Wednesday, 5 December 2018

NI BAA KASHE MIN KOWA BA A YAKIN BOKO HARAM

BA WANI NAWA DA AKA KASHE NA JINI
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

✍ *Haruna I Muh'd*
        *08069582878*
Hdindima.blogspot.com
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

Assalamu Alaikum Yan'uwana maza da mata yau na tuna da irin mummunar halin da Al'ummah ta shiga ne a shekarun baya!!!!

A shekarun baya Ko ta ina ba zaman lafiya, daga kaji maganar an ta da bomb sai kaji an sace wasu ana garkuwa dasu, sai kaji wai Boko Haram.........

Abun da ya faru a baya yasa kowa ya shiga taitayinsa dole tasa muka koma ga Allah muna yawan addu'o'in zaman lafiya, Allah kuwa ya jikammu ya kawo mana sauki.

Kamar yadda muka ta addu'o'in nan yanzu haka ma ya kamata Yan'uwana kowa da kowa ya sake dukufa musamman yadda muke fuskantar zabe mai zuwa.

Fitintinu sabbi suna kara tunkarar mu, ga wata kungiya wai sabuwa ita ma ba boko Haram din ba ce, ga kuma wasu sun shiga sun kashe soji wai suna cewa su ba Boko Haram ba ne wata ce ta balle daga Boko Haram.

Manzon Allah (saw) ya fada mana addu'a ita ce takwabin mu'amini, da ita zamu iya yakan ko wace irin bala'i da ta fuskancemu.

Kuskure ne kaji wasu suna cewa _ai ni tun da aka fara baa kashe kowa nawa ba_!!!

Ya Allah ka bamu zama lafiya, wan nan sako ya kamata mu yada wa Yan'uwa a ko ina mu rike addu'o'i, a gidajemmu, kasuwannimmu, da ma Masallatanmu kamar yadda muka yi a baya.

A kashe ina addu'ar Allah ya hadamu dakai/ke a cikin ladan yada wan nan sako dan Al'ummah mu fadaka Ameeeeeen.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_________________

No comments:

Post a Comment