Wednesday, 7 June 2017

RAMADAN MUBARAK (13)

*MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN*

🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 *0013*🌿🌿
————————
*By Haruna I Muh'd*
*08069582878*
*hdindima.blogspot.com*

*———————*
*_ABUN DA MAI AZUMI AKE SO YAYI KENAN NA SUNNONIN MANZON ALLAH (SAW)_*
*———(C)———*

*Assalamu Alaikum*

   *Yan'uwana musulmai a cikin azumi akwai sunnonin manzon Allah da dama da ake son ko wani mai azumi ya dinga yinsu, ga kadan daga ciki kamar haka:*

*7* *Yawan yin sadaka a cikin Ramadana da wajen Ramadan*
        *Ya zo a Hadith Manzon Allah (Saw) ya kan zama mafi yawan ba da kyauta da sadaka a Ramadan, musamman lokacin da Mala'ika Jibril ya zo ya masa bitan al-Qur'an, yakan ninka kyautan da yake yi (saw)*

*8* *Yawan karanta al-Qur'an, wato ba lallai sai mahaddata ba, ko sura daya ka iya kayi ta mai-maitata Allah zai ninka maka lada akan hakan, dan Allah ya ce mana a wannan wata ta Ramadan Allah ya saukar da al-Qur'an wa Manzon Allah (saw)*
       *Allah ya ce:*

Surah Al-Baqara, Verse 185:

*_"شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدًى لِّلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِّنَ الْهُدَىٰ وَالْفُرْقَانِ فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ"_*

*_"The month of Ramazan is that in which the Quran was revealed, a guidance to men and clear proofs of the guidance and the distinction; therefore whoever of you is present in the month, he shall fast therein, and whoever is sick or upon a journey, then (he shall fast) a (like) number of other days; Allah desires ease for you, and He does not desire for you difficulty, and (He desires) that you should complete the number and that you should exalt the greatness of Allah for His having guided you and that you may give thanks."_*

*9* *Kiyamul Lail (Sallar Asham, ko Tahajjud ko sauran Nafiloli)*
       *A kan wan nan manzon Allah yana jan hankalinmu da mu dage da sallar Dare a ramadana da bayanta in da hali. Manzon Allah ya ce:*

*_"من قام رمضان  إيمانا واحتسابا، غفر له ما تقدم من ذنبه"_*

*_"Duk wanda yayi sallah (Asham ko Tahajjud ko Nafiloli na daban) a Ramadan, yana mai Imani da kuma tsammanin Samun lada (da sakamako mai kyau) a wajen Allah, za'a gafarta masa Zunubansa kaf da yayi a baya"_*

   *Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*

——N.B.——
*U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH*

*_"Kuyi gaggawa zuwa ga samun rahamar Ubangijinku, da kuma neman Al-Jannah, wacce fadin cikinta kamar fadin sama da kasa, an tanadeta ne kawai ga masu tsoron Allah"_*
——————

Via
*hdindima.blogspot.com*

No comments:

Post a Comment