*MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN*
🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 *0010*🌿🌿
————————
*By Haruna I Muh'd*
*08069582878*
*hdindima.blogspot.com*
———————
*FALALAR AZUMI*
———(G)———
19. *Duk wan da ya mutu yana Azumi zai shiga Al-Jannah, inji manzon Allah (saw):*
*_"من قال لا إله إلا الله ابتغاء وجه الله، ختم له بها دخل الجنة، ومن صام يوما ابتغاء وجه الله ختم له بها، ومن تصدق بصدقة ابتغاء وجه الله ختم له بها دخل الجنة"_*
*_"Duk wanda ya ce La Ilaha Illal-Lah don neman yardar Allah, kuma ya mutu da ita zai shiga Al-Jannah, haka duk wanda yayi azumin don nemar yardar Allah, kuma ya mutu dashi zai shiga Al-Jannah, da kuma duk wanda yayi sadaka don neman yardar Allah zai shiga Al-Jannah"_*
20. *_"Allah ya tanadi kololuwar Al-Jannah ga masu Azumi yadda Shari'ah ta tanadar, da kuma masu Ciyarwa, da masu magana mai Taushi ma yan'uwansu, da masu yada sallama tsakanin jama'ah, da masu sallah lokacin da mutane ke barci*
*Duk wadan nan sun zo a Hadith na manzon Allah kamar haka:*
*_"إن في الجنة غرفا، يرى ظاهرها من باطنها، و باطنها من ظاهر، أعدها الله تعالى لمن أطعم الطعام، وألان الكلام، و تابع الصيام، وأفشى السلام، وصل بالليل والناس نيام"_*
*_"Lallai cikin Al-Jannah akwai manyan Gini na dakuna, daga ciki kana ganin waje, daga waje kana ganin ciki, Allah ya tanadesu ne ga masu ciyar wa, da masu iya magana mai taushi, da masu Azumi da masu Yada sallama(ga wanda suka sani ko wanda basu sani ba) da masu Sallah cikin dare mutane na barci"_*
21. *Allah na karban addu'ar mai Azumi har lokacin da zai sha ruwa, ba a mayar da addu'arsa baya. Hakan ya fito ne daga baki fiyeyyen Halitta manzon Allah (saw) yadda ya ce:*
*_"ثلاثة لا ترد دعوتهم: الإمام العادل، الصائم حتى يفطر، ودعوة المظلوم يرفعها الله فوق الغمام يفتح لها أبواب السماء، ويقول الرب: بعزتي لأنصرنك ولو بعد حين"_*
*_" (mutane nau'uka) uku ba'a mayar da addu'arsu: Shugaba mai adalci, mai Azumi har yasa ruwa, da addu'ar wanda aka zalunta, Allah zai daga ta har zuwa Girgije san nan a bude mata kofofin Sama, Ubangiji sai ya ce : Na rantse da buwayata sai na taimakeka ko da bayan shekara ne"_*
*Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*
——N.B.——
*U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH*
——————
Via
*hdindima.blogspot.com*
No comments:
Post a Comment