Monday, 20 May 2019

DARUSAN RAMADAN (009)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (014)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
ADDU'AR DA AKE YI BAYAN WUTIRI
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

✍ Haruna I Muh'd
Hdindima@yahoo.com
  080 69582878
————————
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai akwai addu'ar da ya tabbata Manzon Allah yana yi bayan Sallar Wutiri, wanda da dama an shagala akai.

Ga addu'ar kamar haka: ana son mutum ya karanta sau uku, amma na ukun sai ya dan daga muryarsa kadan sama da na baya.

"SUBHANAL MALIKIL KUDDUS"
(Sahihu Abi Dawud 1284)

سبحان الملك القدوس

Kuma ya halalla mutum ya kara da

"Rabbil Mala'ikatu War-Ruuh" wato mutum ya ce
"Subhanal Malikil Kuddus, Rabbil Mala'ikaku war-Ruuh"

سبحان الملك القدوس، رب الملائكة والروح

Allah ya bamu ikon kiyaye wan nan Sunnah ta Manzon Allah (saw).
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
www.hdindima.blogspot.com
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

DARUSAN RAMADAN (008)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (015)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
RAMADAN WATAN TUBA CE
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍ Haruna I Muh'd
    08069582878
Hdindima@gmail.com
🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

Assalamu Alaikum yan'uwana maza da mata, lallai Ramadan ko bayan Ramadan ana son kowa ya tuba zuwa ga Allah akan duk zunubansa, ana son mu kara neman tuba musamman a wan nan wata mai al-Barka

Lallai tuba tana da sharuda har guda shiga (6) kuma in mutum bai cikasu ba, tubarsa ba ta zama mai amfani ba.

Sharudan tubah(6):
———————
1. *Tuba domin Allah, kar mutum ya tuba dan wata abun da ta shafi duniya, (wato a saka tsoron Allah a ciki).

2. Tuba a cikin Lokacinta da Allah yake karba, in mutum yazo mutuwa ko yaga mutuwa da idonsa ko ya tuba anan ya makara, mutum ya tuba tun kafin wan nan lokaci ya sameshi.

3. Mutum yayi Baran-Baran da zunubin da ya aikata a baya, mutum ba zai tuba kuma amma yana cikin ko yana kan aikata zunubin ba.

4. Mutum yayi nadama akan abun da ya aikata, sabo da Manzon Allah (saw) ma ya ce :"Nadama ma tubah ce".

5. Mutum ya kulla Aniyar cewa ba zai sake dawowa kan wan nan laifi ba har abada.

6. Idan kuwa abun da ya tuba akai tana da alaqa da hakkin wani ne, dole ne ka mayar masa da kayansa, na kudi ne ko na mutunci ko wani abu daban.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Alhamdulil-Lah Allah ya bamu ikon tuba zuwa ga zunubammu baki daya, ya kuma karba mana ibadunmmu. Ameeeeeen

🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Share this pls
www.hdindima.blogspot.com
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Saturday, 18 May 2019

DARUSAN RAMADAN (007)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (013)
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

BA LAIFI BA NE DAN KA AIKATA A RAMADAN
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

✍ Haruna I Muh'd
     08069582878
Hdindima@gmail.com
—————————

Assalamu Alaikum yan'uwana akwai wasu abubuwa da mutane na ganin kamar laifi ne a Ramadan amma ba komai:

➡ Ba laifi ba ne dan al-Fijr ya tarar da mutum yana da Janaba a jikinsa.

Nana Aishat (RA) ta ce, Manzon Allah (Saw) ya kasance al-Fijr na samunsa yana da Janaba a Ramadan, ba kuma (Janaba) na mafarki ba, sai yayi wanka ya ci gaba da Azuminsa ".
(Ibn abi Shaibah 9171)

Kuma haka ma akwai Hadith na Ummu Salma wanda Ibn Abdul-Barr ya fitar shima mai kama da wanda ya gabata.

A karkashin wan nan haka duk macen da ke al'adah ko jinin Haihuwa, in har ya tsaya musu kafin al-Fijr zasu iya daukan Azumi koda ba su yi wanka ba har gari ya waye.

➡ Zuba ruwa a kai dan zafin Rana ko Wahalar Azumi.

Lallai ba laifi ba ne dan mutum ya na yawan zuba ruwa a kansa ko yana wanka akai-akai dan zafi ko wahala.

