*LALLAI BAKA SAN KO SU DIN SU WAYE BA NE*
——-UWA-——
———DA———
——-UBA-——
*BIYAYYA WA IYAYE*
Assalamu Alaikum wa Rahmatul-Lah wa Barkatuhu, Yan'uwana musulmai ina mai muku fatan al-khairi da Neman gudumawarku wajen saurarona kan wan nan takarda mai muhimmancin gaske akan _Biyayya wa iyaye_.
Bin Iyaye ibada ne wacce Allah (swt) ya wajabta akan yara da su yi wa Iyayensu, kuma ibada ce mai matukar girma wacce Allah ya jinginata da Bauta masa, sabo da matsayinta.
Ya ce :"
*( ﻭَﺍﻋْﺒُﺪُﻭﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﻻ ﺗُﺸْﺮِﻛُﻮﺍ ﺑِﻪِ ﺷَﻴْﺌﺎً ﻭَﺑِﺎﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﻳْﻦِ ﺇِﺣْﺴَﺎﻧﺎً)*
( ku bauta wa Allah, kada ku masa Shirka da komai, Iyaye kuma ku kyautata musu).
*Ibn Abbas* (RA) ya ce *:" Allah na nufin ku gwada musu tsantsan Biyayya tare da Tausasa musu, da iya xama dasu cikin taushi, kada ku kaurara harshe wajen amsa musu magana, ku dinga sa idonku kan jin dadinsu, kuma kar ku dinga daga murya sama da tasu, ku kasan ce tare dasu kamar Bawa ne da shugabansa, wajen kankan da kai da kaskantar da kai"*
Duk da na gari ba zai gushe ba yana yawan addu'a wa Iyayensa yana cewa
*ﻭَﻗُﻞْ ﺭَﺏِّ ﺍﺭْﺣَﻤْﻬُﻤَﺎ ﻛَﻤَﺎ ﺭَﺑَّﻴَﺎﻧِﻲ ﺻَﻐِﻴﺮﺍً*
*"Allah ka musu rahama(Ka Rahamushes su) kamar yadda suka raineni tun ina karami"*
Wa dan nan fa su ne Iyaye, sau nawa sukan hakura da abun da suke sha'awa dan kai kaji dadi!, sau nawa sukan hana idonsu barci dan kai!, sau nawa sukan dau nauyinka cikin Kauna!, sau nawa zaka ga iyaye na wahala dan Dansu!, ka yawaita fadin
*_(Allahummar-Hamhuma kama Rabbayani Sagiran)_*
Wai me yasa Yara yanzu su burinsu wai su rabu da Iyayensu ne kawai, Amma sun manta cewa su kuma Iyaye so suke ka ci gaba a rayuwa!
Ya kai dan'uwana ka ranta wan nan Hadith ka dau izina a ciki
Wata rana wani mutum ya zo wajen Umar Ibn Khattab ya ce masa
*" Ina da mahaufiyata, ta gama tsufa kuma wlh ko bayan gari bata iya yayi sai na kaita, ina mata Biyayya yadda ya kamata, shin na biya Hakkinta kuwa? Sai Umar ya ce " Aa, ina! ka manta ita ma ta maka wan nan aikin. kuma duk da haka burinta ka rayu ka zama wani abu a rayuwa, kai kuma gashi kana mata amma kana son ku rabu!"*
Wani abu mafi girma ya ku Yan'uwana shi ne Al-Jannah na ko wani da yana karkashin Iyayensa ne, in har basu yaba da dansu ba ba yadda za ayi ya rabauta.
Akwai wata rana wani mutum ya zo wajen manzon Allah (saw) ya ce masa yana son ya bishi yaki, sai manxon Allah ya ce *:" amma kana da mahaifiya?" Sai ya ce eeee, sai Manzon Allah ya ce :" ka je ka taimaka mata, dan Al-Jannah yana karkashin kafafuwanta".*
Wata rana manzon Allah saw ya ce, *:" Na shiga Al-Jannah sai naji ana rera karatu, sai na ce waye haka? Sai aka ce min Harith Bn Nu'aman ne, sai na ce :" kun gani sakamakon Biyayya kenan, sakamakon Biyayya kenan".* *Harith bn Nu'aman* shi ne wan da duk duniya ba wanda ya kaishi Biyayya wa Mahaifiyarsa.
