Monday, 10 June 2019

LABARIN TSOHUWA MAI YARA UKU

*UWAR MIJI DA FITSARIN KWANCE A GIDAN SURKUWARTA!!!!!!*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
✍ *Haruna I Muhammad*
*080 6958 2878*
Hdindima@gmail.com
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

*Asl. Yan'uwana wan nan labari ne mai dauke da darasi,*

*Akwai wata mata wacce ta manyanta, kuma Allah ya azurtata da yara har uku Maza, duk kansu kuwa Sun yi aure.*

*Wata-Rana wan nar mata taga girma ya kamata kuma ga tarin Arziki da ta boye ba wanda ya sani, sai tace zata gwada matan yarantan nan baki daya, duk wacce taga ta fisu kirki sai ta mallaka mata wani abu mai tsoka daga wan nan dukiya.*

*Matar nan sai ta dau aniyar zata kai musu ziyara baki daya,*

*Ran nan sai gata a gidan daya daga cikinsu, aka karbeta hanu bib-biyu, aka bata masauki.*

*Da ta kwana sai ta dibi ruwa ta zuba akan gadon, ta kira matar dantan, tace mata, 'ya ta an samu matsala fa! yau na yi fitsari akan gadon da na kwana!!!!.*

*Matar dan kuwa ta fara surutu, da cin mutunci, a karshe ma har ta ce sai dai ki wanke da kanki!*

*Haka tsohuwar nan ta wanke gadon, kuma da dantan ya dawo aka bashi labari bai ce komai wa matarsa ba.*

*Ta sallamesu ta tafi gidan daya yaron nata,*

*Tana isa gidan kuwa, sai labari ya maimaita kansa, shima aka ci mata mutunci har ta wanke kayan fitsarin.*

*Ta sallami gida na biyun ta kama hanya zuwa gidan na ukun.*

*Tana zuwa aka mata karba mai kyau. Ta sake zuba ruwa akan gadon.*

*Da gari ya waye sai matar dan ta fito, tsohuwa ta fada mata ga abun da ya faru ta mata fitsari akan gado.*

*Matar tace "Haba Mama! Ai Wallahi ba komai kar ki damu, ai wan nan girma kenan, muma ai da muke yara kun wahala damu fiye da haka, ba komai zan wanke kar ki damu."*

*Ta nemi wani kaya ta ba tsohuwar nan ta kuma wanke gadon da kanta, ta rarrashi Mahaifiyar tasu.*

*Tsohuwar nan ta sallamesu ta koma gida, daga nan sai ta tura musu cewa duk kansu su zo su sameta a gida.*

*Yaran nan kuwa kowa ya dauko matarsa suka iso, bayan sun gaisa sai Mahaifiyar ta kwashe Labarin abun da ta yi a gidajensu, ta kuma fada musu tayi haka ne da gangan dan ta gwadasu.*

*Anan dai ta musu fada sosai, ta kuma dauki dukiya mai yawa taba wacce ta ci wan nan Jarabawa. Ta ce mata in Allah yasa tsufa ya kamani sosai, ina ba da wasiyan a kaini gidan wan nan yarinyar dan ita ce zata iya kula dani da kyau.*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲

*Anan darusan dake ciki a fili suke, maza ku kara sa ido akan yadda mata ke Mu'amula da iyayensu, suma matan su kara ba da muhimmanci ga iyayen mazansu kamar yadda suke bawa iyayensu.*
☘☘☘☘☘☘
www.hdindima.blogspot.com

MADACI BISHIYA MAI AMFANI AMMA SAI DACI

*MADACI WANI BISHIYA NE MAI DACIN GASKE, AMMA KUMA YANA MAGANI, AMMA GA WANI WAI SUNANSA MADACI!!!*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
✍ Haruna I Muh'd
*080 6958 2878*
Hdindima@yahoo.com
🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Yan'uwana ku biyoni a hankali kuji hirata da Madaci.

