู… ุตูŠุงู… ุฑู…ุถุงู† .
*2) ุงู„ุฃุถุญู‰:* ูˆู…ู†ุงุณุจุชู‡ ุงุฎุชุชุงู… ุนุดุฑ ุฐูŠ ุงู„ุญุฌุฉ .
*3) ุงู„ุฌู…ุนุฉ:* ูˆู‡ูˆ ุนูŠุฏ ุงู„ุฃุณุจูˆุน ูˆู…ู†ุงุณุจุชู‡ ุงุฎุชุชุงู… ุงู„ุฃุณุจูˆุน ูˆู„ุง ูŠุญุชูู„ ุจู…ุง ุณูˆุงู‡ุง .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 191)

*⭕ู…ุง ุญูƒู… ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ู„ู„ุฑุฌุงู„❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุฐูŠ ูŠุธู‡ุฑ ุฃู† ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ูุฑุถ ุนูŠู† .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ (16/ 214).

▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุจุงุฒ ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ูุฑุถ ูƒูุงูŠุฉ ุนู†ุฏ ูƒุซูŠุฑ ู…ู† ุฃู‡ู„ ุงู„ุนู„ู… ، ูˆุฐู‡ุจ ุจุนุถ ุฃู‡ู„ ุงู„ุนู„ู… ุฅู„ู‰ ุฃู† ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ูุฑุถ ุนูŠู† ูˆู‡ุฐุง ุงู„ู‚ูˆู„ ุฃุธู‡ุฑ ููŠ ุงู„ุฃุฏู„ุฉ ูˆุฃู‚ุฑุจ ุฅู„ู‰ ุงู„ุตูˆุงุจ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (13/ 7)

▪️ ุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ :
ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏูŠู† ุงู„ูุทุฑ ูˆุงู„ุฃุถุญู‰ ูƒู„ ู…ู†ู‡ู…ุง ูุฑุถ ูƒูุงูŠุฉ، ูˆู‚ุงู„ ุจุนุถ ุฃู‡ู„ ุงู„ุนู„ู…: ุฃู†ู‡ู…ุง ูุฑุถ ุนูŠู† ูƒุงู„ุฌู…ุนุฉ؛ ูู„ุง ูŠู†ุจุบูŠ ู„ู„ู…ุคู…ู† ุชุฑูƒู‡ุง .
๐Ÿ“œุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ : (8/ 284)

*⭕ุญูƒู… ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ู„ู„ู†ุณุงุก❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุจุงุฒ ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ูŠุณู† ู„ู„ู†ุณุงุก ุญุถูˆุฑู‡ุง ู…ุน ุงู„ุนู†ุงูŠุฉ ุจุงู„ุญุฌุงุจ ูˆุงู„ุชุณุชุฑ ูˆุนุฏู… ุงู„ุชุทูŠุจ.
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (13/ 7)

▪️ ุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ : 
ุฎุฑูˆุฌ ุงู„ู†ุณุงุก ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏูŠู† ุณู†ุฉ ู…ุคูƒุฏุฉ، ู„ูƒู† ุจุดุฑุท ุฃู† ูŠุฎุฑุฌู† ู…ุชุณุชุฑุงุช ู„ุง ู…ุชุจุฑุฌุงุช. 
๐Ÿ“œุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ : (8/ 287)

▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุฐูŠ ู†ุฑู‰ ุฃู† ุงู„ู†ุณุงุก ูŠุคู…ุฑู† ุจุงู„ุฎุฑูˆุฌ ู„ู…ุตู„ู‰ ุงู„ุนูŠุฏ ูŠุดู‡ุฏู† ุงู„ุฎูŠุฑ ูˆูŠุดุงุฑูƒู† ุงู„ู…ุณู„ู…ูŠู† ููŠ ุตู„ุงุชู‡ู…، ูˆุฏุนูˆุงุชู‡ู… ู„ูƒู† ูŠุฌุจ ุนู„ูŠู‡ู† ุฃู† ูŠุฎุฑุฌู† ุชูู„ุงุช ุบูŠุฑ ู…ุชุจุฑุฌุงุช ูˆู„ุง ู…ุชุทูŠุจุงุช ููŠุฌู…ุนู† ุจูŠู† ูุนู„ ุงู„ุณู†ุฉ، ูˆุงุฌุชู†ุงุจ ุงู„ูุชู†ุฉ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 211)

*⭕ุญูƒู… ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุญู‚ ุงู„ู…ุณุงูุฑ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ุง ุชุดุฑุน ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุญู‚ ุงู„ู…ุณุงูุฑ ู„ูƒู† ุฅุฐุง ูƒุงู† ุงู„ู…ุณุงูุฑ ููŠ ุงู„ุจู„ุฏ ุงู„ุฐูŠ ุชู‚ุงู… ููŠู‡ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ูุฅู†ู‡ ูŠุคู…ุฑ ุจุงู„ุตู„ุงุฉ ู…ุน ุงู„ู…ุณู„ู…ูŠู† .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 236)

*⭕ู‡ู„ ุชู‚ุถู‰ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุฅุฐุง ูุงุชุช❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุฅุฐุง ูุงุชุชู‡ ูุฅู†ู‡ ู„ุง ูŠู‚ุถูŠู‡ุง .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 214)

*⭕ู‡ู„ ู‡ู†ุงูƒ ุตูŠุบุฉ ู…ุญููˆุธุฉ ุนู† ุงู„ุณู„ู ููŠ ุงู„ุชู‡ู†ุฆุฉ ุจุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุชู‡ู†ุฆุฉ ุจุงู„ุนูŠุฏ ู‚ุฏ ูˆู‚ุนุช ู…ู† ุจุนุถ ุงู„ุตุญุงุจุฉ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุนู†ู‡ู…، ูˆุนู„ู‰ ูุฑุถ ุฃู†ู‡ุง ู„ู… ุชู‚ุน ูุฅู†ู‡ุง ุงู„ุขู† ู…ู† ุงู„ุฃู…ูˆุฑ ุงู„ุนุงุฏูŠุฉ ุงู„ุชูŠ ุงุนุชุงุฏู‡ุง ุงู„ู†ุงุณ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 208)

▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุจุงุฒ ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ุง ุญุฑุฌ ุฃู† ูŠู‚ูˆู„ ุงู„ู…ุณู„ู… ู„ุฃุฎูŠู‡ ููŠ ูŠูˆู… ุงู„ุนูŠุฏ ุฃูˆ ุบูŠุฑู‡ ุชู‚ุจู„ ุงู„ู„ู‡ ู…ู†ุง ูˆู…ู†ูƒ ุฃุนู…ุงู„ู†ุง ุงู„ุตุงู„ุญุฉ ، ูˆู„ุง ุฃุนู„ู… ููŠ ู‡ุฐุง ุดูŠุฆุง ู…ู†ุตูˆุตุง.
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (13/ 25)

*⭕ุญูƒู… ุงู„ู…ุตุงูุญุฉ ูˆุงู„ู…ุนุงู†ู‚ุฉ ุจุนุฏ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ุง ุจุฃุณ ุจู‡ุง ู„ุฃู† ุงู„ู†ุงุณ ู„ุง ูŠุชุฎุฐูˆู†ู‡ุง ุนู„ู‰ ุณุจูŠู„ ุงู„ุชุนุจุฏ ูˆุงู„ุชู‚ุฑุจ ุฅู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนุฒ ูˆุฌู„، ูˆุฅู†ู…ุง ูŠุชุฎุฐูˆู†ู‡ุง ุนู„ู‰ ุณุจูŠู„ ุงู„ุนุงุฏุฉ، ูˆุงู„ุฅูƒุฑุงู… ูˆุงู„ุงุญุชุฑุงู… .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 209)
[20/04, 8:43 AM] +970 567 674 559: *⬛ ุฃุญูƒุงู… ู…ุฎุชุตุฑุฉ ููŠ ูŠูˆู… ุงู„ุนูŠุฏ ❷⬛*

*⭕ู…ุง ู‡ูŠ ุขุฏุงุจ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงุณุชุญุจุงุจ ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ، ูŠุฃูƒู„ ุชู…ุฑุงุช ูˆุชุฑุง ู‚ุจู„ ุงู„ุฎุฑูˆุฌ ู„ู„ุนูŠุฏ (ููŠ ุนูŠุฏ ุงู„ูุทุฑ) ، ูŠู„ุจุณ ุฃุญุณู† ุซูŠุงุจู‡ ูˆู‡ุฐุง ู„ู„ุฑุฌุงู„ ุฃู…ุง ุงู„ู†ุณุงุก ูู„ุง ุชู„ุจุณ ุงู„ุซูŠุงุจ ุงู„ุฌู…ูŠู„ุฉ ุนู†ุฏ ุฎุฑูˆุฌู‡ุง ุฅู„ู‰ ู…ุตู„ู‰ ุงู„ุนูŠุฏ ، 

ูŠุบุชุณู„ ุงู„ุฅู†ุณุงู† ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ، ูŠู‡ู†ู‰ุก ุงู„ู†ุงุณ ุจุนุถู‡ู… ุจุนุถุง ، ูŠุดุฑุน ู„ู…ู† ุฎุฑุฌ ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุฃู† ูŠุฎุฑุฌ ู…ู† ุทุฑูŠู‚ ูˆูŠุฑุฌุน ู…ู† ุขุฎุฑ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 216-223)

*⭕ู…ุง ุงู„ุณู†ุฉ ู„ู„ุฅู†ุณุงู† ู‚ุจู„ ุงู„ุตู„ุงุฉ ููŠ ุนูŠุฏ ุงู„ูุทุฑ ูˆุนูŠุฏ ุงู„ุฃุถุญู‰❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุณู†ุฉ ููŠ ุนูŠุฏ ุงู„ูุทุฑ ุฃู† ูŠุฃูƒู„ ุชู…ุฑุงุช ูˆุชุฑุง ู‚ุจู„ ุฃู† ูŠุฎุฑุฌ ุฅู„ู‰ ุงู„ู…ุตู„ู‰ ، ูˆุฃู…ุง ููŠ ุนูŠุฏ ุงู„ุฃุถุญู‰ ูุงู„ุณู†ุฉ ุฃู† ูŠุฃูƒู„ ู…ู† ุฃุถุญูŠุชู‡ ุงู„ุชูŠ ูŠุฐุจุญู‡ุง ุจุนุฏ ุงู„ุตู„ุงุฉ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 234)

*⭕ู‡ู„ ุงู„ุณู†ุฉ ุงู„ุฐู‡ุงุจ ู„ู…ุตู„ู‰ ุงู„ุนูŠุฏ ู…ุงุดูŠุง ุฃูˆ ุฑุงูƒุจุง❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ูŠุณู† ุฃู† ูŠูƒูˆู† ู…ุงุดูŠุง ุฅู„ุง ุฅุฐุง ูƒุงู† ูŠุญุชุงุฌ ุฅู„ู‰ ุงู„ุฑูƒูˆุจ ูู„ุง ุจุฃุณ ุฃู† ูŠุฑูƒุจ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 235)