*ABIN DA KAYI SHI ZAA MAKA*
mutane da dama na kuka wa musamman yadda yara ke kausasa wa mahaifansu, da yadda suke wulakantasu, amma Wallahi kowa ya sani yadda kayi haka zaa maka, duk wanda ya wulakanta iyayensa shima haka yaransa zasu wulakantashi, wanda kuwa ya gwada Biyayya wa iyayensa shima yaransa zasu
Manzon Allah (saw) ya ce
*" ﺑﺮﻭﺍ ﺁﺑﺎﺀﻛﻢ ﺗﺒﺮﻛﻢ ﺃﺑﻨﺎﺅﻛﻢ .".*
*"Kuyi Biyayya wa iyayenku, sai yaranku su muku Biyayya "*
Misali ya gaba in kuka lura da tarihin Annabi Ibrahim (as) yadda mahaifinshi ya cutar dashi amma duk da haka ya gwada masa Biyayya sau da kafa tare da soyayya har kuma da uban yaki karban Musulunci ya ce nasa
*(ﺳَﻼﻡٌ ﻋَﻠَﻴْﻚَ ﺳَﺄَﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُ ﻟَﻚَ ﺭَﺑِّﻲ ﺇِﻧَّﻪُ ﻛَﺎﻥَ ﺑِﻲ ﺣَﻔِﻴّﺎً )* ( ﻣﺮﻳﻢ)
(Aminci ya tabbata a gareka zan nema maka gafarar Ubangijin, do min yana kula dani).
Shima sanadiyar haka Allah ya bashi yaro na gari _Annabi Ismail_ har san da ya girma Allah ya umarci mahaifin da ya yankashi, amma da Biyayya sai dan ya ce wa mahaifin nasa Annabi Ibrahim
*( ﻳَﺎ ﺃَﺑَﺖِ ﺍﻓْﻌَﻞْ ﻣَﺎ ﺗُﺆْﻣَﺮُ )*
*(Ya babana aikata duk abin da aka umarceka)*
Bayan Iyayenka sun rasu ma kana da amfanin da zaka musu matukar kai na gari ne, kai ne Sadaqatul Jariya nasu. Ka dinga musu addu'a iya iyawanka.
A karshe Yan'uwana ina son in kammala wan nan takarda tawa da wan nan hadith na Manzon Allah (saw) kan duk mai son ya dinga kai ziyara wa mahaifinsa ko mahaifiyansa to ya dinga zuwa yana sada zumuncinsu, zuwa gaishe da abokansu, da sauran yan mutunci nasu ko da bayan rasuwarsu ne
ﺃﺑﻲ ﺑﺮﺩﺓ ﻗﺎﻝ : ﻗﺪﻣﺖ ﺍﻟﻤﺪﻳﻨﺔ ﻓﺄﺗﺎﻧﻲ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﻓﻘﺎﻝ : ﺃﺗﺪﺭﻱ ﻟِﻢَ ﺃﺗﻴﺘﻚ؟ ﻗﺎﻝ : ﻗﻠﺖ : ﻻ . ﻗﺎﻝ : ﺳﻤﻌﺖ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻳﻘﻮﻝ :
*" ﻣﻦ ﺃﺣﺐ ﺃﻥ ﻳﺼﻞ ﺃﺑﺎﻩ ﻓﻲ ﻗﺒﺮﻩ ﻓﻠﻴﺼﻞ ﺇﺧﻮﺍﻥ ﺃﺑﻴﻪ ﻣﻦ ﺑﻌﺪﻩ، ﻭﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﺑﻴﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﻤﺮ ﻭﺑﻴﻦ ﺃﺑﻴﻚ ﺇﺧﺎﺀً ﻭﻭﺩ، ﻓﺄﺣﺒﺒﺖ ﺃﻥ ﺃﺻﻞ ﺫﻟﻚ " .* [ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ]
Abi Bardah ya ce, wata rana na shigo madina, kawai sai Abdul-Lahi dan Umar sai yazo gaisheni sai ya ce kasan me yasa na zo gaisheka? Sai na ce masa aa. Sai ya ce naji manzon Allah (saw) ne yana cewa :
*" duk wanda yake son ya hadu da babansa yana kabari to ya dinga ziyartar Yan'uwansa( Yan'uwan baban) bayansa, sabo da ya kasance tsakanin babana Umar da Babanka akwai Yan'uwantaka da kuma soyayya, shi yasa na sadar da ita"*
Allah ya azurtani daku baki daya wajen Biyayya wa iyayenmmu baki daya.
✍ *Haruna I Muh'd*
*080 69582878*
Hdindima.blogspot.com
No comments:
Post a Comment