Wednesday, 7 June 2017

RAMADAN MUBARAK (12)

*MARABA DA BABBAN BAKO RAMADAN*

🌿🌿🌿🌿🌿🌿
🌿🌿 *0012*🌿🌿
————————
*By Haruna I Muh'd*
*08069582878*
*hdindima.blogspot.com*

*———————*
*_ABUN DA MAI AZUMI AKE SO YAYI KENAN NA SUNNONIN MANZON ALLAH (SAW)_*
*———(B)———*

*4.* *Jinkirta yin sahur*
     *lallai ya tabbata daga Manzon Allah (saw) ya ce:*

*_"تسحروا فإن في السحور بركة"_*

*_"Ku yi sahur sabo da cikinsa akwai albarka "_*

*5.* *Kame Baki da duk kan gabbai akan abubuwan da Allah ya haramta*
     *Manzon Allah (saw) ya ce:*

*_" من لم يدع قول الزور والعمل به والجهل، فليس لله حاجة في أن يدع طعامه وشرابه"_*

*_"Duk wanda bai bar shaidar Zur ba( shaidar karya), ko amfani da ita, ko aikin jahilci (a Azumi) ba ruwan Allah ko ya bar cin abu ko shan abu, (ko yayi azubi ko kar yayi ba ruwan Allah)"_*

*6* *Ciyar da mai Azumi a watan Ramadan*
      *Manzon Allah (saw) ya ce :*
       *_"من فطر صائما فله مثل أجره، غير أنه لا ينقص من أجر الصائم شيء"_*

*_"Duk wanda ya ciyar da mai azumi (da abun bude-baki), yana da irin ladan mai azumin, ba tare da an rage na mai azumin komai ba"_*

   *Allah yasa da wan nan yar nasiha ta zamu amfana baki daya, Allah ya kara bamu ladansa Ameeeeeeeeeeeen*

——N.B.——
*U CAN SHARE THIS FISABILIL-LAH*
——————

Via
*hdindima.blogspot.com*

No comments:

Post a Comment