*_MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN_*
🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 0005 🌿🌿
————————
*_By Haruna I Muh'd_*
*_08069582878_*
*_hdindima.blogspot.com_*
———————
*FALALAR AZUMI*
———(B)———
4. *Azumi garkuwa ce wa mutum, zata kare mai yinta ga barin shiga WUTA, hakam ya tabbata a Hadith na manzon Allah (Saw) ya ce :*
*_"قال ربنا: الصيام جنة، يستجن بها العبد من النار،وهو لي وأنا أجزي به"_*
*_"Ubangijinmu ya ce: Azumi garkuwa ce wacce mutum yakan samu tsaro da ita ga barin shiga wuta, kuma shi (azumi) nawa ne, NI zan sakanka (ga masu azumin)_*
5. *Kuma har yanzu, Azumi Tsaro ce ga barin shiga wuta, kamar yadda manzon Allah (saw) ya ce:*
*_"الصيام جنة وحصن، حصين من النار"_*
*_" Azumi Garkuwa ce da kuma tsaro, tsaro ga barin shiga wuta"_*
6. *Azumi kariya ce ga Sha'awa, manzon Allah Ya ce:*
*_"......و من لم يستطع فعليه بالصوم، فإنه له وجاء"_*
*_"(.... Wanda bai da ikon (yin aure) ya din ga yin azumi, sabo da (Azumi) zai zame masa garkuwa (ga barin Sha'awa)."_*
*Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*
——N.B.——
U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH
——————
Via
*_hdindima.blogspot.com_*
No comments:
Post a Comment