DARUSAN RAMADAN 1440AH/2019 (004)
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
DAGA CIKIN ABUBUWAN DA AKA YI SASSAUCI WA MAI AZUMI
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
✍ Haruna I Muh'd
080 69582878
Hdindima@gmail.com
———————
Assalamu Alaikum yan'uwana Musulmai, musulunci ya mana rangwami akan abubuwa kamar haka:
1. Duk wanda ya ci abu ko ya sha bisa mantuwa, Azuminsa na nan, kuma ba biya a kansa.
Manzon Allah (saw) ya ce :" duk wanda ya manta yana Azumi ya ci ko ya sha, to ya cika Azuminsa, Allah ne ya ciyar dashi kuma ya shayar dashi".(Bukhari&Muslim)
2. Duk wanda ya wayi gari yana da janaba a jikinsa na Jima'i ko na mafarkin da yayi da dare, zai yi Azuminsa ba komai a kansa, sai yayi wanka daga baya kawai.
3. Yin amfani da Ashwaki ko Brush a lokacin Azumi, ba matsala, sai dai an fi so da ayi a wasu gurabe na musamman, (wato lokutan da ake bukata)
Ya halatta ayishi a ko wani lokaci sai dai akwai lokutan da Nassi ya yi magana akai guda shida (6) kamar haka:
a) Lokacin Alola.
b) Lokacin Sallah.
c) Lokacin shiga gida.
d) Lokacin da ka tashi daga Barci.
e) Lokacin da za'a karanta al-Qur'an.
*f) Lokacin da kaso canza warin baki
4. Kurkuran baki da sheka ruwa a Hanci. lallai ba damuwa dan mutum ya sheka ruwa a hanci ko yawan kurkuran baki, sai dai an mana sassauci kan mu yi kurkuran baki a hankali dan kar ruwa ya wuce, Manzon Allah ya ce ma wani sahabinsa mai suna Laqidu bn Swabrah :"Ka kai matuka wajen kurkuran baki da sheka ruwa ahanci(wajen alola) sai dai in kana Azumi"
5. Mutum zai iya shan ruwa da rana in yana cikin tafiya, anfi so ma ya sha din matukar zai wahala a Azumi, tafiyar kuwa ko a jirgi ne ko mota ko wani abu
Alhamdulil-Lah
Muna fatan Allah ya amfanar damu da wan nan yar takaitacciyar nasiha, Dan'uwana kar kayi rowan ilmi ka aika ma wasu wan nan sako dan muyi tarayya a ladan, fatan al-Khairi
🌻🌻🌻🌻🌻🌻
No comments:
Post a Comment