*MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN*
🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 *0011*🌿🌿
————————
*By Haruna I Muh'd*
*08069582878*
*hdindima.blogspot.com*
*———————*
*_ABUN DA MAI AZUMI AKE SO YAYI KENAN NA SUNNONIN MANZON ALLAH (SAW)_*
*———(A)———*
*Assalamu Alaikum*
*Yan'uwana musulmai a cikin azumi akwai sunnonin manzon Allah da dama da ake son ko wani mai azumi ya dinga yinsu, ga kadan daga ciki kamar haka:*
*1* *Gaggauta shan ruwa da zarar an tabbatar rana ta fadi*
*Manzon Allah (saw) ya ce:*
*_"لا يزال الناس بخير ما أجلوا الفطر"_*
*_"Mutane ba zasu gushe ba suna tare da al-khairi, matukar suna gaggauta shan ruwa"_*
*2* *Fara bude-baki da danyen kayan itatuwa ko dabino ko ruwa*
*_"Sahabin manzon Allah Anas (ra) ya ce manzon Allah ya kasance yana bude-baki da danyen abu, in babu ko da dabino ko da ruwa"_*
*3* *Yin addu'a lokacin bude baki*
*Sahabin manzon Allah, Abdul-Lahi ibn Umar ya ce manzon Allah in yazo bude-baki yakan karanta wan nan addu'a kamar haka:*
*ADDU'AR BUDE-BAKI(SHAN RUWA)*
*_"ذهب الظمأ وابتلت العروق وثبت الأجر إن شاء الله"_*
*_"Zhabaz-Zhama'u, Wabtallatil-Uruqu, Wathabatal-Ajru insha Allah"_*
*Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*
——N.B.——
*U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH*
——————
Via
*hdindima.blogspot.com*
No comments:
Post a Comment