Sunday, 21 August 2022

HADITH CLASS 15 MACE TACE TANA SON MUTUM NAGARI

*🔶AL-MAR'AH ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)🔶*

*▪️HADITH CLASS 15*

*♦️MACE ZATA IYA GWADA KANTA KO NA YAR'TA GA MUTUM NA GARI DON YA AURA♦️*

*♦️عرض المرأة نفسها أو ابنتها على الرجل الصالح♦️*

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪

*Hadith No:1*

*🔹«قال عمر بن الخطاب رضي الله عنه، أتيت عثمان بن عفان فعرضت عليه حفصة ، فقال :سأنظر في أمري»*. 

رواه البخاري

*🔻An karbo Hadith daga Umar Bn Khaddab (RA) ya ce, na je wajen Usman Bn Affan na tallata masa  Hafsat , (ko zai aureta) sai ya ce min, Bari in yi Shawari (nazari)"*

Bukhari
★★★★★★★★★★★★★★★

*Hadith No: 2*

*🔹«قال أنس جائت امرأة الى رسول الله صلى عليه وسلم تعرض عليه نفسها ، قالت يا رسول الله ، ألك بي حاجة؟ فقالت بنت أنس : ما أقل حياءها واسوأتاه، فدقال هي خير منك، رغبت في النبي صلى الله عليه وسلم، فعرضت نفسها.»*

*🔻Anas (RA) ya ce: wata mata ta zo wajen Manzon Allah (saw) tana tallata masa kanta ko zai aureta, ta ce ya Manzon Allah (saw) shin kana da bukatar ka aureni? Sai yar Anas ta ce: Kash!! wan nan tana da karancin Kunya! Kuma ya munana ace taje wajensa (tana gwada ya aureta) Sai ya ce (Anas) ai ta fiki Alkhairi, ta fa gwada Kwadayinta ne akan Manzon Allah (saw) shi yasa ta tallata masa kanta"*

*⭕BAYANIN HADITH⭕*

*✔️Lallai yan'uwana wan nan na kara karfafa maganar Bahaushe _A rashin kira karan bebe ya bata_ kuma _a rashin tayi akan bar arha_*

*✔️Ba aibi ba ne mace in taga mutum na gari ta gwada masa tana sonsa, ko ta nemi ya auri yarta, ko mahaifi ya nema ma yar'sa ko WA ya duba ma Kanwarsa.*

*✔️Tarihi da dama ya tabbata yadda  magabata suke nema wa yaransu mazajen aure.*

*✔️Kar a bari ga mutanen kirki kuma a sake har na banza ko na dama-dama ya zo yayi kaka-gida.* 

*✔️Ko da yaushe mata na gudun gori ne ko zubar da kima, ki sani duk wanda kika ce kina sonsa, muddin in na garin ne, ba zaki taba samun ya wulakantaki ba, ko bai aureki ba, zaki kara kima ne ma a wajensa.*

*✔️Allah azurta marassa aure da abokan zama na gari. Ameeeeen*
★★★★★★★★★★★★★★★

No comments:

Post a Comment