*🔹AL-MAR'AH ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)🔹*
*▪️HANYAR WARWARE SHIHIRI BAYAN FARUWANSA (001)▪️*
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
★★★★★★★★★★★★★★★
Assalamu Alaikum yan'uwana musulmai tambayoyi na yawaita game da hanyar da ake warware shihiri a Musulunci,
Hanyoyi kala biyu ne
➖1) Bindokoki na Azkar
➖2a.) Karanta Ayoyi tare da magani
▪️b) Karanta wasu Addu'o'in da manzon Allah (saw) ya bayar.
▪️c) Ja wa mutum Kaho a inda sihirin ya bayyana.
▪️d) Magunguna na Sharia
In Allah ya yarda zamu fara da Bangare na 2a &b) dan na farkon tambaya bai yawaita a kansa.
Kuma a nasiha ta gaba zamu yi magana akai in Allah ya yarda.
*🔮2a)*
Shi ne ana son masu jinya da su bincika inda aka kulla sihirin ko layar ko tsafin sai warwareshi ko a lalatashi ta yadda sharia ta bayar da dama. (Wato kar a kuma a cilla futsari ko ayi wani kulunboto lokacin batawan, ko ayi wasu yanke-yanke ko zubar da jini) kawai a kwance a zubar a kuma gode ma Allah akan gane hakan.
Wan nan shi ne nau'i na farko a kashi na biyu.
*🔮2b)*
*🌻(i)* In aka gane anyi Sihiri wa mutum sai a nemi ganyen magarya guda bakwai koraye shar, a daka ko a markade da dutse yayi laushi, san nan a zuba ruwan da zai isa wanka a kai sai a karanta wadan nan ayoyi ana tofawa a cikin ruwan.
Sai a fara da
✔️Auzu billahi Minasshaitanir-Rajeeem
✔️1. Ayatul Kursy Bakara 255 (dukanta)
✔️2. Suratu Aaraf 117-122
✔️3. Suratu Yunus (79-82)
✔️4. Suratu Daha (65-70)
✔️5. Suratul Kafirun (Dukanta)
✔️6., Suratul Ikhlas,
✔️7. Suratul falaq
✔️8. Suratun Nass.
✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩✩
Bayan an karanta wadan nan a cikin ruwan , sai kuma a sha sau uku (ana kamfata da hanu) san nan sai ayi wanka da sauran ruwan
Kuma za'a iya ta maimaitawa har bukata ta biya, kuma shi wan nan ma ana amfani dashi har wa mutumin da aka shiga tsakaninsa da Iyalinsa.
Allah ya bamu nasara ya kuma karemu daga sharrin masharranta. Ameeeeen
No comments:
Post a Comment