Saturday, 4 June 2022

SAKAQA DA ABINCIN MIJI

*AL-MAR'A ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)*

*⭕Yin Sadaqa da abincin miji*

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com

Assalamu Alaikum yan'uwana musulmai na wan nan Zaure mai tarin albarka, lallai tambayoyi na yawaita akan 

_«shin zan iya yin Sadaka da kayan abinci ko abincin mijina ba tare da izininsa ba?»_

*Amsa:*

Lallai ba za kiyi sadaka da kayan abincin mijinki ba tare da izininsa ba, wato muddin in ya hana bai halatta kiyi sadaqa dashi ba. Amma za ki iya yu in ya amince, kuma amincewa kala biyu ne, 

▪️1. Amincewa na Zahiri da lafazi( kamar ya ce ba komai duk wanda kika ga yana da bukatar a taimaka masa zaki iyayi) wan ba laifi ba ne.

▪️2. Ko ya amince a dabi'ance, (misali bai ce maki kiyi sadaqa ba, amma ya aminta dake ya sake maki komai, kuma in da za kiyi ba zai taba damuwa ba,) to a irin wan nan duk kuna da tarayya a cikin ladan baki dayanku, muddin baki barnata abun ba.

Ga Hadith na Manzon Allah (saw) akan hakan:

*وعن عائشة رضي الله عنها قالت: قال النبيُّ ﷺ: «إذا أنفقت المرأةُ من طعام بيتِها غير مفسدةٍ كان لها أجرُها بما أنفقت، ولزوجها أجره بما اكتسب، وللخازن مثل ذلك, لا ينقص بعضُهم من أجر بعضٍ شيئًا».* متفقٌ عليه.

🌲Hadith daga daga Nana Aishatu (RA) ta ce, Manzon Allah (saw) ya ce: 

*«Idan mace ta ciyar da abincin gidan mijinta, ba tare da tayi barnansa ba, tana da ladanta sabo da ciyarwan , mijinta ma yana da ladansa saboda nemowan da yayi, mai lura da abincin (Store Keeper) shima da ladansa, ba tare da an rage ma kowa nashi ladan ba»*

Bukhari da Muslim

Allah ya taimakemu baki daya, yan'uwa.
*___________________________*

No comments:

Post a Comment