Tuesday, 12 September 2023

HUKUNCIN KASUWANCI A INTERNET

*AL-MAR-ATUSSALIHA ORPHAN AND VULNERABLE FOUNDATION*
 
🔘 *Hukuncin Kasuwancin Internet*

Yan'uwana musulmai mai tambaya akan masu tallan kaya ta waya ta habyar photon kayan sai su karbi kudin su kawo masu kaya.

Amsa

Tabbas Internet (yanar gizo) yana da alkhairinsa kuma yana da sharrinsa.

Kasuwanta ta Yanar gizo kamar Facebook, Twitter, Instagram, workplace, WhatsApp, Millate, da sauransu, ba haramun ba ne, hasali ma yana daga cikin alkhairin internet.

Amma yana da sharudan da malamai suka gindaya:

1. Dole ya zama mai kasuwan yana tura asalin Photon abun da zai sayo (banda yaudara, kar ya dauki photon abun da baya hanunsa)

2. Ya zama akwai alaka na Kasuwanci tsakaninsa da masu Kasuwan (In baya da shago, sai yaje ya samu mai shago, suyi ciniki, a bashi farashi, sai ya dauki zahirin photon abun ya tura wa mai saya) ya zama kamar mai talla ne.

3. In bai zama mai talla ba , dole ya zama ya mallaka da kansa kafin ya dinga tallan, (Kamar mai Dinkin kayan sawa da kanta, ko mai sayar da abu da kanta na abinci ko abun sha.)

Sannan kuma akwai dokoki kamar haka:

1. Kar mutum ya tura abun da bai da tabbaci a kansa.

2. Kar mutum ya tura abun da Musulunci ya haramta  sayarwa (kamar karin gashi, na ido ko na kai ko giya ko duk kayan shaye-shaye ......)

3. Kar mutum ya yi kasuwan da akwai ribah (interest) a cikinta

Yan'uwa wan nan shi ne bayani a takaice akan Kasuwanci na yanar gizo. Allah ya bamu nasara baki daya. 

Allah ya sa masu irin wan nan Kasuwancin zasu dinga mai da hankali sosai, dan hatsarinsa na da yawa, wanda zai iya kiyayewa Alhamdulil-Lah Katheeran ba laifi.
*______________________*

No comments:

Post a Comment