Tuesday, 9 August 2022

MUHIMMANCIN KIRA AKAN AIKIN ALKHAIRI

*🌻AL-MAR'AH ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)🌻*

*◼️ALBISHIRINKU KUNGIYOYIN ALKHAIRI*
✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪✪

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com

Assalamu Alaikum yan'uwana musulmai, duk lokacin da Al'umma ta doshi lalacewa, Allah madaukakin Sarki yana kiran da a samu wasu daga cikinku su hada kansu wajen kira da Jaddada wa Mutane Addini ta hanyar Umurni da kyawawan abubuwa, da kuma Hani akan Munanan Ayyuka.
✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯✯

🔘Allah (SWT) ya ce:
Surah Aal-e-Imran, Verse 104:

◼️_*«وَلْتَكُن مِّنكُمْ أُمَّةٌ يَدْعُونَ إِلَى الْخَيْرِ وَيَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنكَرِ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُفْلِحُونَ»*_
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

◼️_*«And from among you there should be a party who invite to good and enjoin what is right and forbid the wrong, and these it is that shall be successful.»*_
✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩

◼️_*« A Samu wata al-Ummah daga cikinku ta tsaya wajen kira ga kyawawan ayyuka( Alkhairi) kuma suna Umurni da Kyakkyawan Aiki kuma suna hani akan munanan Ayyuka, Wadan nan su ne masu Rabauta»*_
★★★★★★★★★★★★★★★★

🔘Fiyayyen Halitta (Saw) ya ce:

◼️_*«ما من قوم يعمل فيهم بالمعاصي، ثم يقدرون على أن يغيروا ثم لا يغيروا؛ إلا يوشك أن يعمهم الله منه بعقاب»*_
رواه أبو داوود و صححه الألباني
✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰✰

◼️_*«Duk al-Ummahr da a cikinta ana aikata sabo, kuma suna da ikon su kawo canji amma basu kawo canjin ba, saura kiris Allah ya gamesu dukansu da narkon Azaba»*_
⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟⍟

*🪴N.B🪴*
✔️Bisa lura da wadan nan Nassosi yan'uwana masu irin wan nan Zaure na yada aikin alkhairi, kar muyi kasa a gwuiwa kuma kar mu bari shaidan ya lalata mana ayyukammu.

Duk al-Ummahr da ba'a samu wasu na tashi suna ankararwa tabbas zasu gamu da azabar Allah, kamar Yunwa, tsadar rayuwa, talauci, rashin tsaro, karancin ruwa, matsalar Jinya, cututtuka da sauransu.

Allah ya kara tsare mana Imaninmu baki daya. Ameeeeen
*___________________________*

No comments:

Post a Comment