*AL-MAR'A ASSALIHA ( ZAUREN MACE TA GARI)*
*HADITH CLASS (7)*
*____________________*
*BABIN AL'ADA DA JININ HAIHUWA*
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
*🕹️Hadith {4}*
*«عن أنس قال :كان صلى الله عليه وسلم وقت للنفساء أربعين يوما، إلا أن ترى الطهر قبل ذلك»*
رواه ابن ماجه
🦋 *An karbo Hadith daga Anas (RA) ya ce: Manzon Allah (saw) ya sanya wa mata masu jinin haihuwa (tsawon zaman da za suyi ba su ibada) Kwana arba'in, sai dai in (mace) ta ga tsarki kafin nan ( in har taga tsarki ko da a ranar haihuwa ne ta samu tsarki, ba sai ta kai arba'in ba, komai na Ibada ya dawo kanta)*
🕹️ *Hadith (5)*
*«قالت أم سلمة كانت المرأة من نساء النبي صلى عليه وسلم تقعد في النفاس أربعين ليلة، لا يأمرها النبي صلى عليه وسلم لقضاء صلاة النفاس»*
رواه أبو داود
*🦋Ummu Salma (RA) ta ce,: Daya daga cikin matan Manzon Allah (saw) takan zauna a cikin jinin haihuwa har na tsawon kwanaki Arba'in, amma Manzon Allah (saw) bai taba umartanta da ta biya sallah ba, dan jinin haihuwa"*
Wan nan shi ne hukuncin da Manzon Allah (saw) ya sanya wa mace mai jinin haihuwa, akan mafi tsayinsa, in tana cikin jinin haihuwa zata bar Sallah da Azumi , in har ya tsaya sai ta biya Azumi amma banda Sallah.
Kuma mafi yawan malamai sun ce, mafi tsayin jinin haihuwa baya wuce kwanaki Arba'in, in kuma ya wuce sai ta ci gaba da sallah da Azumi , sai ta nemi maganin jinin , don ya zama na cuta.
Allah ya karba mana kyawawan Ibadunmu baki daya. Ameeeeen.
*_________________________*
No comments:
Post a Comment