Wednesday, 28 September 2022

BAYIN ALLAH NA DA YAWAN GASKE

*🪞AL-MAR'AH ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)🪞*

*💡WAI KANA ZATON ALLAH YA DAMU DA IBADARKA NE?!!!!💡*

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*________________________*

Assalamu Alaikum yan'uwana tabbas Allah ya kawomu Duniya ne dan muyi aiki mai kyau kuma dan kammu, in muka ki yin mai kyau ma dan kanmu!!

✔️♦️ قال رسول الله صلى عليه وسلم:

*«البيت المعمور في السماء السابعة، يدخله كل يوم ألف ملك، ثم لا يعودون إليه حتى تقوم الساعة»*

أخرجه مسلم (162) مطولا

✔️♦️Manzon Allah (saw) ya ce:

*«Masallacin Baitul Maamur da take sama ta bakwai, Mala'iku dubu ne ke shiganta a ko wani rana, kuma ba zasu sake dawowa cikinta ba har Tashin Kiyama»*

Muslim ne ya Rawaito

*🔭BAYANI🔭*

Lallai yan'uwana mu lura da kyau, tun da akayi Duniya fa, ko yaushe sai Mala'iku dubu sun shiga Masallacin nan kuma gobe ba su ba ne, sai dai wasu,har tashib Kiyama.

Hakan na gwada mana irin tarin yawan bayin Allah kenan, ko ki bauta ma Allah yadda ya kamata, dan kanki, ko ki ki, dan kanki.

Allah ya karba mana Ibadummu ba dan halimmu ba.

🖥️FOR MORE🖥️
www.hdindima.blogspot.com

No comments:

Post a Comment