*MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN*
🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 *0009*🌿🌿
————————
*By Haruna I Muh'd*
*08069582878*
*hdindima.blogspot.com*
———————
*FALALAR AZUMI*
———(F)———
16. *al-Qur'an da Azumi zasu ceci masu yinsu ranar al-Qiyamah kamar yadda manzon Allah ya fada:*
*_"الصيام والقرآن يشفعان للعبد يوم القيامة، يقول الصيام: أي يا رب منعته الطعام والشهوات بالنهار، فشفعني فيه، ويقول القرءان: منعته النوم بالليل، فشفعني فيه"_*
*_"Azumi da al-Qur'an za su ceci bawa ranar al-Qiyamah, Azumi zai ce: Ai ya Ubangiji na hanashi cin abinci da wasu Sha'awarsa da rana, Allah ka bani cetonsa, Sallah ma zai ce: Ya Ubangiji na hanashi barci cikin dare (yana Sallah): Allah ka bani cetonsa"_*
17. *Azumi na gusar da Kullace-kullacen wani ko wasiwasi ko yawan fushi. Manxon Allah (swa) ya ce*
*_" صوم شهر الصبر، وثلاثة أيام من كل شهر: يذهبن وحر الصدر"_*
*_"Azumi na wata guda sai da hakuri, da kuma azumin da ake yi Uku a ko wani wata, suna gusar da kyashi(kofe ko takaicin) a cikin zuciya"_*
18. *Azumi kofa ce daga kofofin al-khairi, kamar yadda manzon Allah (saw) ya ce:*
*_"الصوم جنة، والصدقة تطفئ الخطيئة كما تطفئ الماء النار، وصلاة الرجل من جوف الليل....."_*
*_"Azumi garkuwa ce, Sadaqa kuma tana kankare kura-kurai kamar yadda ruwa ke kashe wuta haka ma sallar mutum a cikin tsakiyar dare*_*
*Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*
——N.B.——
*U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH*
——————
Via
*hdindima.blogspot.com*
No comments:
Post a Comment