*FIQHUN MATA ZALLAH*
*_________*
*MATSAYIN ALOLAR MACE IN TA TABA GABANTA*
✍ *Haruna I Muhd*
*08069582878*
*hdindima@gmail.com*
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*Assalamu Alaikum Yan'uwana mata, kamar yadda muka gabatar a sama, lallai ya tabbata a Musulunci cewa idan har Mace ko namiji bayan tayi alola sai kuma ta saka hanu a al'auranta to alola ya karye.*
*Lallai Majority na malamai suna kan wan nan fahimtar,*
*Hakan kuma yana da alaqa da wadan nan Hadiths na Manzon Allah (saw):*
*Manzon Allah ya ce: "duk wanda ya taba al-auransa to ya sake alola, haka duk macen da ta shafi farjinta to ta sake alola*
Imam Ahmad (2/223)
*Ummu Habiba ta ce taji Manzon Allah (saw) yana cewa: "Duk wanda ya shafi Farjinsa to yayi alola"*
Ibn Maja (48)
*Bisa kuma yadda malamai suke bayani cewa, sai dai in ya zama ta taba gabantan ba tare da wani abu akai ba(zallah/tsirara) amma in har da akwai wani dan kyalle ko tsumma a kai ba matsala.*
*Allah yasa mu dace baki daya, kuma kar ki wuce wan nan sako ba tare da kin yadashi a grp naki ba. Fatana Allah yasa mu dace baki daya.*
Ga masu neman shiga grp zasu iya tuntubarmu ta
08069582878
Ko kuma
Hdindima@gmail.com
ko kuma su dinga ziyartar shafimmu
www.hdindima.blogspot.com
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
No comments:
Post a Comment