*_MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN_*
🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 0002 🌿🌿
————————
*_By Haruna I Muh'd_*
*_hdindima.blogspot.com_*
*MA'ANAR AZUMI*
*Assalamu Alaikum Yan'uwana yau kuma sakon mu akan ma'anar Azumi ne.*
*Azumi na da yadda ake ba da ma'anarsa guda biyu kamar haka:*
1. *_Ma'anarsa A yaren Larabci:-_*
*Azumi ita ake kira "Saumu" kuma kalma ce ta Larabci mai ma'anar "Kamewa" idan har ka kame ka kiyi yin wani abu sai a kirashi "Saumu"*
2. *Ma'anarsa A addinin musulunci(A Shari'ah):-*
*Azumi a Shari'ah na da ma'anoni da dama daga bakin malamai, amma ga daya daga ciki, kuma wanda yafi karbuwa:*
*_Ibadar Allah ce da mutum na musamman zai yita wa Ubangijinsa tare da niyyar kamewa daga barin cin wani abu, ko shan wani abu, ko guje ma duk wani abun da zai karya masa azumi, tun daga fitowar al-Fijir na biyu, har zuwa faduwar Rana wajen bin sharuda na musamman_*
*_"الصوم هو التعبد لله تعالى بالإمساك بنية: عن الأكل والشرب، وسائر المفطرات، من طلوع الفجر الثاني إلى غروب الشمس، من شخص مخصوص بشروط مخصوصة"_*
*Alhamdu-lillah yau Yan'uwana batum mu ya takaita ne akan ma'anar Axumi. Allah ya kaimu da rai da lafiya. Ameeeeeeeeeeeen*
—————
Share it pls, Fisabilil-Lah
—————
Via:
*_hdindima.blogspot.com_*
No comments:
Post a Comment