ZANCE MAI KAWATARWA
HALIN DAN'ADAM
"Mun Kasance muna son abun da ya wuce, kuma fa dan ya wucen ne, da zai dawo baya sai munji mun kyamaceshi"
"نحن نحب الماضي لأنه ذهب . ولو عاد لكرهناه"
Kowa na ce wa "wan da ya tuna bara bai ji dadin bana ba"_
Kuma da bayan zai dawo shi zai fara kyamatar hakan.
Misali zaka ji ana cewa mutanen da sun more, sabo da su suna da koshin lfy, ga shi suna cin abinci mai amfani sama da namu, kuma da za'a ce a koma zamanin baya kawa sai ya kyamaci hakan, ace sai ka noma da hanunka kafin ka ci, ko sai ka taka tsawon Kilometer 100 kafin ka isa wani gari, ba mota ba machine ba waya..... Ashe kawai dan ya wuce ne muke marmarinsa.!
Misali nan kusa shi ne, zaka ji wasu na ce ai gwanda Mulkin Jonathan, wai akwai walwala da samun kudi da sauransu, ai wai gwanda walwala da tashin hankali akan yunwa!
Ayya kuma da zaa dawo mana da zamanin kowa sai ya tsani ya ganshi a lokacin.
Wan nan shi ne halin dan Adam,
Ana bukatar kullum ka kara gode wa Allah a duk lokacin da ka samu kanka.
Allah yasa mu dace
✍ Haruna I Muhammad
080 69582878
Via
Hdindima.blogspot.com
No comments:
Post a Comment