Tuesday, 30 May 2017

RAMADAN MUBARAK (6)

*_MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN_*

🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 0006 🌿🌿
————————
*_By Haruna I Muh'd_*
*_08069582878_*
*_hdindima.blogspot.com_*

———————
*FALALAR AZUMI*
———(C)———

7.     *Idan mutum yayi azumi na kwana daya tsakaninsa da Allah, Allah yakan nisantashi da WUTA na tsawon shekaru saba'in 70years. Haka manzon Allah (saw) ya ce:*

*_"من صام يوما في سبيل الله بعد الله وجهه عن النار سبعين خريفا"_*

*_"Duk wanda yayi azumin kwana daya sabo da Allah, Allah zai nisanta fuskarsa(shi kansa) daga wuta na tsawon shekaru saba'in (70 years )"_*

8. *Wanda yayi azumin kwana daya tsakani da Allah, Allah zai nisantashi da Wuta kamar yadda ya nisanta Sama da Kasa, in ji manzon Allah (saw):*

*_"من صام يوما في سبيل الله جعل الله بينه وبين النار خندقا كما بين السماء والأرض"_*

*_"Duk wanda yayi azumi na rana daya tsakani da Allah, Allah zai sanya shamaki tsakaninsa da wuta kamar yadda ya raba Sama da Kasa"_*

9. *Azumi Wasiyyar manzon Allah ce (saw).*

*Sahabin manzon Allah Abi Umamah ya zo wajen manzon Allah (saw) ya ce Ya manzon Allah, ka umarceni mana da wata aiki wacce Allah zai amfanar dani da ita, sai manzon Allah (saw) ya ce masa:*

*_"عليك بالصوم فإنه لا مثل له"_*

*_"Ka riki yin Azumi don babu abu kamarsa"_*

*Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*

——N.B.——
U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH
——————

Via
*_hdindima.blogspot.com_*

No comments:

Post a Comment