Monday, 11 May 2020

TSARKIN DA YAFI DACEWA DA MACE SHI NE NA RUWA BA NA DUTSE BA

TSARKIN DA YAFI DACEWA DA MACE SHI NE NA RUWA BA NA DUTSE BA

Yan'uwana mata akwai mats'ala da ta shafi maza kai tsaye, amma ban da mata, ita ce yin tsarki da dutse.

Shi namiji in ya samu kansa a inda ba ruwa ko zai hada biyu, zai iya neman duwatsu mara ( wato 3 ko 5 ko 7 ko 9 ko 11....) Dai dai inda zai tsarkaka dasu.

Amma ga bangaren mata, abun da yafi dacewa ita ce, yin amfani da ruwa a ko wani tsarki.

Imam malik ya kawo Hadith a Muwadda cewa, yaji ana tambayar Saeeed bn Musayyin kan Tsarki, sai ya ce ai tsarku da ruwa na mata ne( ma'ana) su mata da ruwa yafi dacewa.

Allah ya sa mu dace.

✍🏻 Haruna I Muhd
Hdindima@gmail.com
*Zauren Fiqhun Mata Zallah*
*———————*

Saturday, 2 May 2020

ALOLA TARE DA MIJI KO MUHARRAMI

ALOLA TARE DA MIJI KO MUHARRAMI

Yan'uwana mata akwai wata Kyakkyawar dabi'a da ya kamata mu gane,

Musulunci addini ne mai wayewa kuma wanda yake koya mana soyayya.

Abdullahi bn Umar ya rawaito Hadith cewa, Maza da mata suna Alola tare a zamanin Manzon Allah (saw).

Ba laifi ba ne ya zama in an sha ruwa ko in an zo cin abinci, ku ci tare da maigidanki, hakan na kara dankon soyayya a tsakani.

NB
Alakan cin abincin nan fa dole sai tsakanin ma'aurata ko muharramai, amma duk wanda ta ci abinci da wani kato, ta aikata shaidananci. Kuma Allah zai kamasu, balle ma har su dinga gaisawa hanu-da-hanu.

✍🏻 Admin Zauren Fiqhun Mata Zallah.
Hdindima@gmail.com

WANKAN JANABA/KO NA JIN DADI TSAKANIN MATA DA MIJINTA A BOKATI DAYA

WANKAN JANABA/KO NA JIN DADI TSAKANIN MATA DA MIJINTA A BOKATI DAYA

_Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da farinta_ dalilin wan nan karin magana ita ce, tun kafin wani mai jan kunne yazo wai yana koya wa musulmai Vuluntine day, ko ranar soyayya wacce yinta kafurci ne, tuni Islam ya koya mana soyayya mai kyau mai tsafta.

Abu ne mai kyau, ya zama in kika yi aure, ku dinga shiga ban daki da mijinki kuna wanka tare , kuna diban ruwan tare kuna cuda junanku ma, duk a ban dakin. Kuma ku kara kulla soyayya tsakaninku.

Matar Manzon Allah kuma uwar Muminai, Nana Aishatu, (ra) ta ce : "Ni din nan na kasance muna wankan Janabah tare da manzon Allah(saw) a abun wanka daya, kuma muna kamfatan ruwan tare".

*N.B*
Bai kamata mu yi aure amma mu dinga gwada wa matammu gidadanci da kauyanci ba, ko suma su dinga mana. Kamata yayi mu zama daya da juna muna wanka tare, muna aikin gida tare muna shawari tare, da abubuwa daban-daban.

A karshe ina rokon Allah ya bamu maza na gari da mata nagari, ya kuma azurtamu da zuria ta gari, ya kuma hadamu a al-Jannah baki dayammu. Ameeeeeeeeeeeeen

✍🏻 Admin Zauren Fiqhun Mata Zallah.
Hdindima@gmail.com
————————