*💧ZAUREN AL-MAR'ATUS-SALIHA💧*
*TA YAYA ZAMU MAGANCE YIN TAZARA DAGA DA'A MA ALLAH BAYAN RAMADAN?*
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*⬜ كيف نعالج فتور النفس عن الطاعة بعد رمضان ؟⬜*
Abun da ya kamata mu fara sani shi ne dole mu dage mu Toshe tazara, kuma hakan wajibi ne, *Ko wani Aiki fa ana iya samun Sharri, shi kuma sharri yana samuwa in aka bar tazara*
💡لِنعلمْ أولا أن تخلُّلَ الفَترات للسَّالكين أمرٌ لا بد منه؛ فإن *"لكل عملٍ شِرَّة، ولكل شرَّة فترةٌ".*
Don mu magance wan nan tazara, zamu lura da wadan nan al'amura kamar haka:
*⭕ ومن ثم فمعالجة الفتور عن الطاعة تقتضي أمورًا :*
▪️Daya: Neman taimako daga Allah.
(Ko wani aiki ana son ka nemi taimakon Allah dan samun dacewa, kana yawan fadan "Iyyaka Na'abudu wa iyyaka Nasta'eeen" kaji hakan har cikin ranka da kuma yi a aikace) da kuma yawan fadin "Allahumma A'innah alaa Zikrika wa shukrika wa husni ibadatuka"
*أوَّلا :* الاستعانة بالله عز وجل؛ فإنه لا يدرك خير إلا بعونه.. مستحضرين مقام *﴿ إياك نعبد وإياك نستعين ﴾* مرددين بلسان المقال مع صدق الحال: *"اللهم أعنا على ذكرك وشكرك وحسن عبادتك".*
▪️Na biyu = Dawwama akan Kokari da Tarbiya mai kyau, yin abu don Allah da kuma nema tukuru, kana kuma ji ma ranka in har kayi kokari zaka samu sakamako mai kyau a wajen Allah.
(Allah ya ce : "wadan da suke kokari a cikin addininmu , zamu shiryar dasu hanyarmu mai kyau")
*ثانيًا :* دوام المجاهدة والدأب ؛ وصدق الإلحاح والطلب؛ مستحضرين حلو عاقبة: *﴿ والذين جاهدوا فينا لنهدينهم سبلنا ﴾.*
▪️ Na uku= Tausasa rai da kuma saka mata abu mai saukin da zata iya, da kuma iya tafiyar da ita yadda ya kamata, da kuma mata jagoranci a hankali wajen aikin Alkhairi.
( Hakan yana daidai da fadin Manzon Allah (saw) :" kuna daura ma kanku daidai abun da zaku iya yi, na rantse da Allah, shi Allah baya kosawa har sai kun kosa" " abu kadan kadan cikin manufa sai a cimma abun da ake so" "ku kara dagewa da kokari")
*ثالثًا :* الرفق بالنفس، وأخذها باليسر، وحسن سياستها، وقيادها إلى الخير ؛ متأملين حكمته صلى الله عليه وسلم في قوله: *"اكلفوا من الأعمال ما تطيقون؛ فوالله لا يمل الله حتى تملوا".* وقوله: *"القصد القصد تبلغوا"* و *"سددوا وقاربوا".*
▪️ Na hudu: Rainon rai wajen yin abu da za'a jima ana yi koda kadan ne, don yafi Alkhairi akan aiki mai yawan da ba za'a dauwama akai ba.
(Manzon Allah (saw) ya kasance " ayyukansa ko yaushe yana dawwama ne akai" kuma yace mafi " aikin da Allah yafi so, shi ne wanda mai yi ya dawwama akai komai kashinsa")
*رابعًا :* تعويدُ النفس على القليل الدائم الذي هو خير من الكثير المنقطع؛ ملتفتين إلى أنه : *"كان عمله صلى الله عليه وسلم دِيمةً"* *"وَأنّ أَحَبَّ الْأَعْمَالِ إِلَى الله مَا دَامَ عليه صاحبه وَإِنْ قَلَّ".*
▪️Na biyar: Canza ayyukan Alkhairi, ya zama kana yinsu nau'i-nau'i da canza da'a ma Allah kala-kala , hakan yana sa rai tana jin annashuwa da marmarin aiki, dan zai sama ta kosa da wani aiki sai ka kara kaita wani daban, sai ya kara mata annashuwa.
*خامسًا :* تنويع العمل الصالح وتجديد الطاعة بعد الطاعة وعدم قصر النفس على لون واحد من التعبد؛ ففي ذلك إجمام للنفس وتطرية لها.. فإذا سئمت النفس من عمل ، انتقلت إلى آخر؛ حتى تكون هي التي تشتاق إلى ذلك العمل؛ فتجد له خفة ونشاطا ولذة وحلاوة..
🤲 Muna rokon Allah ya azurtamu da jin dandanon ganawa dashi da kuma zakin yi masa biyayya, don shi ne mafi cancantar da a rokeshi.
*والله المسؤول أن يذيقنا حلاوة مناجاته، ولذة طاعته؛ إنه أكرم مسؤول .*
*✒️د. زياد خياط*
٣ شوال ١٤٤١
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
No comments:
Post a Comment