Hadith na Abubakar Ibn Abdur-Rahman ya ce" daga sashin Sahabban Manzon Allah (saw) ya ce naga Manzon Allah (saw) a Lokacin zafi yana zuba ruwa a kansa kuma yana Azumi, sabo da Ishi ko Zafi (Zafin Rana)".
(Abu Dawud: 2365)
👆👆👆👆👆👆👆

Da wan nan yar nasiha nake rokon Allah ya karba mana ibadummu baki daya.

🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Ka tura wan nan sako ma yan'uwa baki daya dan muyi tarayya a lada baki daya
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
www.hdindima.blogspot.com
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

DARUSAN RAMADAN (006)

DARUSAN RAMADAN 1440/2019 (012)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

HADITHAN DA BASU INGANTA BA GAME DA AZUMI
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

✍ Haruna I Muh'd
    080 69582878
hdindima@gmail.com
————————

Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai, lallai akwai Hadithai da dama da basu inganta ba inji malaman Hadith, wadan da suke da alaqa kuma da Azumi, ga sunan kamar haka:

➡ Hadith _"Barcin mai Azumi Ibada ne" Hadisi ne mai Rauni, bai inganta ba.

➡ Hadith _"duk wanda ya sha (ya karya) Azuminsa da Gangan ko da yayi Azumin Shekara bai wadatar ba"  Wan nan Hadith ma Bai inganta ba.

➡ Hadith _"Ku yi Azumi zaku ji Wasai (zaku samu lafiya garau)"_ Wan nan ma Hadith ne mai rauni sosai. Bai inganta ba.

➡ Hadith da wai ake cewa Annabi (saw) yana ce wa Sahabbai in Ramadan ta zo _" Ramadan ya zo muku....(har in da wai yake cewa) Ramadan ya zo muku wata mai Girma mai Al-Barka, Allah ya sanya Azumi a cikinsa Farillah, Sallan dare a cikinsa kuma Sunnah, kuma duk wan da yazo da wata dabia mai kyau kamar wanda yayi Farilla ne a wasu watanni, haka wan da yayi farilla a ciki kamar wan da yayi Farillai Saba'in ne a wasu watanni, kuma wata ne wanda Farkonsa Rahma, tsakiyarsa Gafara, Karshensa kuma yantawa daga wuta,".
wan nan Hadith din ma Ba ingantacce ba ne. Da'ifi ne, wasu ma sun ce Munkar ne.

Allah ya bamu ikon aiki da Hadiths na manzon Allah Ingantattau, ya kuma sa muyi muwa faka, kuma kowa ya kara shiga taitayinsa kar daga ganin an ce maka Hadith kawai ka fara yada wa mutane. Allah yasa mu dace.
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

www.hdindima.blogspot.com
———————

Saturday, 11 May 2019

DARUSAN RAMADAN (001)

*֮֮֮R֮֮֮A֮֮֮M֮֮֮A֮֮֮D֮֮֮A֮֮֮N֮֮֮ K֮֮֮A֮֮֮R֮֮֮E֮֮֮E֮֮֮M֮֮֮ 2֮֮֮0֮֮֮1֮֮֮9֮֮֮*֮֮֮
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*֮֮֮M֮֮֮u֮֮֮h֮֮֮i֮֮֮m֮֮֮m֮֮֮a֮֮֮n֮֮֮c֮֮֮i֮֮֮n֮֮֮ A֮֮֮z֮֮֮u֮֮֮m֮֮֮i֮֮֮*֮֮֮
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

֮✍֮ *֮H֮a֮r֮u֮n֮a֮ I֮ M֮u֮h֮'֮d֮*֮
֮*֮0֮8֮0֮ 6֮9֮5֮8֮2֮8֮7֮8֮*֮
Hdindima@gmail.com
☂☂☂☂☂☂

Bismillahir-Rahmanir-Raheeem

🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Yan'uwana musulmai lallai watan Ramadana yana da falala sosai tare da muhimmanci a rayuwarmu tanan Duniya da kuma Lahira.

Ga kadan daga cikin Falala da muhimmancin Azumin:

1. Allah (swt) ya farlanta wan nan Azumi a kammu da kuma al-Ummah da ta rigayemu.
(Qur'an:2:183)

2. Sanadiyar Azumi Allah yana gafarta wa mutane duk zunubansu, kamar yadda Manzon Allah ya ce " Wanda yayi Azumin watan Ramadan yana mai Imani da kuma sa ran samun Lada, za a gafarta masa duk abun da ya aikata a baya"

3. A Azumi ne Allah ya gwada mana cewa ladansa ba adadi,  kawai Ladan kamfata za a yi a bashi.

Manzon Allah ya ce: " Allah ya ce duk ayyukan bayi sakamakonsa nasu ne, amma banda Azumi ita kam tawa ce, kuma Ni zan ba da ladansa,....."