Turkashi!! Jiya an kwalla rana matuka kuma sai gashi kafin yamma an samu ruwa, ikon Allah, nazo wucewa kenan sai na tarar da Madaci yana zaune a majalisa shi kadai, kuma abun mamaki yana cikin rana!!

*NI*: Madaci mai ke faruwa ne haka yau na ganka kamar an koroka daga gida ko baka da kudin cefane ne?!!

*MADACI*: Ka fara kenan ko, kai ko ma kaji me ke damuna baka yi ba, kawai ka hau kaina da zancen gida, gida kam ai sai wanda Allah ya bashi mata ta gari, amma in ba haka ba zaka ga yana yawo yana lissafi akan titi.

*NI*: kai madaci so kake dai sai na zauna, ni kuma yau so nake in je in karbo bashina dan naji anyi salary, sabo da masu karban salary wani lokaci ma ko isansu baya yi, kasata kenan!.

*MADACI*: Hahahahaha ai ni na riga na karbo nawa, kai ne ka makara, amma fatana kar kaje a hanya kaga kaga _Direrriya_ kaima ka nemi cikin rana ka zauna irina.

*NI*: Kai Madaci nifa ban gane ina ka dosa ba, so dai kake sai na zauna, kuma a rana, amma dan ka bani labari bari in zauna na minti uku. Amma ban gane direrriya ba!!, kana nufin zanga wata mata ta diro a KEKE NAPEP ne?

*MADACI*: Hahahahaha, abokina kenan, ni ko labari ma ba zan baka ba.

*---------------*
Sai muka zauna shiru kowa na zuwa ma kowa ido
*---------------*
*NI*: Kai ka ganka ko daman na fada maka bata min lokaci kawai zaka yi, amma sai naga kamar Zikiri Madaci yake yi, yana Astagfirul-Lah, kai sai na lura da kyau naga kamar yana son ya kawo wata aya ce a cikin al-Qur'an. Sai na ce kai Madaci me kake tattaunawa kai kadai?!.

*MADACI*: Na kasa kawo wata aya ce ta al-Qur'an, amma zan iya tuna kan gaban da zan fada maka, in kaga dama ka dauka in kuma baka so ka kama hanyarka, Allah ya kiyaye dan ban san ina zaka isa ba.

*NI*: ko zaka iya tuna sakon ayar in tuna maka?

*MADACI*: EE tana maga ne akan _Jalabib_

*NI*: Hahahahaha na ganoka ga ayar

Surah Al-Ahzab, Verse 59:

*"يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَابِيبِهِنَّ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا"*

"O Prophet! say to your wives and your daughters and the women of the believers that they let down upon them their over-garments; this will be more proper, that they may be known, and thus they will not be given trouble; and Allah is Forgiving, Merciful."

*MADACI*: yauwa na tuna wan nan ayar ce, Amma sakona ita ce, sai kuma wan nan Sallah naga mafi Yawancin yan matanmu ba adon da suke yi kamar adon GYALE, ni kuma a ganina yawancin gyalen bai rufe dukkan jikinsu, kuma abun tausayimma har da yaran malamai, kai kusan ko ina fitinar ta shiga.

*NI*: har kasa jikina yayi saniyi duk da yadda Allah yake hana mata bude jiki amma yanzu ya fara zama kamar ma ba komai ba ne.!! Allah sarki al-Ummahta!!!!.

*MADACI*: tashi ka tafi nasan ka gane me nake nufi da direrriya, ai duk macen da tasa kaya amma duk zanen halittanta ya bayyana ina ji mana tsoron kar mu fada cikin wadan da ba zasu shiga al-Jannah ba, ko kamshinta ma ba zasu ji ba. (Kasiyatun Ariyat). Inji Manzon Allah (saw).

*NI*: Lallai Madaci abun da ka fada Gsky ce Allah ya bamu ikon gyrawa.

*MADACI*: Abokina kenan bamu makara ba, mu tura wan nan sako ma kowa, amma daci gareta kamar yadda Ni madaci nake da daci.

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
www.hdindima.blogspot.com