*🐓AL-MAR'A ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)🐓*
🕖 *FALALAN SALLAHR WALHA, DA LOKACIN DA AKE YI DA KUMA YAWAN RAKA'O'INTA*
✍️ *Haruna Isah Muh'd*
hdindima@gmail.com
★An karbo Hadith daga Abu Zarrin (RA), lallai ya ce:
*«Gaban (gabobin jikin mutum) ko wani bawa yakan wayi gari yana da irin sadaqan da zai bayar, ko wani Tasbihu (subhanallah) na da ladan sadaqa, ko wani Hamdala (Alhamdulil-Lah) yana da ladan sadaqa, ko wani Hailala (La haula wala Quwwata Illa billahil), ko wani Kabbara (Allahu Akbar) yana da ladan sadaqa, Umurni da kyakkyawar aiki na da ladan sadaqa, hani da Mummunan aiki yana da ladan Sadaqa, abun da zai wadatar maka akan duk wadan nan duka shi ne , yin Raka'a biyu wanda mutum zai yi na Sallahr Walha»*
Sahihu Muslim (720)
★ An karbo Hadith daga Al-Qaseem Asshaibani, lallai Zaid Bn Arkam yaga wasu mutane suna Sallah da Hantsi (Sallahr walha amma da Wuri-wuri), sai ya ce masu, shin baku ganin yin Sallah ba a wan nan lokaci ba yafi falala‚
Lallai Manzon Allah (saw) ya ce *«Sallahr Bayin Allah din nan, lokacin da dan Rakumi ne ke Durkusa (wato lokacin da rana ta fito sosai kafin Azahar har dan Rakumi na jin Zafin Kasa)»*
Sahihu Muslim (748)
💡 *Lokutan Sallahr Walha:*
1. *Farkonta*
*Tana farawa ne daga lokacin da rana ta fito kamar tsayin mashi (tsayin hanun dayanku), wato bayan lokacin da aka hana yin Sallah*.
2. *Karshenta*
*Tana karewa ne lokacin da rana ta karkata daga sama, (wato lokacin Sallahr Azahar)*
*N.B*
_Lokacin da aka fi son mutum yayi shi ne lokacin da rana ta fito sosai, kamar yadda Hadith na Abu Zarrin ya gwada na baya._
*▪️FALALAN SALLAHR WALHA*
👉 1.*Wasiyya ce ta Manzon Allah (saw) da yayi wa Sahabbai kamar su Abu Huraira, abud Darda'a da Abu Zarrin, kuma ya zama na dukkan al-Ummah.*
👉 2. *Tana daidai da aikin da gabban mutum Dari Uku da Sittin za su yi (360), kamar yadda Hadith na farko ya gwada.*
👉 3. *Lallai alama ce da take gwada bawan Allah ya zama _Awwab_ (Mai mayar da duk lamuransa ma Allah), musamman in yana yinta a lokacin da aka fi so.*
👉 4. *Lallai Sallah ce da Mala'iku ke halartanta, suna zuwa lokacin da mutum yake yinta.*
👉 5. *Sallah ce da Manzon Allah (saw) ya yabi masu yinta*
*🥜 RAKA'O'INTA*
★ Mafi karancinta shi ne Raka'o'i biyu. Sabo da Hadith na abu Huraira (RA) ya ce :*«badadina Manzon Allah (saw) yamin wasiyya da abu uku, daga ciki ya kawo ya ce da Raka'o'i biyu na Dhuha»*
Bukhari (1981) , Muslim (721)
*N.B*
_Amma magana yawan Raka'o'in Walha ba iyaka, duk da akwai wadan da suka ce, mafi yawan shi ne Raka'o'i takwas, amma Nana Aishatu (RA) ta ce Manzon Allah (saw) yana Sallahr Walha Raka'a hudu, kima yana karawa)_ Muslim (719).
Allah ya karba mana dukkan Ibadunmu baki daya, ka tura ma yan'uwa dan muyi tarayya cikin ladan wan nan Nasiha ta musamman.
*______________________________*