*⭕ู…ุง ุงู„ุญูƒู…ุฉ ู…ู† ู…ุฎุงู„ูุฉ ุงู„ุทุฑูŠู‚ ูŠูˆู… ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุงู‚ุชุฏุงุก ุจุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ูุฅู† ู‡ุฐุง ู…ู† ุงู„ุณู†ุฉ ، ุฅุธู‡ุงุฑ ุงู„ุดุนูŠุฑุฉ، ุดุนูŠุฑุฉ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุฌู…ูŠุน ุฃุณูˆุงู‚ ุงู„ุจู„ุฏ ، ููŠู‡ ุชูู‚ุฏุง ู„ุฃู‡ู„ ุงู„ุฃุณูˆุงู‚ ู…ู† ุงู„ูู‚ุฑุงุก ูˆุบูŠุฑู‡ู… ، ุฃู† ุงู„ุทุฑูŠู‚ูŠู† ุชุดู‡ุฏุงู† ู„ู‡ ูŠูˆู… ุงู„ู‚ูŠุงู…ุฉ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 237)

*⭕ุญูƒู… ุฅู‚ุงู…ุฉ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ู…ุณุงุฌุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุชูƒุฑู‡ ุฅู‚ุงู…ุฉ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ู…ุณุงุฌุฏ ุฅู„ุง ู„ุนุฐุฑ ู„ุฃู† ุงู„ุณู†ุฉ ุฅู‚ุงู…ุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ุตุญุฑุงุก .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 230)

*⭕ู‡ู„ ูŠุดุฑุน ุฅู‚ุงู…ุฉ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ุจูˆุงุฏูŠ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุจุงุฒ ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุฅู†ู…ุง ุชู‚ุงู… ููŠ ุงู„ู…ุฏู† ูˆุงู„ู‚ุฑู‰  ูˆู„ุง ุชุดุฑุน ุฅู‚ุงู…ุชู‡ุง ููŠ ุงู„ุจูˆุงุฏูŠ ูˆุงู„ุณูุฑ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (13/9)

*⭕ุญูƒู… ุฅู‚ุงู…ุฉ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ุงุณุชุงุฏ ุงู„ุฑูŠุงุถูŠ❓*
▪️  ู‚ุงู„ ุงุจู† ุจุงุฒ ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ุง ุญุฑุฌ ููŠ ุตู„ุงุชูƒู… ููŠ ุงู„ู…ูƒุงู† ุงู„ู…ุฐูƒูˆุฑ ู…ุง ุฏุงู… ุทุงู‡ุฑุง ู„ูŠุณ ููŠู‡ ุดูŠุก ู…ู† ุงู„ู†ุฌุงุณุฉ ، ูˆุฅู† ุชูŠุณุฑ ู…ูƒุงู† ู…ุณุชู‚ู„ ุฃุญุณู† ู…ู†ู‡ ูู‡ูˆ ุฃูˆู„ู‰ ูˆุฃูุถู„ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (13/ 11)

*⭕ุญูƒู… ุชุนุฏุฏ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ุจู„ุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุฅุฐุง ุฏุนุช ุงู„ุญุงุฌุฉ ุฅู„ู‰ ุฐู„ูƒ ูู„ุง ุจุฃุณ ูƒู…ุง ุฅุฐุง ุฏุนุช ุงู„ุญุงุฌุฉ ุฅู„ู‰ ุงู„ุฌู…ุนุฉ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 224)

*⭕ู…ุง ู‡ูˆ ูˆู‚ุช ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ูˆู‚ุช ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ู…ู† ุงุฑุชูุงุน ุงู„ุดู…ุณ ู‚ูŠุฏ ุฑู…ุญ ุฅู„ู‰ ุงู„ุฒูˆุงู„، ุฅู„ุง ุฃู†ู‡ ูŠุณู† ุชู‚ุฏูŠู… ุตู„ุงุฉ ุงู„ุฃุถุญู‰ ูˆุชุฃุฎูŠุฑ ุตู„ุงุฉ ุงู„ูุทุฑ، 

ู„ู…ุง ุฑูˆูŠ ุฃู† ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุนู„ู‰ ุขู„ู‡ ูˆุณู„ู… ูƒุงู† ูŠุตู„ูŠ ุตู„ุงุฉ ุนูŠุฏ ุงู„ุฃุถุญู‰ ุฅุฐุง ุงุฑุชูุนุช ุงู„ุดู…ุณ ู‚ูŠุฏ ุฑู…ุญ، ูˆุตู„ุงุฉ ุงู„ูุทุฑ ุฅุฐุง ุงุฑุชูุนุช ู‚ูŠุฏ ุฑู…ุญูŠู† .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16-229)

*⭕ุญูƒู… ุชุญูŠุฉ ุงู„ู…ุณุฌุฏ ู‚ุจู„ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ ู‚ุงู„ ุงุจู† ุจุงุฒ ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏูŠู† ุฅุฐุง ุตู„ูŠุช ููŠ ุงู„ู…ุณุฌุฏ ูุฅู† ุงู„ู…ุดุฑูˆุน ู„ู…ู† ุฃุชู‰ ุฅู„ูŠู‡ุง ุฃู† ูŠุตู„ูŠ ุชุญูŠุฉ ุงู„ู…ุณุฌุฏ ، 

ุฃู…ุง ุฅุฐุง ุตู„ูŠุช ููŠ ุงู„ู…ุตู„ู‰ ุงู„ู…ุนุฏ ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏูŠู† ูุฅู† ุงู„ู…ุดุฑูˆุน ุนุฏู… ุงู„ุตู„ุงุฉ ู‚ุจู„ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (13/ 15-16)
[20/04, 11:28 AM] +970 567 674 559: *⬛ ุฃุญูƒุงู… ู…ุฎุชุตุฑุฉ ููŠ ูŠูˆู… ุงู„ุนูŠุฏ ❸⬛*

*⭕ู‡ู„ ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุฃุฐุงู† ูˆุฅู‚ุงู…ุฉ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ู„ูŠุณ ู„ู‡ุง ุฃุฐุงู† ูˆู„ุง ุฅู‚ุงู…ุฉ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 237)

*⭕ุญูƒู… ุงู„ู†ุฏุงุก ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุจุงุฒ ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ู†ุฏุงุก ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุจุฏุนุฉ ู„ุง ุฃุตู„ ู„ู‡ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (13/ 23)

▪️ู‚ุงู„ุช ุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ :
ุงู„ู†ุฏุงุก ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏูŠู† ุจุงู„ุตู„ุงุฉ ุฌุงู…ุนุฉ ุฃูˆ ุบูŠุฑู‡ุง ู…ู† ุงู„ูƒู„ู…ุงุช ู„ุง ูŠุฌูˆุฒ ุจู„ ู‡ูˆ ุจุฏุนุฉ ู…ุญุฏุซุฉ . 
ุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ : (8/ 316)

*⭕ุตูุฉ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
1) ูŠูƒุจุฑ ุชูƒุจูŠุฑุฉ ุงู„ุฅุญุฑุงู… ูˆูŠุณุชูุชุญ ุซู… ูŠูƒุจุฑ ุณุช ุชูƒุจูŠุฑุงุช، ุซู… ูŠู‚ุฑุฃ ุงู„ูุงุชุญุฉ ูˆุณูˆุฑุฉ ู…ุนู‡ุง: ุฅู…ุง «ุณุจุญ» ูˆุฅู…ุง «ู‚» ููŠ ุงู„ุฑูƒุนุฉ ุงู„ุฃูˆู„ู‰

2) ูˆููŠ ุงู„ุซุงู†ูŠุฉ ุฅุฐุง ู‚ุงู… ู…ู† ุงู„ุณุฌูˆุฏ ุณูŠู‚ูˆู… ู…ูƒุจุฑุงً، ุซู… ูŠูƒุจุฑ ุฎู…ุณ ุชูƒุจูŠุฑุงุช ุจุนุฏ ู‚ูŠุงู…ู‡، ุซู… ูŠู‚ุฑุฃ ุงู„ูุงุชุญุฉ ูˆุณูˆุฑุฉ، ูุฅู† ู‚ุฑุฃ ููŠ ุงู„ุฃูˆู„ู‰ «ุณุจุญ» ู‚ุฑุฃ ููŠ ุงู„ุซุงู†ูŠุฉ «ุงู„ุบุงุดูŠุฉ» ูˆุฅู† ู‚ุฑุฃ ููŠ ุงู„ุฃูˆู„ู‰ «ู‚» ู‚ุฑุฃ ููŠ ุงู„ุซุงู†ูŠุฉ «ุงู‚ุชุฑุจุช ุงู„ุณุงุนุฉ ูˆุงู†ุดู‚ ุงู„ู‚ู…ุฑ» . 
ู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16-223)

*⭕ุญูƒู… ุตู„ุงุฉ ู…ู† ุงู‚ุชุตุฑ ุนู„ู‰ ุชูƒุจูŠุฑุฉ ุงู„ุฅุญุฑุงู… ููŠ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุตู„ุงุชู‡ ุตุญูŠุญุฉ ุฅุฐุง ุงู‚ุชุตุฑ ุนู„ู‰ ุชูƒุจูŠุฑุฉ ุงู„ุฅุญุฑุงู…، ู„ุฃู† ุงู„ุชูƒุจูŠุฑุงุช ุงู„ุฒุงุฆุฏุฉ ุนู„ู‰ ุชูƒุจูŠุฑุฉ ุงู„ุฅุญุฑุงู… ุณู†ุฉ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 238)

*⭕ู…ุชู‰ ูŠุณุชูุชุญ ุฏุนุงุก ุงู„ุฅุณุชูุชุงุญ ููŠ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ูŠุณุชูุชุญ ุจุนุฏ ุชูƒุจูŠุฑุฉ ุงู„ุฅุญุฑุงู… ูˆุงู„ุฃู…ุฑ ููŠ ู‡ุฐุง ูˆุงุณุน ุญุชู‰ ู„ูˆ ุฃุฎุฑ ุงู„ุงุณุชูุชุงุญ ุฅู„ู‰ ุขุฎุฑ ุชูƒุจูŠุฑุฉ ูู„ุง ุจุฃุณ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 240)

*⭕ู…ุงุฐุง ูŠู‚ุงู„ ุจูŠู† ูƒู„ ุชูƒุจูŠุฑุฉ ูˆุชูƒุจูŠุฑุฉ ููŠ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏูŠู†❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ูŠุณ ููŠ ุฐู„ูƒ ุฐูƒุฑ ู…ุญุฏูˆุฏ ู…ุนูŠู† ุจู„ ูŠุญู…ุฏ ุงู„ู„ู‡ ูˆูŠุซู†ูŠ ุนู„ูŠู‡، ูˆูŠุตู„ูŠ ุนู„ู‰ ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ุนู„ู‰ ุฃูŠ ุตูุฉ ุดุงุก، ูˆุฅู† ุชุฑูƒู‡ ูู„ุง ุจุฃุณ ู„ุฃู†ู‡ ู…ุณุชุญุจ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ (16/ 241)

▪️ู‚ุงู„ุช ุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ : 
ูŠุดุฑุน ู„ู‡ ุฃู† ูŠุญู…ุฏ ุงู„ู„ู‡ ูˆูŠุณุจุญู‡ ูˆูŠูƒุจุฑู‡ ูˆูŠุตู„ูŠ ุนู„ู‰ ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ุจูŠู† ูƒู„ ุชูƒุจูŠุฑุชูŠู† .
๐Ÿ“œุงู„ู„ุฌู†ุฉ ุงู„ุฏุงุฆู…ุฉ : (8/ 302)

