Thursday, 7 March 2019

FIQHUN MATA (2)

*MATA KU KARA GODE WA ALLAH*
*___________*

✍ *Haruna I Muhammad*
*08069582878*
Hdindima@gmail.com

Mata a musulunci ana gwada musu Soyayya da kuma kimantasu sama da ko wace addini.

A musulunci ne fa miji ya halarta yayi wanka tare da matarsa, ya kalleta ta kalleshi kuma ko ina ya halarta ta gani haka shima.

Manzon Allah (saw) ya kasance yana wanka tare da matarsa, har Nana Aishat (RA) tace :

" Mun kasance muna wanka tare da manzon Allah a abun wanka guda daya kuma na Janaba, muna kamfatan ruwan tare."

Imam Bukhari (299)

Allah ya kara bamu ikon fahimtar musulunci.

Kar ki wuce wan nan sako baki tura wa yar'uwa musulma ta karanta ba.

Allah yasa muyi tarayya daku a lada.
🎄🎄🎄🎄🎄🎄
🌲🌲🌲🌲🌲🌲

Join Us @
*ZAUREN FIQHUN MATA ZALLAH*
Or
www.hdindima.blogspot.com

https://chat.whatsapp.com/FomGxvgI5UT9fN737GdDbV

FIQHUN MATA (1)

*ZAKI IYA WANKAN IBADA DA SAURAN RUWAN DA MIJINKI YAYI WANKAN IBADA DA ITA, HAKA SHIMA ZAI IYA YI*
*____________*

✍ *Haruna Isah Muhammad*
08069582878
www.hdindima.blogspot.com

*Assalamu Alaikum yan'uwana maza da mata kamar yadda muka yi bayani a baya kan yadda musulunci ya gwada mana yadda ake tabbatar da Soyayya a tsakanimmu har ya bamu damar muyi wanka tare, na janaba ko na jin dadi tare da mazajenmu.*

*Har ila yau musulunci ya bamu damar muyi wanka da sauran ruwan da mijimmu yayi wankan Ibada da ita ko shi yayi da namu,*

*Hakan ya tabbata cewa Manzon Allah (saw) yayi wanka da sauran ruwan da matansa suka yi, duk da hadisan sun zo har da wanda aka hana yin haka,*

*A karshe dai abun da yafi dacewa shi ne ba kokonto kan suyi wanka tare, kuma ba kokonto mace tayi da sauran na mijinta, haka shima sai dai in kamar tayi wanka ne da ya shafi kawar da wata jini, to ana son shi kar yayi.*

*Manufa dai ana son kowa ya tsarkaka ne.*

*Allah ya bamu ikon amfana da abun da muke gabatarwa ya kuma bamu ladan yadawa.*

Domin mana gyara ko ba da gudumawa
*_____________*

Hdindima@gmail.com

Pls Join Us @
*ZAUREN FIQHUN MATA ZALLA*

https://chat.whatsapp.com/FomGxvgI5UT9fN737GdDbV

Tuesday, 5 March 2019

FIQHUN MATA (4)

*FIQHUN MATA ZALLAH*
*_________*

*MATSAYIN ALOLAR MACE IN TA TABA GABANTA*

✍ *Haruna I Muhd*
*08069582878*
*hdindima@gmail.com*
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

*Assalamu Alaikum Yan'uwana mata, kamar yadda muka gabatar a sama, lallai ya tabbata a Musulunci cewa idan har Mace ko namiji bayan tayi alola sai kuma ta saka hanu a al'auranta to alola ya karye.*

*Lallai Majority na malamai suna kan wan nan fahimtar,*

*Hakan kuma yana da alaqa da wadan nan Hadiths na Manzon Allah (saw):*

*Manzon Allah ya ce: "duk wanda ya taba al-auransa to ya sake alola, haka duk macen da ta shafi farjinta to ta sake alola*

Imam Ahmad (2/223)

*Ummu Habiba ta ce taji Manzon Allah (saw) yana cewa: "Duk wanda ya shafi Farjinsa to yayi alola"*

Ibn Maja (48)

*Bisa kuma yadda malamai suke bayani cewa, sai dai in ya zama ta taba gabantan ba tare da wani abu akai ba(zallah/tsirara) amma in har da akwai wani dan kyalle ko tsumma a kai ba matsala.*

*Allah yasa mu dace baki daya, kuma kar ki wuce wan nan sako ba tare da kin yadashi a grp naki ba. Fatana Allah yasa mu dace baki daya.*

Ga masu neman shiga grp  zasu iya tuntubarmu ta

08069582878
Ko kuma
Hdindima@gmail.com

ko kuma su dinga ziyartar shafimmu

www.hdindima.blogspot.com
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

FIQHUN MATA (3)

*SHAFAN KAI AKAN HIMAR KO DAN KWALI A LOKACIN ALOLA*
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

✍ Haruna I Muhammad
08069582878
Hdindima@gmail.com
🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Lallai ya tabbata a musulunci idan namiji yazo Alola yayi shafan kai akan Rawaninsa,

Haka kuma ita ma mace tana da wan nan babbar damar.

Idan kin zo yin shafan kai sai ki dan fidda kadan daga cikin gashin farko na gaban goshinki, sai ki fara shafawa ki kuma hada da Himar naki ko dan kwali.

Duk da cewa Hadithan akwai maganganun akansu

Amma mafi inganci shi ne ya halatta tayi shafar.

Allah yasa mu dace.

Sako daga:
_*Zauren Fiqhun Mata Zallah*_

Ka tura wan nan sako zuwa grp biyu a kalla, dan muyi tarayya dakai a wajen lada.

🌻🌻🌻🌻🌻🌻