*🪞AL-MAR-ATUSSALIHA ORPHANS AND VULNERABLE FOUNDATION (ZAUREN MACE TA GARI DON TALLAFA WA MARAYU DA MARASSA GALIHU)🪞*
*🔰HADITH CLASS 25🔰*
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*_______________________*
*🔲هجرة المرأة فراش زوجها🔲*
*♦️KAURACEWAR MACE GA SHINFIDAR MIJINTA♦️*
عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى عليه وسلم
*_«إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشه، فلم تأته ، فبات غضبان عليها، لعنتها الملائكة، حتى تصبح»_*
متفق عليه
🔘Hadith 001🔘
An karbo Hadith daga Abu Huraira (RA) ya ce, Manzon Allah (saw) ya ce:
*_« idan mutum ya kira matarsa zuwa ga shinfidarsa (don saduwa ta aure) sai Taki zuwa, har ya kwana yana fushi da ita, Mala'iku zasu la'anceta har ta wayi gari»_*
Bukhari da Muslim
*_________________________*
⚪Hadith 002⚪
عن ابن عمر رضي الله عنه، أن رسول الله صلى عليه وسلم، قال،
*_«لعن الله المسوفات، التي يدعوها زوجها الى فراشه، فتقول سوف حتى يغلبه عيناه»_*
الطبراني
☑️An karbo Hadith daga dan Umar (Abdullahi dan Umar) (RA) ya ce: lallai Manzon Allah (saw) ya ce:
*_« Allah ya la'anci (ya tsine) wa macen da take cewa jirani ina zuwa, wacce idan mijinta ya kirata zuwa ga shinfidarsa (don saduwar Aure) sai ta ce masa, jirani ina zuwa, har idonsa ya rinjayeshi (har barci ya daukeshi»_*
Dabarani
*________________________*
*🔘Hadith 003🔘*
عن أبي هريرة رضي الله عنه، أن رسول الله صلى عليه وسلم قال:
«لعن الله المفسلة، التي إذا أراد زوجها أن يأتيها قالت أنا حائض»
أبو يعلى في مسنده
☑️An karbo Hadith daga Abu Huraira (RA) ya ce: lallai Manzon Allah (saw) ya ce:
*_«Allah ya la'anci mai kashe shaawar mijinta da ganganci, wacce idan mijinta ya nufeta da saduwa ta aure sai ta ce, ina Al-adah ( kuma na karya)»_*
Abu Yaalah
*________________________*
🔲BAYANI🔲
Yan'uwa mu kara kiyayewa ga yadda zamantakewarmu ke gudana, lura da hadithai din nan, suna daga cikin abubuwan da suke kawo matsalolin aure, sama da tunanin kowa,
Dan haka mu iya kokarinmu don kyautata zamantakewa.
Kuma gareku maza, dan an fadi haka, ba lasisi ba ne namiji ya cutar da matarsa, yadda muke shaawa suma haka ne, kuma Allah ya ce « suma mata suna son irin abun da muma muke so, duk wanda ya take hakkinta na shaawa ko na biyan bukata shima yana da irin tasa azabar da zai tarar.
Allah ya tsaremu baki daya.
➖➖➖➖➖➖➖
No comments:
Post a Comment