WANKAN JANABA/KO NA JIN DADI TSAKANIN MATA DA MIJINTA A BOKATI DAYA
_Tun kafin a haifi uwar mai sabulu, balbela take da farinta_ dalilin wan nan karin magana ita ce, tun kafin wani mai jan kunne yazo wai yana koya wa musulmai Vuluntine day, ko ranar soyayya wacce yinta kafurci ne, tuni Islam ya koya mana soyayya mai kyau mai tsafta.
Abu ne mai kyau, ya zama in kika yi aure, ku dinga shiga ban daki da mijinki kuna wanka tare , kuna diban ruwan tare kuna cuda junanku ma, duk a ban dakin. Kuma ku kara kulla soyayya tsakaninku.
Matar Manzon Allah kuma uwar Muminai, Nana Aishatu, (ra) ta ce : "Ni din nan na kasance muna wankan Janabah tare da manzon Allah(saw) a abun wanka daya, kuma muna kamfatan ruwan tare".
*N.B*
Bai kamata mu yi aure amma mu dinga gwada wa matammu gidadanci da kauyanci ba, ko suma su dinga mana. Kamata yayi mu zama daya da juna muna wanka tare, muna aikin gida tare muna shawari tare, da abubuwa daban-daban.
A karshe ina rokon Allah ya bamu maza na gari da mata nagari, ya kuma azurtamu da zuria ta gari, ya kuma hadamu a al-Jannah baki dayammu. Ameeeeeeeeeeeeen
✍🏻 Admin Zauren Fiqhun Mata Zallah.
Hdindima@gmail.com
————————
No comments:
Post a Comment