*⭕ู…ุง ุงู„ุญูƒู… ู„ูˆ ู†ุณูŠ ุชูƒุจูŠุฑุงุช ุงู„ุนูŠุฏ ุญุชู‰ ุดุฑุน ููŠ ุงู„ู‚ุฑุงุกุฉ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ูˆ ู†ุณูŠ ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ููŠ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ، ุญุชู‰ ู‚ุฑุฃ ุณู‚ุท؛ ู„ุฃู†ู‡ ุณู†ุฉ ูุงุช ู…ุญู„ู‡ุง، ูƒู…ุง ู„ูˆ ู†ุณูŠ ุงู„ุงุณุชูุชุงุญ ุญุชู‰ ู‚ุฑุฃ ูุฅู†ู‡ ูŠุณู‚ุท . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 244)

*⭕ู…ุง ุงู„ุญูƒู… ู„ูˆ ุฃุฏุฑูƒุช ุงู„ุฅู…ุงู… ูˆู‚ุฏ ูุงุชู†ูŠ ุดูŠุก ู…ู† ุงู„ุชูƒุจูŠุฑุงุช ุงู„ุฒูˆุงุฆุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุฅุฐุง ุฏุฎู„ุช ู…ุน ุงู„ุฅู…ุงู… ููŠ ุฃุซู†ุงุก ุงู„ุชูƒุจูŠุฑุงุช ููƒุจุฑ ู„ู„ุฅุญุฑุงู… ุฃูˆู„ุง ุซู… ุชุงุจุน ุงู„ุฅู…ุงู… ููŠู…ุง ุจู‚ูŠ ูˆูŠุณู‚ุท ุนู†ูƒ ู…ุง ู…ุถู‰ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 245)

*ุฅุฐุง ูุงุช ุงู„ุฅู†ุณุงู† ุดูŠุก ู…ู† ุชูƒุจูŠุฑุงุช ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุณู‚ุท ู…ุง ูุงุชู‡ ูˆู„ู… ูŠุฃุช ุจู‡، ูˆูƒุฐู„ูƒ ุฅุฐุง ู†ุณูŠู‡ ุฃูˆ ุจุนุถู‡ ุญุชู‰ ุดุฑุน ููŠ ุงู„ู‚ุฑุงุกุฉ ูุฅู†ู‡ ู„ุง ูŠุฃุชูŠ ุจู‡؛ ู„ุฃู†ู‡ ุณู†ุฉ ูุงุช ู…ุญู„ู‡ุง ، ุฃู…ุง ู„ูˆ ูุงุชุชู‡ ู…ุน ุงู„ุฅู…ุงู… ุฑูƒุนุฉ ูƒุงู…ู„ุฉ ูุฅู†ู‡ ูŠุฃุชูŠ ุจุชูƒุจูŠุฑุงุช ุชู„ูƒ ุงู„ุฑูƒุนุฉ ุงู„ูุงุฆุชุฉ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16-241)

*⭕ุฅุฐุง ุฏุฎู„ ุงู„ู…ุตู„ูŠ ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ูˆุงู„ุฅู…ุงู… ู‚ุฏ ุงู†ุชู‡ู‰ ู…ู† ุงู„ุฑูƒุนุฉ ุงู„ุฃูˆู„ู‰ ูƒูŠู ูŠู‚ุถูŠู‡ุง❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ูŠู‚ุถูŠู‡ุง ุฅุฐุง ุณู„ู… ุงู„ุฅู…ุงู… ุจุตูุชู‡ุง، ุฃูŠ ูŠู‚ุถูŠู‡ุง ุจุชูƒุจูŠุฑู‡ุง .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16-256)
[20/04, 11:29 AM] +970 567 674 559: *⬛ ุฃุญูƒุงู… ู…ุฎุชุตุฑุฉ ููŠ ูŠูˆู… ุงู„ุนูŠุฏ ❹⬛*

*⭕ุญูƒู… ุชู‚ุฏูŠู… ุฎุทุจุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุนู„ู‰ ุงู„ุตู„ุงุฉ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุชู‚ุฏูŠู… ุฎุทุจุฉ ุงู„ุนูŠุฏูŠู† ุนู„ู‰ ุงู„ุตู„ุงุฉ ุจุฏุนุฉ ุฃู†ูƒุฑู‡ุง ุงู„ุตุญุงุจุฉ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุนู†ู‡ู… .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 249)

*⭕ู‡ู„ ู„ู„ุนูŠุฏ ุฎุทุจุฉ ุฃู… ุฎุทุจุชุงู†❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุณู†ุฉ ุฃู† ุชูƒูˆู† ู„ู„ุนูŠุฏ ุฎุทุจุฉ ูˆุงุญุฏุฉ، ูˆุฅู† ุฌุนู„ู‡ุง ุฎุทุจุชูŠู† ูู„ุง ุญุฑุฌ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 248)

*⭕ู‡ู„ ูŠุจุชุฏู‰ุก ุงู„ุฎุทูŠุจ ุฎุทุจุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุจุงู„ุงุณุชุบูุงุฑ ุฃูˆ ุจุงู„ุชูƒุจูŠุฑ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุฃู…ุง ุงู„ุงุณุชุบูุงุฑ ูู„ุง ุชุณุชูุชุญ ุจู‡ ، ูˆู„ุง ุฃุนู„ู… ุฃุญุฏุง ู‚ุงู„ ุจู‡ ، ูˆุฃู…ุง ุงู„ุชุญู…ูŠุฏ، ุฃูˆ ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ูุงู„ุนู„ู…ุงุก ู…ุฎุชู„ููˆู† ููŠ ู‡ุฐุง ، ูู…ู†ู‡ู… ู…ู† ู‚ุงู„ ، ุชุจุฏุฃ ุจุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ، ูˆู…ู†ู‡ู… ู…ู† ู‚ุงู„ ، ุชุจุฏุฃ ุจุงู„ุชุญู…ูŠุฏ ๐Ÿ‘ˆ๐Ÿฝ ูˆุงู„ุฃู…ุฑ ููŠ ู‡ุฐุง ูˆุงุณุน . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 248)