A karkashin wan nan Hadith Allah ya ambato abubuwa masu muhimmanci kan wan nan Wata mai al-Barka:

a) Allah ya ware Azumi ya zama nashi ne dan yana cewa "bawana yabar ci da sha da kuma sha'awarsa duk danni" ni zan bashi ladan hakan.

b) Allah fa da kansa ya ce zai saka ma wadan ya yayi Azumi, dan ya gwada karrama mai Azumi.

c) Allah ya ce Azumi garkuwa ce, zata hana mutum aikata munanan ayyuka, kuma manzon Allah ya ce
:" Azumi garkuwa ce wada ake samu tsanin mutum da shiga wuta".

d) Kuma a Hadith din Allah ya ce warin da yake fita daga bakin mai Azumi darajarsa yafi kamshin Turaren Al-Misk, hakan na gwada yadda Allah yaba Azumi daraja.

e) Allah ya ce mai  Azumi zai yi farin-ciki a wurare biyu,

i. Lokacin da yayi bude baki da kuma
ii. Lokacin da zai hadu da Ubangiji, dan zai samu lada mai yawa.

4. Azumi zai ceci mai yinsa a ranar al-Qiyamah, Manzon Allah (saw) ya ce :" Azumi da al-Qur'an zasu ceci bawa ranar al-Qiyamah, Azumi zata ce ya Allah na hanashi cin komai da kuma sha'awarsa, ka bani cetonsa mana! Sai Al-Qur'an ma ya ce ya Allah na hanashi Barci da dare, ya Allah ka bani cetonsa mana! (Sai manzon Allah) ya ce  sai kuma a basu ceton".

Anan zamu takaita Allah ya bamu ikon fara Azumi lafiya ya sa mu gama lafiya ya kuma bamu duk ladan da ake samun a wan nan wata mai al-Barka.

Dan samun wan nan lada tun daga yanzu ka/ki tura wan nan sako  grp naku dan muyi tarayya a ladan baki daya.
🌼🌼🌼🌼🌼🌼

DARUSAN RAMADAN (002)

RAMADAN KAREEEM 2019
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

MUHIMMANCIN KO FALALAR WATAN RAMADAN (02)
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

✍ Haruna I Muh'd
    080 69582878
Hdindima@gmail.com
🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Assalamu Alaikum yan'uwana maza da mata hakika Manzon Allah (saw) ya fada mana Falalar wan nan wata mai al-Barka.
–––––––

Yau zamu yi nazari ne akan Hadith guda daya mai tarin Darusa.
👇👇👇👇👇👇

Imam Ahmad ya fidda Hadith daga Abu Hurairah (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) Ya ce:

" An ba wa Al-Ummahta wasu al'amura guda biyar wadan da baa ba wata al-Ummah da tazo a baya ba, a cikin watan Ramadan:

👉 1. Warin da yake fita a bakin mai Azumi (darajarsa) yafi kamshin Turaren almisk a wajen Allah

👉 2. Mala'iku suna nema musu gafar Zunubansu har sai lokacin da suka yi buda-baki

👉 3. A ko wace rana kuma Allah yana kawata Al-Jannah yana kuma cewa :" saura kadan bayina su zo su sameni, (sun kusa su bar hidindimun duniya da cutarwar da suke tararwa wajen bin Allah)

👉 4. Kuma za'a daure Shaidanu daga ko wace zirga-zirga, ba su isa su cimma wadan da suke so su cimma ba a cikin bayin Allah na gari

👉 5. Kuma Allah zai gafarta musu a ko wace karshen dare, sai Sahabbai suka ce ya Manzon Allah ko ita ce Lailatul-Qadr? Sai ya ce ah-ah, ko wani mai aiki za a bashi ladan aikinsa ne da zarar ya gama aikinsa"

Imam Bazzar da Baihaqi ne suka rawaito a Kitab Thawab, Isnad nashi yana da rauni sosai, amma sashinsa akwai Shawahid Ingantattu.
––––––––

Allah ya bamu ikon cin moriyar da ke cikin an nan wata mai al-Barka.

