Saturday, 11 May 2019

DARUSAN RAMADAN (003(

*֮֮֮D֮֮֮A֮֮֮R֮֮֮U֮֮֮S֮֮֮A֮֮֮N֮֮֮ R֮֮֮A֮֮֮M֮֮֮A֮֮֮D֮֮֮A֮֮֮N֮֮֮ (֮֮֮3֮֮֮)֮֮֮ 1֮֮֮4֮֮֮4֮֮֮0֮֮֮/֮֮֮2֮֮֮0֮֮֮1֮֮֮9֮֮֮*֮֮֮
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
KADAN CIKIN HUKUNCE-HUKUNCEN AZUMI
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
By Haruna I Muhd
080 69582878
Hdindima@gmail.com
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
Azumi yana da Hukunce-Hukunce masu yawa, ga kadan daga ciki:
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
1. Shuhur: lallai Sunnah ce mai karfi da ake bukatar kowa yayi kafin daukan Azumi, kuma ana son mu dinga jinkirtawa kamar saura kadan a kira sallah sai mutum yayi Saur nashi da hanzari ya gama komai, Manzon Allah (saw) ya ce:" kuyi Sahur, damin cikin Sahur akwai Al-Barka". "Abun da ya banbanta tsakanin Azuminmu da Azumin Ahlul kitab shi ne yin Sahur".

2. Bude-baki: shi kuma ana son mutum ya gaggauta buda-baki da zarar rana ta fadi, Manzon Allah (Saw) ya ce:" Mutane ba zasu gushe ba suna cikin Al-Khairi matukar suna gaggauta shan ruwa". Kuma ya sake cewa:" Al-Ummahta ba zasu gushe ba suna cikin al-Khairi matukar suna gaggauta shan ruwa suna kuma jinkirta Sahur"

3. KARYA AZUMI:
i) idan mutum ya ci ko yasa da gangan a ramadan, zai tuba ya kuma yi Istigfar kuma ya biya wan nan Azumin da ya sha. Amma ba kaffara a kansa,
ii). Wanda kuma ya karya Azuminsa ta hanyar Jima'i wan nan kam zaiyi:
(a) Tubah zuwa ga Allah
(b) ya kuma kame bakinsa har akai wan nan Azumi
(c) ya kuma biya Azumin.
(d). Ya kuma yi kaffara: ita ce ya yanta baiwah, in bai da hali ya yi  wata biyu a jere yana Azumi, in bai da hali ya ciyar da Miskinai guda Sittin (60), in har ya tabbata bai da ikon ko daya, kaffarar ta fadi akansa.

4. Yin amai da gangan: Wanda yayi amai da gangan, azuminsa ta baci zai biya daga baya. Manzon Allah (S.A.W) ya ce:" wanda ya kirkiro amai da gangan to ya biya (Azumin) wanda kuma Amai din ne ta rinjayeshi babu biya akansa."

5. Mai Al'adah ko  jinin Haihuwa: duk wacce take al'adah ko jinin haihuwa ba zata yi Azumi ba kuma bayan Azumi sai ta biya kawai

N.B
Anan muke kara jan hankalin Jama'ah kan duk abun da yayi kama da wadan nan shima irinsu ne, wanda aka saka masa Allurar da yake kai abinci to shima abinci ne ba Azumi, wanda shima yayi ta wasa da Al'auransa ko kallon film na batsa kuma har ya fitar da maniyyi to shima kamar wanda yayi Jima'i ne.

Allah ka kara bamu fahimtar Addini, Ameeeeeen, kai ma ka tura iya groupda zaka iya dan samun lada a Ramadan
🌳🌳🌳🌳🌳🌳

No comments:

Post a Comment