*⭕ุญูƒู… ุญุถูˆุฑ ุฎุทุจุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุญุถูˆุฑู‡ุง ู„ูŠุณ ุจูˆุงุฌุจ ูู…ู† ุดุงุก ุญุถุฑ ูˆุงุณุชู…ุน ูˆุงู†ุชูุน ูˆู…ู† ุดุงุก ุงู†ุตุฑู .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 249)

*⭕ุญูƒู… ุงู„ูƒู„ุงู… ุฃุซู†ุงุก ุฎุทุจุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ุง ุดูƒ ุฃู† ู…ู† ุงู„ุฃุฏุจ ุฃู† ู„ุง ูŠุชูƒู„ู…؛ ู„ุฃู†ู‡ ุฅุฐุง ุชูƒู„ู… ุฃุดุบู„ ู†ูุณู‡، ูˆุฃุดุบู„ ุบูŠุฑู‡ ู…ู…ู† ูŠุฎุงุทุจู‡، ุฃูˆ ูŠุณู…ุนู‡ ูˆูŠุดุงู‡ุฏู‡ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 247)

*⭕ู‡ู„ ุงู„ุณู†ุฉ ุฃู† ูŠู‚ูˆู… ุงู„ุฎุทูŠุจ ููŠ ุฎุทุจุฉ ุงู„ุนูŠุฏ ุฃูˆ ูŠูƒูˆู† ุฌุงู„ุณุง❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุณู†ุฉ ููŠ ุงู„ุฎุทุจุฉ ููŠ ุงู„ุฌู…ุนุฉ ูˆุงู„ุนูŠุฏ ุฃู† ูŠูƒูˆู† ุงู„ุฎุทูŠุจ ู‚ุงุฆู…ุง .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 247)

*⭕ู‡ู„ ูŠุณู† ู„ู„ุฅู…ุงู… ุฃู† ูŠุฎุทุจ ุนู„ู‰ ู…ู†ุจุฑ ููŠ ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ูŠุฑู‰ ุจุนุถ ุงู„ุนู„ู…ุงุก ุฃู†ู‡ ุณู†ุฉ ، ูˆุฐู‡ุจ ุจุนุถ ุงู„ุนู„ู…ุงุก ุฅู„ู‰ ุฃู† ุงู„ุฎุทุจุฉ ุจุฏูˆู† ู…ู†ุจุฑ ุฃูˆู„ู‰ ، ูˆุงู„ุฃู…ุฑ ููŠ ู‡ุฐุง ูˆุงุณุน . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 250)

*⭕ู…ุชู‰ ูŠุจุชุฏู‰ุก ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ูˆูŠู†ุชู‡ูŠ ู„ุนูŠุฏ ุงู„ูุทุฑ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ูŠูˆู… ุงู„ุนูŠุฏ ูŠุจุชุฏู‰ุก ู…ู† ุบุฑูˆุจ ุงู„ุดู…ุณ ุขุฎุฑ ูŠูˆู… ู…ู† ุฑู…ุถุงู†، ุฅู„ู‰ ุฃู† ูŠุญุถุฑ ุงู„ุฅู…ุงู… ู„ุตู„ุงุฉ ุงู„ุนูŠุฏ . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 259)

*⭕ู…ุง ู‡ูŠ ุตูุฉ ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ููŠ ุงู„ุนูŠุฏูŠู†❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
*▫️ุตูุชู‡ ุฃู† ูŠู‚ูˆู„ :*

ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ، ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุงู„ู„ู‡

ูˆุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ، ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ ูˆู„ู„ู‡ ุงู„ุญู…ุฏ

*▫️ุฃูˆ ูŠู‚ูˆู„ :*

ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ، ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ، ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุงู„ู„ู‡

ูˆุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ ุงู„ู„ู‡ ุฃูƒุจุฑ ูˆู„ู„ู‡ ุงู„ุญู…ุฏ .
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 259)

*⭕ู…ุง ุญูƒู… ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ุงู„ุฌู…ุงุนูŠ ููŠ ุฃูŠุงู… ุงู„ุฃุนูŠุงุฏ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ุงู„ุฌู…ุงุนูŠ ููŠ ุงู„ุฃุนูŠุงุฏ ุบูŠุฑ ู…ุดุฑูˆุน ، ูˆุงู„ุณู†ุฉ ููŠ ุฐู„ูƒ ุฃู† ุงู„ู†ุงุณ ูŠูƒุจุฑูˆู† ุจุตูˆุช ู…ุฑุชูุน ูƒู„ ูŠูƒุจุฑ ูˆุญุฏู‡ . 
ู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 268)

*⭕ู…ุง ุฑุฃูŠูƒู… ููŠู…ู† ูŠูƒุจุฑ ููŠ ุงู„ู…ุณุฌุฏ ููŠ ุฃูŠุงู… ุงู„ุนูŠุฏ ุนุจุฑ ู…ูƒุจุฑ ุงู„ุตูˆุช ูˆูŠุชุงุจุนู‡ ุงู„ุนุงู…ุฉ ูŠูƒุจุฑูˆู† ุฎู„ูู‡❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ุฃุฎุดู‰ ุฃู† ูŠูƒูˆู† ุฐู„ูƒ ู…ู† ุจุงุจ ุงู„ุชู†ุทุน . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 260)

