MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN
🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 0008 🌿🌿
————————
By Haruna I Muh'd
08069582878
hdindima.blogspot.com
———————
FALALAR AZUMI
———(E)———
13. Allah na bada ladan azumi ne ba tare da lissafi ba
14. mai azumi na da farin-ciki a nan duniya(lokacin da yasha ruwa) da kuma farin-ciki a Lahira(lokacin da Allah zai bashi sakamako)
15. Dan Iskar da yake fita daga bakin mai azumi marar dadi, yafi turaren al-Miski kamshi a wajen Allah
Duk wadan nan abubuwa da muka ambata ya tabbata daga bakin manzon Allah (saw) yadda ya ce:
"قال الله تعالى: كل عمل ابن آدم له إلا الصيام،فإنه لي وأنا أجزي به، والصيام جنة وإذا كان يوم صوم أحدكم، فلا يرفث ولا يصخب، فأن سابه أحد أو قاتله، فليقل: إني امرء صائم، والذي نفس محمد بيده لخلوف فم الصائم، أطيب عند الله من ريح المسك، للصائم فرحتان يفرحهما : إذا أفطر فرح، وإذا لقي ربه فرح بصومه"
Allah madaukakin Sarki ya ce: duk aikin da dan Adam zai yi na aikin (al-khairi) nashi ne, amma banda azumi don ita tawa ce, Ni ne kuma zan ba da ladanta, Azumi garkuwa ce, In har ran da dayanku yayi azumi bai yi wargi ba kuma bai yi shashanci ba ( bai yi Musu da jayayya ba) Idan wani ya zageshi ko ya nemi suyi fada sai ya ce : Ni ina azumi. Na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake hanunsa(Allah) iska marar dadin da yake fita daga bakin mai Azumi tafi kamshin al-Miski a wajen Allah, Mai azumi yana da farin-cikin da zai yi guda biyu: lokacin da yayi bude baki zai yi farin ciki, Da lokacin da ya hadu da Ubangijinsa zai yi farin-ciki da Azumin da yayi
Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen
——N.B.——
*U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH*
——————
Via
hdindima.blogspot.com