DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019AC (005)
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*DAGA CIKIN KURA-KURENMMU DA MUKE YI A RAMADAN*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
✍ Hanuna I Muh'd
080 6958 2817
Hdindima@gmail.com
————————
Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai akwai Kura-kurai da muke tafkawa a ramadana wadan da ya kamata mu gyara, kamar haka:
1. Muna yawaita Ibadah zallah a Ramadan amma bayanta sai mu koma ruwa, a ramadan din ma zaka ga ana cika masallatai musamman Lokacin Sallar Magrib, haka kuma a farkon Ramadan kowa na kokari amma ana gaba gaba aikimmu na raguwa. Ya kamata ni da ku mu gyara.
2. Lallai da yawa muna Azumi wajen barin ci da sha da Jima'i da duk abun da suke karya Azumi, amma bamu iya kame kammu ga aikata abubuwan da suke haramun kamar:
-Gulma
-Rada
-Zage-zage
-Shaidar Zur
-al-Gus
-Karya da
-Gaba da Juna.
Lallai wadan nan su kadai zasu iya samu mu rasa ladan Azumi baki daya, Allah ya karemu.
3. *Kuma masu Nasiha wani lokaci suna gwada wa mutane ribar Azumi na nan take, wato kamar in kayi Azumi lafiyarka zai karu, ko arzikinka......, lallai abun da yafi shi ne a fara gwada musu cewa Ibadah ce, kuma ladan a alaqanta musu da Lahira kafin a zo kan amfanin Duniya daga Baya.
4. Kuma da yawo mukan koma Masu munanan Halaye, sai kaga mutum wai dan sabo da yana Azumi (akwai Yunwa) ya zama mai Turbune fuska wa Iyalansa, Kaushin hali wa Jama'ah, ba dariya ko Faraa a Fuskarsa.....
5. *Da yawa mukan dauki watan Ramadan kamar watan Kasala da sakalci, sai kaga mutum sai barci yake shara kamar yaga malakul Mautu, sai a dinga fakewa da Hadith mai Rauni, wai Annabi ya ce "Barcin mai Azumi Ibadah ne" wan nan Hadith Mai Rauni ne,. Allah yasa mu gyara, mu tuna cewa yakin da aka yi a zamanin Annabi wasu a Ramadan ne ma, mu fita mu nemi arziki mu yi ibadah ban da yawan barcin da bai da amfani
6. Yawan tara abinci da abun Sha wanda baa saba dasu ba, kaga mutum an sha ruwa ya tara abun ci da abun sha wanda sunfi karfinsu, kuma hakan yakan sa bayan ka koshi sai kasala da barci, kai ba ka yi komai ba har gari ya waye. Abun da aka fi so shi ne ayi abun da za a ci madaidaici ko abun da za a sha.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Allah ya bamu ikon kiyayewa baki daya, ka tura akalla ma grp uku naka dan muyi tarayya ikin Lada.
www.hdindima.blogspot.com
No comments:
Post a Comment