*UWAR MIJI DA FITSARIN KWANCE A GIDAN SURKUWARTA!!!!!!*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
✍ *Haruna I Muhammad*
*080 6958 2878*
Hdindima@gmail.com
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*Asl. Yan'uwana wan nan labari ne mai dauke da darasi,*
*Akwai wata mata wacce ta manyanta, kuma Allah ya azurtata da yara har uku Maza, duk kansu kuwa Sun yi aure.*
*Wata-Rana wan nar mata taga girma ya kamata kuma ga tarin Arziki da ta boye ba wanda ya sani, sai tace zata gwada matan yarantan nan baki daya, duk wacce taga ta fisu kirki sai ta mallaka mata wani abu mai tsoka daga wan nan dukiya.*
*Matar nan sai ta dau aniyar zata kai musu ziyara baki daya,*
*Ran nan sai gata a gidan daya daga cikinsu, aka karbeta hanu bib-biyu, aka bata masauki.*
*Da ta kwana sai ta dibi ruwa ta zuba akan gadon, ta kira matar dantan, tace mata, 'ya ta an samu matsala fa! yau na yi fitsari akan gadon da na kwana!!!!.*
*Matar dan kuwa ta fara surutu, da cin mutunci, a karshe ma har ta ce sai dai ki wanke da kanki!*
*Haka tsohuwar nan ta wanke gadon, kuma da dantan ya dawo aka bashi labari bai ce komai wa matarsa ba.*
*Ta sallamesu ta tafi gidan daya yaron nata,*
*Tana isa gidan kuwa, sai labari ya maimaita kansa, shima aka ci mata mutunci har ta wanke kayan fitsarin.*
*Ta sallami gida na biyun ta kama hanya zuwa gidan na ukun.*
*Tana zuwa aka mata karba mai kyau. Ta sake zuba ruwa akan gadon.*
*Da gari ya waye sai matar dan ta fito, tsohuwa ta fada mata ga abun da ya faru ta mata fitsari akan gado.*
*Matar tace "Haba Mama! Ai Wallahi ba komai kar ki damu, ai wan nan girma kenan, muma ai da muke yara kun wahala damu fiye da haka, ba komai zan wanke kar ki damu."*
*Ta nemi wani kaya ta ba tsohuwar nan ta kuma wanke gadon da kanta, ta rarrashi Mahaifiyar tasu.*
*Tsohuwar nan ta sallamesu ta koma gida, daga nan sai ta tura musu cewa duk kansu su zo su sameta a gida.*
*Yaran nan kuwa kowa ya dauko matarsa suka iso, bayan sun gaisa sai Mahaifiyar ta kwashe Labarin abun da ta yi a gidajensu, ta kuma fada musu tayi haka ne da gangan dan ta gwadasu.*
*Anan dai ta musu fada sosai, ta kuma dauki dukiya mai yawa taba wacce ta ci wan nan Jarabawa. Ta ce mata in Allah yasa tsufa ya kamani sosai, ina ba da wasiyan a kaini gidan wan nan yarinyar dan ita ce zata iya kula dani da kyau.*
🌲🌲🌲🌲🌲🌲
*Anan darusan dake ciki a fili suke, maza ku kara sa ido akan yadda mata ke Mu'amula da iyayensu, suma matan su kara ba da muhimmanci ga iyayen mazansu kamar yadda suke bawa iyayensu.*
☘☘☘☘☘☘
www.hdindima.blogspot.com
No comments:
Post a Comment