Tuesday, 30 May 2017

RAMADAN MUBARAK (7)

*_MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN_*

🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 0007 🌿🌿
————————
*_By Haruna I Muh'd_*
*_08069582878_*
*_hdindima.blogspot.com_*

———————
*FALALAR AZUMI*
———(D)———

10. *Allah ya tanada wa masu azumi gida ta musamman a Al-Jannah, yana da kofa mai suna _RAYYAN_ hakan ya fito ne daga bakin manzon Allah (saw) ya ce:*

*_"إن في الجنة بابا يقال له :الريان، يدخل منه الصائمون يوم القيامة، لا يدخل منه غيرهم، فإذا دخل آخرهم أغلق فلم يدخل منه أحد"_*

*_"Lallai a Al-Jannah akwai wani kofa ana kiransa RAYYAN takofar yan' Al-Jannah masu azumi zasu shiga a ranar al-Qiyamah, ba mai shiga (ta kofar nan) in basu ba, idan na karshensu ya shiga sai a rufe ba wanda kuwa zai sake shiga(ta wannan Kofa na masu azumi) "_*

11. *_Azumi na daga abubuwa na farko da suke kai mutum Al-Jannah,*

      *Manzon Allah (saw)  wata rana ya tara Sahabbai yana Tambayarsu kamar haka:_*

*_" من أصبح اليوم منكم صائما؟"_*
*_"Waye daga cikinku yau ya wayi gari yana Azumi?"_*

*Sayyidina Abu-Bakr ya ce: "Ni ya manzon Allah (saw)"*

*_"فمن اتبع منكم اليومة جنازة"_*

*_"Waye daga cikinku kuma yau ya raka gawa har Makabarta? "_*

*Sayyidina Abu-Bakr ya ce: "Ni ya manzon Allah (saw)"*

*_" فمن أطعم منكم اليوم مسكينا؟"_*

*_"Waye daga cikinku yau ya ciyar da miskini(Talaka)?"_*

*Sayyidina Abu-Bakr ya ce: "Ni ya manzon Allah (saw)"*

*_"فمن عاد منكم اليوم مريضا؟"_*

*_"Waye daga cikinku ya gaishe da maras Lafiya a yau?"_*

*Sayyidina Abu-Bakr ya ce: "Ni ya manzon Allah (saw)"*

*A karshe sai manxon Allah ya ce:*

*_"ما جتمعن في امرئ إلا دخل الجنة"_*

*_"Ba wanda zai hada wadan nan siffofi face sai ya shiga Al-Jannah "_*

12. *Azumi na kankare zunubai baki daya na bawa,*

    *Manzon Allah (saw) ya ce :*

*_"فتنة الرجل في أهله، و ماله، و ولده، و جاره، تكفرها : الصلاة و الصوم والصدقة، والأمر، و النهي"_*

*_" Idan Allah ya jarrabi mutun akan Iyalansa, ko akan dukiyarsa, ko akan Yaransa, ko akan makobtansa, Abun da zai kankare masa zunubansa shi ne: Sallah, Azumi, Sadaka, yin umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani kan munanan aiki"_*

*Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*

——N.B.——
*U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH*
——————

Via
*_hdindima.blogspot.com_*

No comments:

Post a Comment