Saturday, 12 March 2022

DAGA CIKIN DALILAN SAMUN ALBARKA

*AL-MAR'A ASWALIHA (DAGA ZAUREN MACE TA GARI)*

✍️ Haruna Isah Muh'd
hdindima@gmail.com

*DAGA CIKIN DALILAN SAMUN ALBARKA*
*⬛ من أسباب البركة ⬛

Hadiths ya zo a cikin Sahihu Muslim, Manzon Allah (saw) ya ce:
*"Idan daya daga cikinku, ya ci abinci, to kar ya wanke hanun har sai ya tsotse su"*

▫️في صحيح مسلم: *(إِذَا أَكَلَ أَحَدُكُمْ طَعَامًا فَلَا يَمْسَحْ يَدَهُ حَتَّى يَلْعَقَهَا أَوْ يُلْعِقَهَا)*

*"Manzon Allah (saw) ya kasance yana cin abinci da yatsu uku, kuma yana tsotse yatsunsa"*

• *(كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَأْكُلُ بِثَلَاثِ أَصَابِعٍ وَيَلْعَقُ يَدَهُ قَبْلَ أَنْ يَمْسَحَهَا)*

*"(Manzon Allah) ya yi umurni da ana tsotse yatsu da kuma tande kwanon abinci , har yake cewa baku sani ba! Shin a ina albarkan yake ba"*

• *(أَمَرَ بِلَعْقِ الْأَصَابِعِ والصحفة وقال: إنكم لا تدرون فِي أَيِّهِ الْبَرَكَةُ)*

*"Idan dayanku lomarsa ta fadi a kasa, (in wajen da dan tsafta) to ya dauki kayansa, sai kuma ya share abun da ya mannu da lomar , ya c kayansa kar ya bar wa Shaitan"*

• *(إِذَا وَقَعَتْ لُقْمَةُ أَحَدِكُمْ فَلِيَأْخُذْهَا فَلْيُمِطْ مَا كَانَ بِهَا من أذى وليأكلها ولايدعها للشيطان)*

Imam Nawawi ya ce:
cikin abinci akwai albarka,
Ba wanda ya sani kan cewa, albarkan tana karkashin yatsunsa ne ko a jikin Kwanon ko kuma a jikin loman da ta fadi a kasa?!

*▪️قال النووي:* الطعام فيه بركة، ولايدرى أن تلك البركة فيما أكله أو فيما بقي على أصابعه أو في ما بقي في أسفل القصعة، أو في اللقمة الساقطة،
Lallai yana da kyau da muna kwatanta Sunnah ta Manzon Allah (saw), kar muna daukansa a matsayin kauyanci. Sai dai in abincin da ya fadin datti ya masa yawan da ba za mu iya gyara kayanmu ba. Allah yasa mu dace, Ameeeeen.

• فينبغي أن يحافظ على هذا كله لتحصل البركة، وأصل البركة: الزيادة وثبوت الخير والإمتاع به، والمراد هنا والله أعلم: ما يحصل به التغذية، وتسلم عاقبته من أذى، ويقوي على طاعة الله تعالى وغير ذلك. 📜(شرح مسلم 13/206)
*___________________________________*

No comments:

Post a Comment