*ZAKI IYA WANKAN IBADA DA SAURAN RUWAN DA MIJINKI YAYI WANKAN IBADA DA ITA, HAKA SHIMA ZAI IYA YI*
*____________*
✍ *Haruna Isah Muhammad*
08069582878
www.hdindima.blogspot.com
*Assalamu Alaikum yan'uwana maza da mata kamar yadda muka yi bayani a baya kan yadda musulunci ya gwada mana yadda ake tabbatar da Soyayya a tsakanimmu har ya bamu damar muyi wanka tare, na janaba ko na jin dadi tare da mazajenmu.*
*Har ila yau musulunci ya bamu damar muyi wanka da sauran ruwan da mijimmu yayi wankan Ibada da ita ko shi yayi da namu,*
*Hakan ya tabbata cewa Manzon Allah (saw) yayi wanka da sauran ruwan da matansa suka yi, duk da hadisan sun zo har da wanda aka hana yin haka,*
*A karshe dai abun da yafi dacewa shi ne ba kokonto kan suyi wanka tare, kuma ba kokonto mace tayi da sauran na mijinta, haka shima sai dai in kamar tayi wanka ne da ya shafi kawar da wata jini, to ana son shi kar yayi.*
*Manufa dai ana son kowa ya tsarkaka ne.*
*Allah ya bamu ikon amfana da abun da muke gabatarwa ya kuma bamu ladan yadawa.*
Domin mana gyara ko ba da gudumawa
*_____________*
Hdindima@gmail.com
Pls Join Us @
*ZAUREN FIQHUN MATA ZALLA*
https://chat.whatsapp.com/FomGxvgI5UT9fN737GdDbV
No comments:
Post a Comment