*⭕ู‡ู„ ูŠู‚ุฏู… ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ุนู„ู‰ ุงู„ุฐูƒุฑ ุงู„ุฐูŠ ุฏุจุฑ ูƒู„ ุตู„ุงุฉ❓*
▪️ู‚ุงู„ ุงู„ุนู„ุงู…ุฉ ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ :
ู„ู… ูŠุฑุฏ ุนู† ุงู„ู†ุจูŠ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ู†ุต ุตุญูŠุญ ุตุฑูŠุญ ููŠ ุจุงุจ ุงู„ุชูƒุจูŠุฑ ุงู„ู…ู‚ูŠุฏ، ู„ูƒู†ู‡ ุขุซุงุฑ ูˆุงุฌุชู‡ุงุฏุงุช ู…ู† ุงู„ุนู„ู…ุงุก، ูˆู‡ุคู„ุงุก ูŠู‚ูˆู„ูˆู†: ุฅู†ู‡ ูŠู‚ุฏู…ู‡ ุนู„ู‰ ุงู„ุฐูƒุฑ ุงู„ุนุงู… ุฃุฏุจุงุฑ ุงู„ุตู„ูˆุงุช . 
๐Ÿ“œู…ุฌู…ูˆุน ุงู„ูุชุงูˆู‰ : (16/ 261)

Saturday, 25 March 2023

ูˆูุงุฉ ‏ุงู„ุณู„ู

*๐Ÿ›‘ ุชุงุฑูŠู€ุฎ ูˆูู€ุงุฉ ุนุธู…ู€ุงุก ุงู„ุงุณู€ู„ุงู… ุงู„ุฐูŠู€ู† ูŠูƒุซู€ุฑ ุงู„ุณู€ุคุงู„ ุนู†ู‡ู€ู… :*

*๐Ÿ“’ ู…ุญู…ุฏ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… 11 ู‡ุฌุฑูŠ*
๐Ÿ“• ุฃุจูˆ ุจูƒุฑ ุงู„ุตุฏูŠู‚ 13 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุนู…ุฑ ุจู† ุงู„ุฎุทุงุจ 23 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ ุนุซู…ุงู† ุจู† ุนูุงู† 35 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุนู„ูŠ ุจู† ุฃุจูŠ ุทุงู„ุจ 40 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุนุงุฆุดุฉ ุจู†ุช ุฃุจูŠ ุจูƒุฑ 57 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ุงุจู† ุนุจุงุณ 68 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงุจู† ุนู…ุฑ 73 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุณุนูŠุฏ ุจู† ุงู„ู…ุณูŠุจ 94 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ ุนู…ุฑ ุจู† ุนุจุฏ ุงู„ุนุฒูŠุฒ 101 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงู„ุญุณู† ุงู„ุจุตุฑูŠ 110 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ุฃุจูˆ ุญู†ูŠูู‡ 150ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ู…ุงู„ูƒ ุจู† ุฃู†ุณ 179 ู‡ุฌุฑูŠู‡
๐Ÿ“˜ ุงู„ุดุงูุนูŠ 204 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ุงุจู† ุฑุงู‡ูˆูŠู‡ 238 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ ุฃุญู…ุฏ ุจู† ุญู†ุจู„ 241 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“—ุฃุญู…ุฏ ุจู† ุณุนูŠุฏ ุงู„ุฏุงุฑู…ูŠ 253 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุนุจุฏ ุงู„ู„ู‡ ุจู† ุนุจุฏ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฏุงุฑู…ูŠ 255 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงู„ุจุฎุงุฑูŠ 256 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ู…ุณู„ู… 261 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงุจู† ู…ุงุฌู‡ 273 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุฃุจูˆ ุฏุงูˆุฏ 275 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ ุงู„ุชุฑู…ุฐูŠ 279 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“—ุนุซู…ุงู† ุจู† ุณุนูŠุฏ ุงู„ุฏุงุฑู…ูŠ 280ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงู„ู†ุณุงุฆูŠ 303 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ุงุจู† ุฌุฑูŠุฑ ุงู„ุทุจุฑูŠ 310 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุงุจู† ุฎุฒูŠู…ุฉ 311 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ุงุจู† ุญุจุงู† 354 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ ุงู„ุฏุงุฑู‚ุทู†ูŠ 385 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงู„ุญุงูƒู… 405 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงุจู† ุญุฒู… 456 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุงู„ุจูŠู‡ู‚ูŠ 458 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ุงุจู† ุนุจุฏ ุงู„ุจุฑ 463 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงู„ุฎุทูŠุจ ุงู„ุจุบุฏุงุฏูŠ 463 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงุจู† ุงู„ุนุฑุจูŠ 543 ู‡ุฌุฑูŠ 
๐Ÿ“˜ ุงุจู† ุฑุดุฏ ุงู„ุญููŠุฏ 595 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ุงุจู† ุงู„ุฌูˆุฒูŠ 597 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงู„ู‚ุฑุทุจูŠ ุตุงุญุจ ุชูุณูŠุฑ ุงู„ุฌุงู…ุน ู„ุฃุญูƒุงู… ุงู„ู‚ุฑุขู† 671 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“•ุงู„ู†ูˆูˆูŠ 676 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงุจู† ุชูŠู…ูŠุฉ 728 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงู„ุฐู‡ุจูŠ 748 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุงุจู† ุงู„ู‚ูŠู… 751 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ ุงุจู† ูƒุซูŠุฑ 774 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงุจู† ุฑุฌุจ 795 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงุจู† ุญุฌุฑ ุงู„ุนุณู‚ู„ุงู†ูŠ 852 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงู„ุณูŠูˆุทูŠ 911 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“˜ ุงู„ุฃู…ูŠุฑ ุงู„ุตู†ุนุงู†ูŠ 1182 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“•ู…ุญู…ุฏ ุจู† ุนุจุฏ ุงู„ูˆู‡ุงุจ 1206 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“—ุงู„ุดูˆูƒุงู†ูŠ 1250 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงู„ุฃู„ูˆุณูŠ 1342 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“™ ุงุจู† ุณุนุฏูŠ 1376 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“• ุงู„ุดู†ู‚ูŠุทูŠ 1393 ู‡ุฌุฑุฉ
๐Ÿ“˜ุงุจู† ุจุงุฒ 1419 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“— ุงู„ุฃู„ุจุงู†ูŠ 1420 ู‡ุฌุฑูŠ
๐Ÿ“” ุงุจู† ุนุซูŠู…ูŠู† 1421 ู‡ุฌุฑูŠ