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Visit our site:
www.hdindima.blogspot.com
🌲🌲🌲🌲🌲🌲🌲

DARUSAN RAMADAN (003(

*֮֮֮D֮֮֮A֮֮֮R֮֮֮U֮֮֮S֮֮֮A֮֮֮N֮֮֮ R֮֮֮A֮֮֮M֮֮֮A֮֮֮D֮֮֮A֮֮֮N֮֮֮ (֮֮֮3֮֮֮)֮֮֮ 1֮֮֮4֮֮֮4֮֮֮0֮֮֮/֮֮֮2֮֮֮0֮֮֮1֮֮֮9֮֮֮*֮֮֮
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
KADAN CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
By Haruna I Muhd
080 69582878
Hdindima@gmail.com
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Azumi yana da Hukunce-Hukunce masu yawa, ga kadan daga ciki:
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
1. Shuhur: lallai Sunnah ce mai karfi da ake bukatar kowa yayi kafin daukan Azumi, kuma ana son mu dinga jinkirtawa kamar saura kadan a kira sallah sai mutum yayi Saur nashi da hanzari ya gama komai, Manzon Allah (saw) ya ce:" kuyi Sahur, damin cikin Sahur akwai Al-Barka". "Abun da ya banbanta tsakanin Azuminmu da Azumin Ahlul kitab shi ne yin Sahur".

2. Bude-baki: shi kuma ana son mutum ya gaggauta buda-baki da zarar rana ta fadi, Manzon Allah (Saw) ya ce:" Mutane ba zasu gushe ba suna cikin Al-Khairi matukar suna gaggauta shan ruwa". Kuma ya sake cewa:" Al-Ummahta ba zasu gushe ba suna cikin al-Khairi matukar suna gaggauta shan ruwa suna kuma jinkirta Sahur"

3. KARYA AZUMI:
i) idan mutum ya ci ko yasa da gangan a ramadan, zai tuba ya kuma yi Istigfar kuma ya biya wan nan Azumin da ya sha. Amma ba kaffara a kansa,
ii). Wanda kuma ya karya Azuminsa ta hanyar Jima'i wan nan kam zaiyi:
(a) Tubah zuwa ga Allah
(b) ya kuma kame bakinsa har akai wan nan Azumi
(c) ya kuma biya Azumin.
(d). Ya kuma yi kaffara: ita ce ya yanta baiwah, in bai da hali ya yi  wata biyu a jere yana Azumi, in bai da hali ya ciyar da Miskinai guda Sittin (60), in har ya tabbata bai da ikon ko daya, kaffarar ta fadi akansa.

4. Yin amai da gangan: Wanda yayi amai da gangan, azuminsa ta baci zai biya daga baya. Manzon Allah (S.A.W) ya ce:" wanda ya kirkiro amai da gangan to ya biya (Azumin) wanda kuma Amai din ne ta rinjayeshi babu biya akansa."

5. Mai Al'adah ko  jinin Haihuwa: duk wacce take al'adah ko jinin haihuwa ba zata yi Azumi ba kuma bayan Azumi sai ta biya kawai

N.B
Anan muke kara jan hankalin Jama'ah kan duk abun da yayi kama da wadan nan shima irinsu ne, wanda aka saka masa Allurar da yake kai abinci to shima abinci ne ba Azumi, wanda shima yayi ta wasa da Al'auransa ko kallon film na batsa kuma har ya fitar da maniyyi to shima kamar wanda yayi Jima'i ne.

Allah ka kara bamu fahimtar Addini, Ameeeeeen, kai ma ka tura iya groupda zaka iya dan samun lada a Ramadan
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

DARUSAN RAMADAN (004)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019 (004)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKA YI SASSAUCI WA MAI AZUMI
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

✍ Haruna I Muh'd
      080 69582878
Hdindima@gmail.com
———————

Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai, musulunci ya mana rangwami akan abubuwa kamar haka:

1. Duk wanda ya ci abu ko ya sha bisa mantuwa, Azuminsa na nan, kuma ba biya a kansa.
Manzon Allah (saw) ya ce :" duk wanda ya manta yana Azumi ya  ci ko ya sha, to ya cika Azuminsa, Allah ne ya ciyar dashi kuma ya shayar dashi".(Bukhari&Muslim)

2. Duk wanda ya wayi gari yana da janaba a jikinsa na Jima'i ko na mafarkin da yayi da dare, zai yi Azuminsa ba komai a kansa, sai yayi wanka daga baya kawai.

