*🦋 AL-MAR'ATUS SALIHAH🧕*
*🪴HADITH CLASS (8)*
*🤱(BABIN YADDA AKE WANKAN AL'ADA DA KUMA NA HAIHUWA)*
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
Hadith 1
*▪️"عن عائشة ، أن أسماء سألت النبي صلى الله عليه وسلم عن غسل المحيض، فقال تأخذ إحداكن ماءها وسدرتها فتطهر فتحسن الطهور، ثم تصب على رأسها فتدلكه دلكا شديدا، حتى تبلغ شئون رأسها، ثم تصب عليها الماء، ثم تأخذ فرصة ممسكة فتطهر بها، فقالت أسماء وكيف تطهر بها فقال سبحان الله تطهرين بها، فقالت عائشة كأنها تخفي ذلك، تتبعين أثر الدم"*
*▪️An karbo Hadith daga Nana Aishatu (RA) lallai Asma'u ta tambayi Manzon Allah (saw) game da wankan mai al'adah, sai ya ce mata, dayanku ta nemi ruwanta da kuma magarya, sai ta tsarkaka ta kuma kyautata tsarkin, sannan ta zuba ruwa a kanta, ta cuccuda sosai, har sai ruwa ya taba har kasan gashinta, sannan sai ta zuba ruwa a dukkan kayin, san nan ta nemi auduganta (ko wani abu mai laushi) ta sanya masa turare (ko abun kamshi) sai ta tsarkaka dashi, sai Asma'u ta ce, ta yaya za tayi tsarki dasu din? Sai (Manzon Allah) ya ce, Subhanallah, ta yi tsarki mana dasu, sai Aishatu (RA) ta ce amma tana sakaye maganar (kamar dan kar kowa a wajen yaji) (ta ce) ta bibiyi duk gurbin jinin mana"*
*💯KARIN BAYANI*
Yan'uwa na wan nan Hadith yana gwada mana wankan Janaba da na Al'ada da na Haihuwa duk iri daya ne, banbancin su shi ne,
➖ Ko wanne akan son a masa niyyarsa.
➖ Shi kuma na Al'ada da na Haihuwa, akwai Abubuwan da ake son lokacin wankan ayi amfani dasu don a kawai da duk wani jini, kamar magaryar a zamanin baya, ko sabulu mai kamshi ko wani mai mai kamshi, sai kuma amfani da auduga ko wani abun share duk wani jinin jiki.
San nan kuma yana da kyau duk mai wa'azi yana amfani da kalmomi na kunya, in har za'a gane ba komai ne za'a dinga zarewa balobalo ba. Ya zama akwai kunya a lamarin.
Allah ya sa mu dace ya kuma karba mana dukkan Ayyukanmu na Alkhairi baki daya. Ameeeeen
➖➖➖➖➖➖➖➖➖➖
No comments:
Post a Comment