*⭕ .. ุฃุฑุณู„ู‡ุง ู„ู„ุทู„ุงุจ ..*
*⭕ .. ุฃุฑุณู„ู‡ุง ู„ู‚ุฑูˆุจ ุฃู†ุช ู…ุดุชุฑูƒ ููŠู‡  ..*
*๐Ÿ’กุซู‚ّู ู…ู† ุญูˆู„ูƒ ู…ู† ู‡ู… ุนุธู…ุงุก ุงู„ุฅุณู„ุงู… .*
*ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€ู€*
๐Ÿ“š  ู„ู„ุงุดุชุฑุงูƒ ููŠ *ุทَู„َู€ุจُ ุงู„ْุนِู„ْู€ู…ِ ุงู„ุดَّุฑْุนِู€ูŠِّ* ุนู„ู‰:
⇜ *ุงู„ูˆุงุชุณ ุงุจ WhatsApp*
https://chat.whatsapp.com/It1rbLAmatWLeFc0YaX1gh
⇜ *ุงู„ุชู„ูŠ ุฌุฑุงู… Telegram*
https://t.me/fwaeeds

Wednesday, 4 January 2023

NISA'U AHLUL JANNAH (MATASA)

*๐ŸŒณNISA'U AHLUL JANNAH๐ŸŒณ*

*๐Ÿ”ทMatasa Mahangan Al'ummah๐Ÿ”ท*

✍️ Haruna Isah Muhammad
hdindima@gmail.com

๐Ÿ”ถู‚ุงู„ ุญูƒูŠู…: 

*๐Ÿ’ก«ุฅุฐุง ุฃุฑุฏุช ุฃู† ุชุนุฑู ู…ุณุชู‚ุจู„ ุฃู…ุฉ ูุงู†ุธุฑ ู…ุงุฐุง ูŠูุนู„ ุดุจุงุจู‡ุง»*
๐Ÿ”ท Wani mai Hikima ya ce:

*๐Ÿ’ก«in kana son ka gane nan gaban al-Ummah (yaya zata kasance) , ka kalle me matasanta suke aikatawa a yanzu»*

๐Ÿ“– Faidodi Masu tarin Yawa

       *๐Ÿ“ปBayani๐Ÿ“ป*

✔️Yan'uwana ba abun dake haskaka yaya al'ummah zaka kasance in ba matasanta ba, in kaga sun lalace to nan gaba sai gyaran Allah.

✔️Amma in har al'ummah ta tashi da gsk har matasa suka gyaru akwai tsammanin za'a samu al'ummah mai kyau.

✔️A yanzu fa an kai Uba yana aikan dansa ya sayo masa Kayan maye, ko kaga iyaye na gani yaransu na Rawa, na wake wake, ko kaga fitsara iri daban daban.!!!

✔️Allah ya wuce maba gaba, ya kuma gyara mana matasanmu baki daya. Ameeeeeen.
www.hdindima.blogspot.com

Monday, 2 January 2023

FAIDODI MASU TARIN YAWA (RIKO DA ALLAH)

*๐Ÿ”ฒ NISA'U AHLUL JANNAH*

๐Ÿ”ทRiko da Allah

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com

๐Ÿ”บ ุณุฆู„ ุฅุจุฑุงู‡ูŠู… ุจู† ุฃุฏู‡ู…، ู„ู… ู„ุง ุชุฎุงู„ุท ุงู„ู†ุงุณ؟ 

▪️ูู‚ุงู„ : *« ุฅู† ุตุญุจุช ู…ู† ู‡ูˆ ุฏูˆู†ูŠ ุฃุฐุงู†ูŠ ุจุฌู‡ู„ู‡، ูˆุฅู† ุตุญุจุช ู…ู† ู‡ูˆ ููˆู‚ูŠ ุชูƒุจุฑ ุนู„ูŠ، ูˆุฅู† ุตุญุจุช ู…ู† ู…ุซู„ูŠ ุญุณุฏู†ูŠ (ุฅู„ุง ู…ู† ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡) ، ูุงุดุชุบู„ุช ู†ู…ู† ู„ูŠุณ ููŠ ุตุญุจุชู‡ ู…ู„ู„ ูˆู„ุง ููŠ ูˆุตู„ู‡ ุงู†ู‚ุทุงุน، ูˆู„ุง ููŠ ุงู„ุฃู†ุณ ุจู‡ ูˆุญุดุฉ».*

๐Ÿ”บ Wata rana an tambayi Ibrahim Ibn Adham, wai shin me yasa baka son yawan Mu'amala da mutane sosai ne?

▪️ Sai ya ce *:« In har na matsi wanda na fishi sai ya cutar dani da Jahilcinsa, in kuma na matsi wanda yake sama dani sai ya dinga min Girman kai, in kuma na matsi wanda muke tsara dashi sai ya min Hassada (Sai wanda Allah ya tsamar kawai), dan haka shi yasa kawai na koma na damu da wanda in na matseshi ma ba wani zamewan da zanyi, haka kuma in na gyara alaqa dashi sam bata tsinkewa, haka kuma in ka kyautata alaqa dashi ba zai taba barinka kayi kewa ba (yana nufin Allah).»*

๐Ÿ“’ Faidodi Masu tarin Yawa

       *♦️ Bayani ♦️*

✔️Wadan nan bayanai suna nuna mana ba yadda za ayi ka gamsar da mutane ko ka samu jin dadin tarayya da mutane 100%, dan haka in kana son ka samu jin dadi mai dorewa, ka koma zuwa ga Allah.

✔️Allah ya kara bamu ikon kyautata Alaqarmu dashi . Ameeeeeen.

www.hdindima.blogspot.com