3. Yin amfani da Ashwaki ko Brush a lokacin Azumi, ba matsala, sai dai an fi so da ayi a wasu gurabe na musamman, (wato lokutan da ake bukata)
Ya halatta ayishi a ko wani lokaci sai dai akwai lokutan da Nassi ya yi magana akai guda shida (6) kamar haka:
a) Lokacin Alola.
b) Lokacin Sallah.
c) Lokacin shiga gida.
d) Lokacin da ka tashi daga Barci.
e) Lokacin da za'a karanta al-Qur'an.
*f) Lokacin da kaso canza warin baki

4. Kurkuran baki da sheka ruwa a Hanci. lallai ba damuwa dan mutum ya sheka ruwa a hanci ko yawan kurkuran baki, sai dai an mana sassauci kan mu yi kurkuran baki a hankali dan kar ruwa ya wuce, Manzon Allah ya ce ma wani sahabinsa mai suna Laqidu bn Swabrah :"Ka kai matuka wajen kurkuran baki da sheka ruwa ahanci(wajen alola) sai dai in kana Azumi"

5. Mutum zai iya shan ruwa da rana in yana cikin tafiya, anfi so ma ya sha din matukar zai wahala a Azumi, tafiyar kuwa ko a jirgi ne ko mota ko wani abu

Alhamdulil-Lah

Muna fatan Allah ya amfanar damu da wan nan yar takaitacciyar nasiha, Dan'uwana kar kayi rowan ilmi ka aika ma wasu wan nan sako dan muyi tarayya a ladan, fatan al-Khairi
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

DARUSAN RAMADAN (005)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (005)
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*DAGA CIKIN KURA-KURENMMU DA MUKE YI A RAMADAN*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹

✍ Hanuna I Muh'd
      080 6958 2817
Hdindima@gmail.com
————————

Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai akwai Kura-kurai da muke tafkawa a ramadana wadan da ya kamata mu gyara, kamar haka:

1. Muna yawaita Ibadah zallah a Ramadan amma bayanta sai mu koma ruwa, a ramadan din ma zaka ga ana cika masallatai musamman Lokacin Sallar Magrib, haka kuma a farkon Ramadan kowa na kokari amma ana gaba gaba aikimmu na raguwa. Ya kamata ni da ku mu gyara.

2. Lallai da yawa muna Azumi wajen barin ci da sha da Jima'i da duk abun da suke karya Azumi, amma bamu iya kame kammu ga aikata abubuwan da suke haramun kamar:
-Gulma
-Rada
-Zage-zage
-Shaidar Zur
-al-Gus
-Karya da
-Gaba da Juna.
Lallai wadan nan su kadai zasu iya samu mu rasa ladan Azumi baki daya, Allah ya karemu.

3. *Kuma masu Nasiha wani lokaci suna gwada wa mutane ribar Azumi na nan take, wato kamar in kayi Azumi lafiyarka zai karu, ko arzikinka......, lallai abun da yafi shi ne a fara gwada musu cewa Ibadah ce, kuma ladan a alaqanta musu da Lahira kafin a zo kan amfanin Duniya daga Baya.

4. Kuma da yawo mukan koma Masu munanan Halaye, sai kaga mutum wai dan sabo da yana Azumi (akwai Yunwa) ya zama mai Turbune fuska wa Iyalansa, Kaushin hali wa Jama'ah, ba dariya ko Faraa a Fuskarsa.....

5. *Da yawa mukan dauki watan Ramadan kamar watan Kasala da sakalci, sai kaga mutum sai barci yake shara kamar yaga malakul Mautu,  sai a dinga fakewa da Hadith mai Rauni, wai Annabi ya ce "Barcin mai Azumi Ibadah ne" wan nan Hadith Mai Rauni ne,. Allah yasa mu gyara, mu tuna cewa yakin da aka yi a zamanin Annabi wasu a Ramadan ne ma, mu fita mu nemi arziki mu yi ibadah ban da yawan barcin da bai da amfani

6. Yawan tara abinci da abun Sha wanda baa saba dasu ba, kaga mutum an sha ruwa ya tara abun ci da abun sha wanda sunfi karfinsu, kuma hakan yakan sa bayan ka koshi sai kasala da barci, kai ba ka yi komai ba har gari ya waye. Abun da aka fi so shi ne ayi abun da za a ci madaidaici ko abun da za a sha.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻

Allah ya bamu ikon kiyayewa baki daya, ka tura akalla ma grp uku naka dan muyi tarayya ikin Lada.
www.hdindima.blogspot.com