Wednesday, 4 January 2023

NISA'U AHLUL JANNAH (MATASA)

*🌳NISA'U AHLUL JANNAH🌳*

*🔷Matasa Mahangan Al'ummah🔷*

✍️ Haruna Isah Muhammad
hdindima@gmail.com

🔶قال حكيم: 

*💡«إذا أردت أن تعرف مستقبل أمة فانظر ماذا يفعل شبابها»*
🔷 Wani mai Hikima ya ce:

*💡«in kana son ka gane nan gaban al-Ummah (yaya zata kasance) , ka kalle me matasanta suke aikatawa a yanzu»*

📖 Faidodi Masu tarin Yawa

       *📻Bayani📻*

✔️Yan'uwana ba abun dake haskaka yaya al'ummah zaka kasance in ba matasanta ba, in kaga sun lalace to nan gaba sai gyaran Allah.

✔️Amma in har al'ummah ta tashi da gsk har matasa suka gyaru akwai tsammanin za'a samu al'ummah mai kyau.

✔️A yanzu fa an kai Uba yana aikan dansa ya sayo masa Kayan maye, ko kaga iyaye na gani yaransu na Rawa, na wake wake, ko kaga fitsara iri daban daban.!!!

✔️Allah ya wuce maba gaba, ya kuma gyara mana matasanmu baki daya. Ameeeeeen.
www.hdindima.blogspot.com

Monday, 2 January 2023

FAIDODI MASU TARIN YAWA (RIKO DA ALLAH)

*🔲 NISA'U AHLUL JANNAH*

🔷Riko da Allah

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com

🔺 سئل إبراهيم بن أدهم، لم لا تخالط الناس؟ 

▪️فقال : *« إن صحبت من هو دوني أذاني بجهله، وإن صحبت من هو فوقي تكبر علي، وإن صحبت من مثلي حسدني (إلا من رحمه الله) ، فاشتغلت نمن ليس في صحبته ملل ولا في وصله انقطاع، ولا في الأنس به وحشة».*

🔺 Wata rana an tambayi Ibrahim Ibn Adham, wai shin me yasa baka son yawan Mu'amala da mutane sosai ne?

▪️ Sai ya ce *:« In har na matsi wanda na fishi sai ya cutar dani da Jahilcinsa, in kuma na matsi wanda yake sama dani sai ya dinga min Girman kai, in kuma na matsi wanda muke tsara dashi sai ya min Hassada (Sai wanda Allah ya tsamar kawai), dan haka shi yasa kawai na koma na damu da wanda in na matseshi ma ba wani zamewan da zanyi, haka kuma in na gyara alaqa dashi sam bata tsinkewa, haka kuma in ka kyautata alaqa dashi ba zai taba barinka kayi kewa ba (yana nufin Allah).»*

📒 Faidodi Masu tarin Yawa

       *♦️ Bayani ♦️*

✔️Wadan nan bayanai suna nuna mana ba yadda za ayi ka gamsar da mutane ko ka samu jin dadin tarayya da mutane 100%, dan haka in kana son ka samu jin dadi mai dorewa, ka koma zuwa ga Allah.

✔️Allah ya kara bamu ikon kyautata Alaqarmu dashi . Ameeeeeen.

www.hdindima.blogspot.com