*🍸AL-MAR-ATUSSALIHA ORPHANS AND VULNERABLE FOUNDATION (ZAUREN MACE TA GARI DON TALLAFA WA MARAYU DA MARASSA GALIHU)🍸*
*HADITH CLASS 23*
➐ عن عبد الرحمن بن سعد قال سمعت أبا سعيد الخدري يقول:
*« قال رسول الله صلى عليه وسلم إن من أشر الناس عند الله منزلة يوم القيامة: الرجل يفضؤ إلى امرأته وتفضي إليه ثم ينشر سرها»*
*⚫HADITH 8⚫*
✔️An karbo Hadith daga Abdurrahman bn Saad ya ce: naji Abu Saeed al-Khudry yana cewa: Manzon Allah saw ya ce:
*_« Lallai daga cikin mafi sharri kuma mai mummunar Makoma a wajen Allah a ranar Al-qiyama, shi ne mutumin da zai sake wa matarsa (ya bayyana mata tsiraici nashi) ita ma ta sake dashi (ta bayyana masa tsiraici nata) San nan ya je yana bayyana sirrinta»_*
⭕➑ عن أبي هريرة رضي الله عنه، أنه سمع رسول الله صلى عليه وسلم يقول:
*«........أسما إمرأة أدخلت على قوم من ليس منهم، فليست من الله في شيء، ولن يدخلها الله الجنة. وأيما رجل جحد ولده وهو ينظر إليه، احتجب الله تعالى عنه، وفضحه على رؤوس الأولين والآخرين»*
*⚫HADITH 8⚫*
✔️An karbo Hadith daga Abu Huraira (RA) lallai yaji Manzon Allah (saw) yana cewa:
*_«..... Duk macen da ta shigar (da yaro) ma wasu mutane, wanda kuma ba nasu ba (kamar ta ce cikin na wani ne), to bata da rabo a wajen Allah, kuma Allah ba zai shigar da ita al-Jannah ba. Haka duk mutumin da ya musanta da (wato ya ce yaron ba nasa ba ne) kuma yana kallonsa (ya san kuma nasa ne) Allah zai nisantashi daga shi (wato Allah zai shamakanceshi daga kallonsa) , kuma zai tozartashi a idon al-Ummahr farko da na karshe»_*
*🔎BAYANI🔎*
Yauwa wan nan babi ne da yake jan hankalimmu akan kyautata zamantakewa na auratayya, bai kamata bayan mace ko miji duk an aminta da juna, sai daga baya aje ana faccaka sirrin juna,.
Kuma duk wanda yasan ciki nashi ne , gwanda ya karba dan gudun abun da zai tarar a ranar kiyama, haka ma ga mata, kar mace ta jingina wani yaro ga wani dangin da ba nashi ba.
Allah ya kara bamu ikon kyautata zamantakewa a gidajemmu na aure.
*🖥️FOR MORE🖥️*
No comments:
Post a Comment