Friday, 17 March 2017

HAKURI HAKURI

*MAI HAKURI YAKAN DAFA DUTSE HAR MA YASHA ROMONSA*

*Haruna Isah Muh'd*
Hdindima.blogspot.com

*GABATARWA*
Bismil-Lah, Imani nau'i biyu ne: Hakuri da Godiya, akan haka wajibi ne dole ko wani musulmi ya yi riko dasu, musamman hakuri wata aba ce da Allah dakansa ya sanyata ta zama wata kyauta ce da yake ba bayinsa na gari kuma wadanda ya daukakasu, don duk wata nasara tana dare da Hakuri. Zamu yi bayani akan hakuri kan bangarori kamar haka:
Ma'anar hakuri, Nau'uka na hakuri, Nassi kan hakuri, muhimmancin hakuri, falalar hakuri hanyoyin samun hakuri da kuma abubuwan da suke rusa hakuri.

*MA'ANAR HAKURI*

Hakuri kalma ce ta larabci "as-swabru" ma'ana kamewa ko katangewa. Hakan ya dace da fadin Allah
" ﻭﺍﺻﺒﺮ ﻧﻔﺴﻚ ﻣﻊ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺪﻋﻮﻥ ﺭﺑﻬﻢ ﺑﺎﻟﻐﺪﺍﺕ ﻭﺍﻟﻌﺸﻲ....."
" ka kame/ katange kanka tare da wadanda suke bauta wa Ubangijinsu safe da yamma".
A Musulunci Hakuri na nufin :- *shi ne mutum ya katange/kame kansa akan aikata wani abu ko barin wani abu don neman yardar Allah* Allah ya ce :
" ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺻﺒﺮﻭﺍ ﺍﺑﺘﻐﺎﺀ ﻭﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ "
"Su ne wadan da suka yi hakuri wajen bin Allah".

*NAU'UKA NA HAKURI*

Hakuri na da nau'uka uku kamar haka:
1. Hakuri wajen yin da'a wa Allah.
2. Hakuri wajen barin saba wa Allah.
2. Hakuri kan kaddarar da Allah ya aiko na rashin dadi.

*NASSOSI KAN HAKURI*
Akwai nassosi masu tarin yawa kan hakuri a cikin al-Qur'an da hadith, amma ga kadan daga ciki:
*Allah (swt) ya ce*
1. " ﻭﻟﺮﺑﻚ ﻓﺎﺻﺒﺮ "
" kayi hakuri game da ubangijinka(wajen masa da'a).
2-" ﻓﺎﺻﺒﺮ ﻛﻤﺎ ﺻﺒﺮ ﺃﻟﻮ ﺍﻟﻌﺰﻡ ﻣﻦ ﺍﻟﺮﺳﻞ "
"Ka yi hakuri kamar yadda manyan manzanni suka yi kafin kai".
3-" ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﺻﺒﺮﻭﺍ ﺍﺑﺘﻐﺎﺀ ﻭﺟﻪ ﺭﺑﻬﻢ .."
" su ne wadan da suka yi hakuri wajen bin Ubangijinsu...".
*Manzon Allah (saw)*
1- " ﺍﻟﺼﺒﺮ ﺿﺒﺎﺀ "
"Hakuri haske ne"
2-" ﺃﻥ ﺍﻟﻨﺼﺮ ﻣﻊ ﺍﻟﺜﺒﺮ "
"Lallai cin nasara na tare da hakuri".

*MUHIMMANCIN HAKURI*
Hakuri babbar dabi'a ce wacce ta tattara duk dabi'a ta gari, misali:
1. *Kamewa*( iffa): hakuri ce kan sha'awar farji ko na ido.
2. *Daukaka* hakuri ne kan sha'awar ciki.
3. *Boye sirri* hakuri ne kan rashin bayyana abun da bai dace a bayyana ba na magana.
4. *Zuhdu* hakuri ne kan abubuwan kyalkyali na duniya.
5. *Kana'a* hakuri ne kan wadatuwa da abun da Allah ya ba mutum.
6. *Taushin rai* hakuri ne kan bari gwada bacin rai.
7. *Jarunta* hakuri ne kan abu guda ba gudu ba ja da baya.
8. *Afwa* hakuri ne kan rashin rama Keta.
9. *Kyauta* hakuri ne kan bayarwa da rashin rowa.
10. *Dauriya* hakuri ne kan zage damtse da barin kasala.

*ALAQAR HAKURI DA CIN NASA A DUNIYA DA LAHIRA*

Anan zamu iya ganin yadda Allah (swt) ya alaqantar da cin nasa da hakuri:
١ - ﻭﺟﺰﺍﻫﻢ ﺑﻤﺎ ﺻﺒﺮﻭﺍ ﺟﻨﺔ ﻭﺣﺮﻳﺮﺍ "
"Ya sakanka musu da Al-Jannah sabo da hakuri nasu..."
٢ "- ﺃﻭﻻﺀﻙ ﻳﺠﺰﻭﻥ ﺍﻟﻐﺮﻓﺔ ﺑﻤﺎ ﺻﺒﺮﻭﺍ "
" su ne wadan da aka sakanka musu da Al-Jannah sabo da hakuri nasu"
٣ "- ﺳﻼﻡ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺑﻤﺎ ﺻﺒﺮﺗﻢ ﻓﻨﻌﻢ ﻋﻘﺒﻰ ﺍﻟﺪﺍﺭ ".
"Amincin Allah ya tabbata a gareku sabo da hakuri da kuka yi madalla da makoma mai kyau."
٤ "- ﻭﺍﺻﺒﺮ ﻭﻣﺎ ﺻﺒﺮﻙ ﺇﻻ ﻟﻠﻪ "
" ka yi hakuri, hakurinka ba ma kowa bane sai dan Allah"..

*FALALAR HAKURI*
Duk ayoyin da muka ambata zasu iya gwada mana falalar hakuri amma gasu a dunkule:
1. Allah ya alaqanta rabauta da hakuri.
2. Allah na ninka ladan masu hakuri.
3. Allah ya jingina masu hakuri a tare dashi.
" ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻊ ﺍﻟﺼﺎﺑﺮﻳﻦ "
4. A aya daya sanda Allah ya hada abubuwa guda uku wa masu hakuri: tsira,rahamar Allah, da kuma shiriyarsa.
5. Allah ya alaqanta nasara sai da hakuri.
6. Mala'iku suna sallama wa masu hakuri a Al-Jannah.
7. Allah yana son masu hakuri.
8. Allah ya gwada masu hakuri sune masu amfani da ayoyinSa.
9. Allah ya kirasu da "Ashabul Yameen" yan dama.
10. Allah ya alaqanta taqawa da hakuri.

*HANYOYIN SAMUN HAKURI*

1. Mutum yasan dabi'a da zamantakewa ta rayuwar duniya.
2. Mutum yaji cewa duk abun da ya mallaka na cikin mallakar Allah ne.
3. Mutum ya samu Yakinin samun sakamako a wajen Allah.
4. Ya dinga neman taimakon Allah.
5. Ya dinga koyi da masu hakuri.
6. Imani da kaddara da Allah ya aiko.

*ABUBUWAN DA SUKE RUSA HAKURI*

1. Debe tsammani kan rahamar Allah.
2. Yawan fushi.
3. Gaggawa.
Masha Allah, Allah ya azurta mu da hakuri. Ameeeeeeeeeeeen.

Via:
Hdindima.blogspot.com

1 comment: