*🦋AL-MAR'A ASSALIHA (ZAUREN MACE TA GARI)🧕*
*★Nasiha an Mai Fuska biyu★*
✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com
Assalamu Alaikum yan'uwana musulmai tabbas akwai nau'in mutane wanda ba wanda ya kaisu sharri a Duniya. Kuma irin wan nan shi ne MUNAFIKI (Magulmaci).
_An karbo Hadith daga Abu Huraira (RA) ya ce : Manzon Allah ﷺ ya ce:_
_*« Mafi Sharri a cikin Mutane shi ne mai Fuska biyu (Munafiki, Magulmaci) , wanda yake zuwa wajen wadan nan da wata fuska daban, ya kuma je wajen wadan can da fuska daban.»*_
(Bukhari)
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ﷺ : *"إِنّ شَرَّ النَّاسِ ذُو الْوَجْهَيْنِ، الَّذِي يَأْتِي هَؤُلاَءِ بِوَجْهٍ وَهَؤُلاَءِ بِوَجْهٍ"،* رواه البخاري
Allah ya karemu da Annamimanci da kuma Gulma. Ameeeeen
*__________________*
No comments:
Post a Comment