*🧕AL-MAR'A ASSALIHA(ZAUREN MACE TA GARI)*
*HADITH CLASS (6)*
*✔️BABIN JININ AL'ADA DA NA HAIHUWA*
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
Hadith No 2
*An karbo Hadith daga Abdullahi bn Saeed ya ce: na tambayi Manzon Allah (saw) akan cin abinci da mai Al'ada, sai ya ce *"Ka ci da ita"*
(Ahmad)
*عن عبد الله بن سعيد قال، سألت النبي صلى الله عليه وسلم عن مؤاكلت الحائض، قال واكلها*
Hadith 3
*An karbo Hadith daga Anas Bin Malik , ya ce : Lallai Yahudawa sun kasance idan mace tayi al'ada a cikinsu, sai su fitar da ita daga gida, ba zasu ci abu da ita ba, kuma ba zasu sha wani abu da ita ba, ba za suyi wani mu'amala da ita ba a cikin gidan, sai aka tambayi Manzon Allah (saw) akan hakan, sai Allah ya saukar da aya akan maganar, ya ce : Suna Tambayarka akan masu Al'ada, ka ce masu shi (al'ada din) kazanta ne, ku nisanci mata a lokacin al'ada (nisantar Saduwa) har karshen Ayar. Sai Manzon Allah (saw) ya ce : kuyi mu'amala dasu a cikin gida, kuma kuyi komai dasu, amma banda Saduwa ta (aure)"*
Abu Dawud
عن أنس بن هالك قال إن اليهود كانت إذا حاضت منهم المرأة ، أخرجوها من اليت ولم يؤاكلوها ولم يشاربوها ولم يجامعوها في البيت، فسئل رسول الله صلى الله عليه وسلم عن ذلك ، فأنزل الله تعالى ذكره
*وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ*
*فقال رسول الله صلى عليه وسلم جامعوهن في البيوت، واصنعوا كل شيء غير النكاح"*
NB
Wan nan na Gwada hukunci ya halarta ayi dukkan muaamala ta yau da kullun da mata, sai dai kawai banda Saduwa ta aure a lokacin da suke Al'ada.
Allah yasa mu dace.
No comments:
Post a Comment