Friday, 6 May 2022

FALALAR SURATU KAHFI

*AL-MAR'A ASSALIHA (DAGA ZAUREN MACE TA GARI)*

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com

*⬜ احاديـث نبويـة فـي فضـل سـورة الكهـف ⬜*

✔️ An karbo Hadith daga Abud Darda'a (RA), lallai Manzon Allah (saw) ya ce :
*"Duk wanda ya haddace ayoyi goman farko na suratu Kahfi, za'a kareshi daga Dujal"*
 Muslim (809)

▪️عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ : *(( مَنْ حَفِظَ عَشْرَ آيَاتٍ مِنْ أَوَّلِ سُورَةِ الْكَهْفِ عُصِمَ مِنَ الدَّجَّالِ ))*
📜صحيح مسلم (809)

✔️ An karbo Hadith daga Abu Saeed al-khudry (RA) , daga Manzon Allah ( saw) ya ce :
*" Duk wanda ya karanta Suratu Kahfi, zata kasance masa haske a ranar al-Qiyama tun daga yadda yake har tazarar zuwa Makkah, haka duk wanda ya karanta ayoyi goman farkonta, lokacin da Dujal zai bayya ba zai cutar dashi ba.........."*
Albani (225)

▪️عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ : *(( مَن قرأَ سورةَ الكَهْفِ كانت لهُ نورًا يومَ القيامةِ مِن مقامِه إلى مكَّةَ ، ومَن قرأ عشرَ آياتٍ مِن آخرِها ثمَّ خرجَ الدَّجالُ لَم يضرَّهُ ،،،، ))*
📜صححه الألباني في صحيح الترغيب (225)

✔️ An karbo Hadith daga Abu Saeed al-khudry har yanzu (RA) , Manzon Allah (saw) ya ce:
*" Duk wanda ya karata Suratu Kahfi a daren Juma'ah, Allah zai haskaka tsakaninsa har tazarar zuwa Dakin nan yantacce(Kaabah)"*
Albani (736) 

▪️وعَنْهُ قَالَ : قَالَ :  رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : *(( من قرأ سورةَ الكهفِ ليلةَ الجمعةِ ، أضاء له من النورِ ما بينه وبين البيتِ العتيقِ ))*
📜صححه الألباني في صحيح الترغيب (736)

✔️ Manzon Allah (saw) ya sake cewa :
*" Duk wanda ya karanta Suratu Kahfi a ranar Juma'ah, Allah zai haskaka masa har tazarar Juma'ah guda biyu (wato sati biyu yana cikin Hasken Allah)"*
Albani (736)

▪️أيضاً قَالَ : *(( من قرأ سورةَ الكهفِ في يومِ الجمعةِ أضاء له من النورِ ما بين الجمُعَتَين ))*
📜صححه الألباني في صحيح الترغيب (736)

*🖇️↓ ‏لقراءة سورة الكهف ↓*
Ga mai son karanta Suratu Kahfi kai tsaye, ka latsa kasan nan
👇👇👇👇👇
‏ ⁦ http://quranapp.com/18

⁩In kana son Sauraron karatun Surar kai tsaye, Latsa nan dake kasa
👇👇👇👇👇👇
*🖇️↓ لسماع سورة الكهف ‏للشيخ القارئ محمد أيوب رحمه الله ↓*
https://download.tvquran.com/download/TvQuran.com__Ayyub/018.mp3

Tayamu yada Alkhairi, don shi Alkhairi Danko ne🤳🤳🤳🤳🤳🤳

No comments:

Post a Comment