Saturday, 18 May 2019

DARUSAN RAMADAN (007)

DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (013)
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

BA LAIFI BA NE DAN KA AIKATA A RAMADAN
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

✍ Haruna I Muh'd
     08069582878
Hdindima@gmail.com
—————————

Assalamu Alaikum yan'uwana akwai wasu abubuwa da mutane na ganin kamar laifi ne a Ramadan amma ba komai:

➡ Ba laifi ba ne dan al-Fijr ya tarar da mutum yana da Janaba a jikinsa.

Nana Aishat (RA) ta ce, Manzon Allah (Saw) ya kasance al-Fijr na samunsa yana da Janaba a Ramadan, ba kuma (Janaba) na mafarki ba, sai yayi wanka ya ci gaba da Azuminsa ".
(Ibn abi Shaibah 9171)

Kuma haka ma akwai Hadith na Ummu Salma wanda Ibn Abdul-Barr ya fitar shima mai kama da wanda ya gabata.

A karkashin wan nan haka duk macen da ke al'adah ko jinin Haihuwa, in har ya tsaya musu kafin al-Fijr zasu iya daukan Azumi koda ba su yi wanka ba har gari ya waye.

➡ Zuba ruwa a kai dan zafin Rana ko Wahalar Azumi.

Lallai ba laifi ba ne dan mutum ya na yawan zuba ruwa a kansa ko yana wanka akai-akai dan zafi ko wahala.

Hadith na Abubakar Ibn Abdur-Rahman ya ce" daga sashin Sahabban Manzon Allah (saw) ya ce naga Manzon Allah (saw) a Lokacin zafi yana zuba ruwa a kansa kuma yana Azumi, sabo da Ishi ko Zafi (Zafin Rana)".
(Abu Dawud: 2365)
👆👆👆👆👆👆👆

Da wan nan yar nasiha nake rokon Allah ya karba mana ibadummu baki daya.

🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Ka tura wan nan sako ma yan'uwa baki daya dan muyi tarayya a lada baki daya
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
www.hdindima.blogspot.com
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

No comments:

Post a Comment